< Luke 21 >

1 As Jesus was observing the rich casting their gifts into the treasury,
Yesu ya tada ido sai ya ga mutane masu arziki wadanda suke saka baikonsu a cikin ma'aji.
2 he saw an indigent widow throw in two mites.
Ya ga wata gwauruwa matalauciya tana saka anini biyu a ciki.
3 And he said, I tell you, truly, that this poor widow has cast in more than any of them;
Sai ya ce, “Gaskiya ina gaya maku, wannan matalauciyar gwauruwa ta saka fiye da dukansu.
4 for all of these, out of their superfluous store, have thrown into the sacred chest, she has thrown in all the little that she had.
Duka wadannan sun bayar da baikonsu daga cikin yalwarsu. Amma wannan gwauruwan, daga cikin talaucin ta, ta saka dukan iyakar kudinta na zaman gari da take da shi.”
5 Some having remarked, that the temple was adorned with beautiful stones and presents, he said,
Kamar yadda wadansu suke maganan haikali, yadda aka yi masa ado da duwatsu masu daraja da bayebaye, ya ce,
6 The time will come, when these things which you behold, shall be razed that one stone will not be left upon another.
“Game da wadannan abubuwa da ku ke gani, rana tana zuwa da ba dutse ko daya da zai zauna kan dan'uwansa da ba za a rushe kasa ba.”
7 Then they asked him, saying, Rabbi, when will these things be: and what will be the sign, when they are about to be accomplished?
Sai suka yi masa tambaya, cewa, “Malam, yaushe ne wadannan abubuwan zasu faru? Menene kuma zai zama alama sa'adda wadannan abubuwa suna shirin faruwa?”
8 He answered, Take care that you be not seduced: for many will assume my character, saying, I am the person, and the time approaches; therefore, do not follow them.
Yesu ya amsa, “Ku yi hankali kada a rude ku. Gama dayawa zasu zo a cikin sunana, suna cewa, 'Ni ne shi,' kuma, 'Lokaci ya yi kusa.' Kada ku bi su.
9 But when you shall hear of wars and insurrections, be not terrified: for these things must first happen; but the end will not immediately follow.
Sa'adda ku ka ji game da yakoki da hargitsi, kada ku firgita, dole ne wadannan abubuwa su faru tukuna, amma karshe ba zai faru nan da nan ba.”
10 He added, Then will nation rise against nation, and kingdom against kingdom.
Sa'annan ya ce masu, “Al'umma za ta tasar ma al'umma, mulki kuma za ya tasar wa mulki.
11 And there shall be great earthquakes in sundry places, and famines, and pestilences; there shall be also frightful appearances, and great prodigies in the sky.
Za a yi babbar girgizan kasa, a wurare dabam dabam kuma za a yi yunwa da annoba. Za a yi al'amura masu ban tsoro da manyan alamu daga sama.
12 But, before all this, you shall be apprehended and prosecuted, and delivered to synagogues, and imprisoned, and dragged before kings and governors, because of my name:
Amma kafin abubuwan nan duka, za su kama ku, su kuma tsananta maku, suna mika ku ga majami'u da kuma gidajen kurkuku, za su kawo ku gaban sarakuna da gwamnoni saboda sunana.
13 and this afford scope for your testimony.
Zai zamar maku zarafin shaida.
14 Be, therefore, resolved not to premeditate what defense you shall make;
Saboda haka ku kudurta a ranku kada ku shirya yadda za ku amsa,
15 for I will give you an utterance, and wisdom, which none of your adversaries shall be able to refute or resist.
gama ni zan ba ku kalmomi da hikima, wadda dukan makiyanku ba za su yi tsayayya ko su karyata ku ba.
16 And you shall be given up even by parents, and brothers, and kinsmen, and friends; and some of you will be put to death.
Amma har da mahaifa da 'yan'uwa da dangi da abokai za su bashe ku, su kuma kashe wadansun ku.
17 And, on my account, you shall be universally hated.
Kowa zai ki ku saboda sunana.
18 Yet not a hair of your head shall be lost.
Amma ba ko gashin kanku da zai hallaka.
19 Save your souls by your perseverance.
A cikin hankurin ku za ku ribato rayukanku.
20 Now, when you shall see Jerusalem invested with armies, know that its desolation is nigh.
Sa'adda ku ka ga Urushalima tana kewaye da sojoji, sai ku sani da cewa faduwarta ta yi kusa.
21 Then let those in Judea flee to the mountains; let those in the city make their escape, and let not those in the country enter the city:
Sai wadanda su ke Yahudiya su gudu zuwa kan tuddai, wadanda suke tsakiyar gari kuma su tafi, kada su bar wadanda suke kauyuka su shigo ciki.
22 for these will be days of vengeance, in which all the denunciations of the scriptures shall be accomplished.
Gama wadannan ranakun ramako ne, saboda duka abubuwan da aka rubuta su cika.
23 But, alas, for the women with child, and for them who give suck in those days! for there shall be great distress in the land, and wrath upon this people.
Kaiton wadanda suke da juna biyu da masu ba da mama a wannan kwanakin! Gama za a sha kunci mai girma a kasan, da fushi kuma zuwa ga mutanen nan.
24 They shall fall by the sword; they shall be carried captive into all nations; and Jerusalem shall be trodden by the Gentiles, until the times of the Gentiles be over.
Za su fadi ta kaifin takobi kuma za a kai su cikin bauta ga dukan kasashe, al'ummai za su tattake Urushalima, har ya zuwa lokacin al'ummai ya cika.
25 And there shall be signs in the sun, and in the moon, and in the stars; and upon the earth, the anguish of desponding nations; and roarings in the seas, and floods;
Za a ga alamomi cikin rana da wata da kuma taurari. A duniya kuma, al'ummai za su sha kunci, za su rude saboda rurin teku da rakuman ruwa.
26 men expiring with the fear and apprehension of those things which are coming upon the world; for the powers of heaven shall be shaken.
Mutane za su suma da tsoro da kuma da tunanin abubuwa da za su abko wa duniya. Gama za a girgiza ikokin sammai.
27 Then they shall see the Son of Man coming in a cloud with great glory and power.
Sa'annan za su ga Dan Mutum yana zuwa a cikin gajimarai da iko da daukaka mai girma.
28 Now when these things begin to be fulfilled, look up, and lift up your heads; because your deliverance approaches.
Amma sa'adda wadannan abubuwa suka fara faruwa, tashi saye, sai ku daga kanku sama, saboda ceton ku ya kusato.”
29 He proposed to them, also, this comparison: Consider the fig tree, and the other trees.
Yesu ya bada misali, “Duba itacen baure, da duka itatuwa.
30 When you observe them shooting forth, you know, of yourselves, that the summer is nigh.
Sa'adda su ke fitar da ganye, za ku gani da kanku cewa bazara ta yi kusa kuma.
31 Know, in like manner, when you shall see these events, that the Reign of God is nigh.
Haka kuma, sa'adda ku ka ga wadannan abubuwa suna faruwa, ku sani cewa mulkin Allah ya yi kusa.
32 Indeed, I say to you, that this race shall not fail until all be accomplished.
Gaskiya, na ke gaya maku, wannan zamani ba za ya shude ba, sai duka abubuwan nan sun faru.
33 Heaven and earth shall fail; but my words shall not fail.
Sama da kasa za su shude, amma maganata ba za ta shude ba.
34 Take heed, therefore, to yourselves, lest your hearts be overcharged with surfeiting, and drunkenness, and worldly cares, and that day come upon you unawares: for, as a net,
Amma ku lura da kanku, domin kada ku nawaita zuciyarku da tararradin duniya da shayeshaye da damuwa ta rayuwa. Gama ranar za ta zo babu shiri
35 it shall inclose all the inhabitants of the earth.
kamar tarko. Gama zai zo akan kowa da ke rayuwa a fuskar dukan duniya.
36 Be vigilant, therefore, praying on every occasion, that you may be accounted worthy to escape all these approaching evils, and to stand before the Son of Man.
Amma ku zama a fadake kowanne lokaci, kuna addu'a domin ku iya samun karfin tserewa dukan wadannan abubuwa da za su faru, da kuma yadda za ku tsaya a gaban Dan Mutum.”
37 Thus Jesus taught in the temple by day, but retired at night to the mountain, called the Mount of Olives.
Da rana yana koyarwa a cikin haikali, dukan dare kuma yakan tafi dutsen da a ke kira zaitun.
38 And every morning the people resorted early to the temple to hear him.
Dukan mutane suka rika zuwa wurinsa da sassafe domin su ji shi a haikali.

< Luke 21 >