< Philippians 4 >
1 So then, my brothers, beloved and longed for, my joy and garland, so stand in the LORD, beloved.
Saboda haka’yan’uwana, ku da nake ƙauna, nake kuma marmarin ganinku, ku da kuke farin cikina da kuma rawanina, ku dāge ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna!
2 I exhort Euodia, and I exhort Syntyche, to be of the same mind in the LORD;
Ina roƙon Yuwodiya ina kuma roƙon Sintike, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne.
3 and I also ask you, genuine yoke-fellow, be assisting those women who strove along with me in the good news, with Clement also, and the others, my fellow-workers, whose names [are] in [the] Scroll of Life.
I, ina kuma roƙonka, abokin famata, ka taimaki matan nan waɗanda suka yi fama aikin bishara tare da ni, haka ma Kilemen da kuma sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suna cikin littafin rai.
4 Rejoice in the LORD always; again I will say, rejoice!
Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki!
5 Let your reasonableness be known to all men; the LORD [is] near;
Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa.
6 be anxious for nothing, but in everything by prayer, and by supplication, with thanksgiving, let your requests be made known to God;
Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.
7 and the peace of God, that is surpassing all understanding, will guard your hearts and your thoughts in Christ Jesus.
Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
8 As to the rest, brothers, as many things as are true, as many as [are] revered, as many as [are] righteous, as many as [are] pure, as many as [are] lovely, as many as [are] of good report, if any worthiness, and if any praise, think on these things;
A ƙarshe,’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.
9 the things that you also learned, and receive, and hear, and saw in me, do those, and the God of peace will be with you.
Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.
10 And I rejoiced in the LORD greatly, that now at length you flourished again in caring for me, for which also you were caring, and lacked opportunity;
Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba.
11 I do not say that in respect of want, for I learned in the things in which I am—to be content;
Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali.
12 I have known both to be abased, and I have known to abound; in everything and in all things I have been initiated, both to be full and to be hungry, both to abound and to be in want.
Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara.
13 I have strength for all things, in Christ’s strengthening me;
Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.
14 but you did well, having shared in my tribulation;
Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina.
15 and you have known, even you Philippians, that in the beginning of the good news when I went forth from Macedonia, no assembly communicated with me in regard to giving and receiving except you only;
Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai;
16 because in Thessalonica also, both once and again you sent to my need;
gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata.
17 not that I seek after the gift, but I seek after the fruit that is overflowing to your account;
Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku.
18 and I have all things, and abound; I am filled, having received from Epaphroditus the things from you—an odor of a refreshing fragrance—a sacrifice acceptable, well-pleasing to God:
An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai.
19 and my God will supply all your need, according to His riches in glory in Christ Jesus;
Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.
20 and to God, even our Father, [is] the glory through the ages of the ages. Amen. (aiōn )
Ɗaukaka ta tabbata ga Allahnmu da Ubanmu har abada abadin. Amin. (aiōn )
21 Every holy one in Christ Jesus greets you; the brothers with me greet you;
Ku gai da dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu.’Yan’uwan da suke tare da ni suna gaishe ku.
22 all the holy ones greet you, and especially those of Caesar’s house.
Dukan tsarkaka suna gaishe ku, musamman waɗanda suke na gidan Kaisar.
23 The grace of our Lord Jesus Christ [is] with you all! Amen.
Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku. Amin.