< Matthew 22 >
1 Jesus continuing to discourse to them in parables, said,
Yesu ya sake yi masu magana da misalai, yace,
2 The Administration of Heaven resembles the conduct of a king, who having made a marriage feast for his son,
“Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya wa dansa liyafar aure.
3 sent his servants to call them, who had been invited; but they would not come.
Ya aiki bayinsa su kira wadanda aka gayyata su zo liyafar auren, amma suka ki zuwa.
4 Then he sent other servants, saying, Tell those who are invited I have prepared my feast; my bullocks and fatlings are slain, and all is ready; come to the marriage.
Sai sarkin ya sake aiken wasu bayin, yace, “Ku gaya wa wadanda aka gayyata, “Duba, na shirya liyafata. An yanka bajimaina da kosassun 'yanmarukana, an gama shirya komai. Ku zo wurin bikin auren.”
5 But they turned away with indifference, one to his farm, another to his merchandize.
Amma mutanen ba su dauki sakon da mahimmanci ba kuma suka yi tafiyarsu. Wani ga gonarsa, wani ga kasuwancinsa.
6 And the rest seizing his servants, abused and killed them.
Sauran kuma suka kama bayin sarkin, suka wulakanta su, suka kuma kashe su.
7 When the king heard this, being enraged, he sent his soldiers, destroyed those murderers, and burnt their city.
Amma sarkin ya ji haushi. Ya aika sojojinsa, ku kashe masu kisan kan nan, ku kuma kone birnin su.
8 Then he said to his servants, The entertainment is ready; but they who were invited were not worthy:
Sai ya ce wa bayinsa, 'An gama shirya bikin, amma wadanda aka gayyata ba su cancanta ba.
9 go therefore, into the public roads, and all that you can find, invited to the marriage.
Saboda haka ku je bakin hanya ku gayyaci iyakar yawan mutanen da za ku samu zuwa bukin auren.'
10 Accordingly they went into the highways, and assembled all that they found, good and bad, so that the hall was furnished with guests.
Bayin suka tafi hanya suka tattaro dukan mutanen da suka samu, da masu kyau da marassa kyau. Zauren auren kuwa ya cika makil da baki.
11 When the king came in to see the guests, observing one who had not on a wedding garment,
Amma da sarkin ya zo don ya ga bakin, sai ya ga wani wanda bai sa kayan aure ba.
12 he said to him, Friend, how came you here without a wedding garment? And he was speechless.
Sai sarkin ya ce masa, 'Aboki, ta yaya ka shigo nan ba tare da kayan aure ba?' Mutumin kuwa ya rasa ta cewa.
13 Then the king said to the attendants, Bind him hand and foot, and thrust him out into darkness, where will be weeping and gnashing of teeth;
Sai sarkin ya ce wa bayinsa, 'Ku daure mutumin nan hannu da kafa, ku jefa shi cikin duhun, inda za ayi kuka da cizon hakora.'
14 for there are many called, but few chosen.
Gama mutane dayawa aka kira, amma kadan aka zaba.”'
15 Then the Pharisees retired, and having consulted how they might entrap him in his words,
Sai Farisawan suka tafi suka shirya makirci akan yadda zasu kama shi ta maganarsa.
16 sent to him some of their disciples, and some Herodians, who being instructed by them, said, Rabbi, we know that you are sincere, and faithfully teach the way of God, without partiality, for you respect not the person of men.
Suka tura masa almajiransu, da Hirudiyawa. Suka ce ma Yesu, “Mallam, mun san kai mai gaskiya ne, kuma kana koyar da hanyar Ubangiji da gaskiya. Ba ka damu da ra'ayin kowa ba, kuma ba ka nuna bambanci a tsakanin mutane.
17 Tell us, therefore, your opinion: Is it lawful to give tribute to Cesar, or not?
To gaya mana, menene tunaninka? Ya halarta a biya haraji ga Kaisar ko a'a?”
18 Jesus, perceiving their malice, said, Dissemblers, why would you entangle me?
Amma Yesu ya gane muguntarsu yace, “Don me kuke gwada ni, ku munafukai?
19 Show me the tribute money. And they reached him a denarius.
Ku nuna mani sulen harajin.” Sai suka kawo masa sulen.
20 He asked them, Whose image and inscription is this?
Yesu yace masu, “Hoto da sunan wanene wadannan?”
21 They answered, Cesar's. He replied, Render, then, to Cesar that which is Cesar's, and to God that which is God's.
Suka ce masa, “Na Kaisar.” Sai Yesu ya ce masu, “To ku ba Kaisar abubuwan dake na Kaisar, Allah kuma abubuwan dake na Allah.”
22 And admiring his answer, they left him, and went away.
Da suka ji haka, suka yi mamaki. Sai suka bar shi suka tafi.
23 The same day Sadducees, who say that there is no future life, came to him and addressed him:
A ran nan sai wadansu Sadukiyawa, wadanda suka ce ba tashin matattu, suka zo wurinsa. Suka tambaye shi,
24 Rabbi, Moses has said, if one die, and have no children, his brother shall marry his widow, and raise issue to the deceased.
cewa, “Mallam, Musa yace, 'Idan mutum ya mutu, bashi da 'ya'ya, dole dan'uwansa ya auri matarsa ya kuwa haifawa dan'uwansa 'ya'ya.
25 Now there lived among us seven brothers; the eldest married and died without issue, leaving his wife to his brother.
Akwai wasu 'yan'uwa bakwai. Na farkon yayi aure sai ya mutu. Da shike bai bar 'ya'ya ba. Ya bar wa dan'uwansa matarsa.
26 Thus also the second, and the third, and so to the seventh.
Sai dan'uwansa na biyu shi ma yayi haka, haka kuma na ukun, har zuwa dan'uwan na bakwai.
27 Last of all the woman died also.
Bayan dukansu, sai matar ta mutu.
28 Now, at the resurrection, whose wife shall she be of the seven; for they all married her?
To a tashin matattu, matar wa zata zama a cikin su bakwai din? Don duk sun aure ta.”
29 Jesus answering, said to them, You err, not knowing the scriptures, nor the power of God;
Amma Yesu ya amsa yace masu, “Kun bata, domin ba ku san litattafai ko ikon Allah ba.
30 for in that state, they neither marry, nor give in marriage: they resemble the angels of God.
Domin a tashin matattu basu aure, ba kuma a bada su aure. Maimaikon haka, suna kama da mala'ikun sama.
31 But as to the revival of the dead, have you not read what God declared to you, saying,
Amma game da tashin matattu, ba ku karanta abinda Allah ya fada maku ba, cewa,
32 "I am the God of Abraham, and the God of Isaac, and the God of Jacob?" God is not a God of the dead, but of the living.
'Nine Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku, da Allah na Yakubu'? Allah ba Allah na matattu bane, amma na rayayyu.”
33 Now, the people who heard this, were struck with awe at his doctrine.
Da taron suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
34 Meantime, the Pharisees hearing that he had silenced the Sadducees, flocked about him.
Amma da Farisawan suka ji cewa Yesu ya kure Sadukiyawa, sai suka tattara kansu.
35 Then, one of them, a lawyer, trying him, proposed this question,
Daya daga cikinsu, masanin shari'a, yayi masa tambaya, yana gwada shi-
36 Rabbi, which is the greatest commandment in the law?
“Mallam, wace doka ce mafi girma a cikin shari'a?”
37 Jesus answered, "You shall love the Lord your God with all your heart, and with all your soul, and with all your mind."
Yesu yace masa, “Ka kaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.'
38 This is the first and greatest commandment.
Wannan itace babbar doka ta farko.
39 The second is like it, "You shall love your neighbor as yourself."
Doka ta biyu kuma kamar ta take- 'Ka kaunaci makwabcinka kamar kanka.'
40 On these two commandments the whole law and the prophets depend.
Akan wadannan dokoki ne dukkan shari'a da annabawa suka rataya.”
41 While the Pharisees were assembled, Jesus asked them,
Yayin da Farisawa suke tattare wuri daya, Yesu yayi masu tambaya.
42 saying, What do you think of the Messiah? Who son should he be? They answered, David's.
Yace, “Me kuke tunani game da Almasihu? Shi dan wanene?” Suka ce masa, ''Dan Dauda ne.”
43 He replied, How then does David, speaking by inspiration, call him his Lord?
Yesu yace masu, “To ta yaya kuma Dauda cikin Ruhu ya kira shi Ubangiji, yana cewa,
44 "The Lord," says he, "said to my Lord, Sit at my right hand until I make your foes your footstool."
“Ubangiji ya cewa wa Ubangijina, zauna a hannun damana, har sai na mai da makiyanka matakin sawayenka.”
45 If the Messiah were David's son, would David call him his Lord?
Idan Dauda ya kira Almasihu 'Ubangiji,' ta yaya ya zama dan Dauda?”
46 To this none of them could answer; and from that day no person presumed to interrogate him.
Ba wanda ya iya bashi amsa, ba kuma wanda ya kara yi masa tambayoyi tun daga wannan rana.