< Leviticus 22 >

1 And YHWH speaks to Moses, saying,
Ubangiji ya ce wa Musa,
2 “Speak to Aaron and to his sons, and they are separated from the holy things of the sons of Israel, and they do not defile My holy Name in what they are hallowing to Me; I [am] YHWH.
“Faɗa wa Haruna da’ya’yansa maza, su lura da tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka keɓe gare ni da bangirma, saboda ba za su ƙazantar da sunana mai tsarki ba. Ni ne Ubangiji.
3 Say to them: Throughout your generations, any man who draws near, out of all your seed, to the holy things which the sons of Israel sanctify to YHWH, and his uncleanness [is] on him—indeed, that person has been cut off from before My face; I [am] YHWH.
“Faɗa musu cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, in wani zuriyarku ya ƙazantu, duk da haka ya kusaci tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka keɓe ga Ubangiji, dole a raba wannan mutum daga gabana. Ni ne Ubangiji.
4 Any man of the seed of Aaron, and he is leprous or has discharging—he does not eat of the holy things until he is clean; and he who is coming against any uncleanness of a person, or a man whose seed [from] intercourse goes out from him,
“‘In zuriyar Haruna yana da kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,
5 or a man who comes against any teeming thing which is unclean to him, or against a man who is unclean to him, even any of his uncleanness—
da duk kuma wanda ya taɓa wani abu mai rarrafe wanda yake ƙazantarwa, ko kuwa wani mutum mai ƙazanta,
6 the person who comes against it has even been unclean until the evening, and does not eat of the holy things, but has bathed his flesh with water,
duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har yamma, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka tukuna.
7 and the sun has gone in, and he has been clean, and afterward he eats of the holy things, for it [is] his food;
Sa’ad da rana ta fāɗi, zai zama tsarkakakke, bayan wannan kuwa zai iya cin tsarkakakkun hadayu, gama abincinsa ne.
8 he does not eat a carcass or torn thing, to become unclean with it; I [am] YHWH.
Kada yă ci wani abin da ya mutu mushe, ko wanda namun jeji suka yayyaga, don kada yă ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji.
9 And they have kept My charge, and bear no sin for it, that they have died for it when they defile it; I [am] YHWH sanctifying them.
“‘Firistoci za su kiyaye umarnaina don kada su yi laifi su mutu saboda sun rena su. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da su masu tsarki.
10 And no stranger eats of the holy thing; a settler [with] a priest and a hired worker does not eat of the holy thing;
“‘Duk wanda ba daga cikin iyalin firistoci ba, ko da yake yana zama tare da su, ko kuwa an ɗauke shi yana yin musu aiki, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun hadayun ba.
11 but when a priest buys a person, the purchase of his money, he eats of it, also one born in his house; they eat of his bread.
Amma in firist ya sayi bawa da kuɗi, ko kuwa in an haifi bawan a gidansa, wannan bawan zai iya cin tsattsarkan abincin.
12 And a priest’s daughter, when she is a strange man’s, she does not eat of the raised-offering of the holy things;
In’yar firist ta auri wani da ba firist ba, ba za tă ci wani tsarkakakkun sadaka ba.
13 but a priest’s daughter, when she is a widow, or cast out, and has no seed, and has turned back to the house of her father, as [in] her youth, she eats of her father’s bread; but no stranger eats of it.
Amma idan’yar firist ta zama gwauruwa ko sakakkiya, ba ta da’ya’ya, ta kuwa dawo don tă zauna a gidan mahaifinta kamar matashiya, za tă iya cin abincin.
14 And when a man eats of a holy thing through ignorance, then he has added its fifth part to it, and has given [it] to the priest, with the holy thing;
“‘In wani ya ci tsarkakakken abinci cikin kuskure, dole yă maido wa firist hadayar, yă kuma ƙara kashi ɗaya bisa biyar na tamanin abin.
15 and they do not defile the holy things of the sons of Israel—that which they lift up to YHWH,
Firist ɗin ba zai ƙasƙantar da tsarkakakkun hadayun da Isra’ilawa suka kawo ga Ubangiji
16 or have caused them to bear the iniquity of the guilt-offering in their eating their holy things; for I [am] YHWH, sanctifying them.”
ta wurin barinsu su ci tsarkakakkun hadayu, ta yin haka su jawo wa kansu laifin da zai bukaci biya ba. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.’”
17 And YHWH speaks to Moses, saying,
Ubangiji ya ce wa Musa,
18 “Speak to Aaron, and to his sons, and to all the sons of Israel, and you have said to them: Any man of the house of Israel, or of the sojourners in Israel, who brings his offering near, of all his vows, or of all his willing offerings which they bring near to YHWH for a burnt-offering—
“Yi wa Haruna da’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa magana ka ce musu, ‘In waninku, ko mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a Isra’ila, ya kawo kyauta don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko don yă cika alkawari, ko kuwa a matsayin hadaya ta yardar rai,
19 [you bring near] at your pleasure a perfect one, a male of the herd, of the sheep or of the goats;
dole ku miƙa dabba namiji marar lahani, daga shanu, tumaki, ko awaki, domin yă zama yardajje a madadinku.
20 nothing in which [is] blemish do you bring near, for it is not for a pleasing thing for you.
Kada ku kawo wani abu mai lahani, domin ba zai zama yardajje ba a madadinku.
21 And when a man brings a sacrifice of peace-offerings near to YHWH, to complete a special vow, or for a willing-offering, of the herd or of the flock, it is perfect for a pleasing thing: no blemish is in it.
Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta salama daga garken shanu, ko na tumaki, ga Ubangiji don yă cika wani alkawari na musamman, ko hadaya ta yardar rai, dole yă zama marar lahani, ko tabo, don yă zama yardajje.
22 Blind, or broken, or maimed, or [having] an oozing sore [[or a defect of the eye]], or itch, or scab—you do not bring these near to YHWH, and you do not make a fire-offering from them on the altar to YHWH.
Kada ku miƙa wa Ubangiji dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko masu gundumi, ko masu ɗiga, ko masu susa, ko masu kirci. Kada ku sa wani daga cikin waɗannan a bisa bagade a matsayin hadaya, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
23 As for an ox or sheep [that] is deformed or stunted—you make it a willing-offering, but it is not pleasing for a vow.
Za ku iya miƙa hadaya ta yardar rai da maraƙi, ko tunkiya mai naƙasa, ko marar cikakken lafiya, amma ba za tă zama yardajje don cika alkawarin da aka yi ba.
24 As for bruised, or beaten, or torn, or cut—you do not bring [it] near to YHWH; and in your land you do not do it.
Ba za ku miƙa wa Ubangiji dabbar da lunsayinta yake da ƙujewa, ko dandaƙewa, ko yagewa, ko yankewa ba.
25 And you do not bring the bread of your God near from the hand of a son of a stranger, from any of these, for their corruption [is] in them; blemish [is] in them; they are not pleasing for you.”
Ba za ku kuma karɓi irin waɗannan dabbobi daga hannun baƙi ku miƙa su a matsayin abinci ga Allahnku ba. Ba za su zama yardajje a madadinku ba, domin sun naƙasa, suna kuma da lahani.’”
26 And YHWH speaks to Moses, saying,
Ubangiji ya ce wa Musa,
27 “When ox, or lamb, or goat is born, and it has been under its mother [for] seven days, then from the eighth day and from now on, it is pleasing for an offering, a fire-offering to YHWH;
“Sa’ad da aka haifi ɗan maraƙi, tunkiya, ko akuya, sai yă kasance da mahaifiyarsa kwana bakwai. Daga rana ta takwas zuwa gaba, zai zama yardajje hadaya, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
28 but an ox or sheep—you do not slaughter it and its young one in one day.
Kada a yanka saniya, ko tunkiya da ɗanta rana ɗaya.
29 And when you sacrifice a sacrifice of thanksgiving to YHWH, you sacrifice at your pleasure;
“Sa’ad da kuka miƙa hadaya ta godiya ga Ubangiji, ku miƙa ta a yadda za tă zama yardajje a madadinku.
30 it is eaten on that day—you do not leave of it until morning; I [am] YHWH.
Dole a ci hadayar a ranar; kada a bar saura sai da safe. Ni ne Ubangiji.
31 And you have kept my commands and have done them; I [am] YHWH;
“Ku kiyaye dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji.
32 and you do not defile My holy Name, and I have been hallowed in the midst of the sons of Israel; I [am] YHWH, sanctifying you,
Kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Dole Isra’ilawa su gane Ni mai tsarki ne. Ni ne Ubangiji, wanda ya keɓe ku a matsayin tsarkaka
33 who am bringing you up out of the land of Egypt, to become your God; I [am] YHWH.”
da kuma wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji.”

< Leviticus 22 >