< 1 Peter 5 >

1 Elders who [are] among you, I exhort [you], [as] a fellow-elder, and a witness of the sufferings of the Christ, and a partaker of the glory about to be revealed,
Zuwa ga dattawan da suke cikinku, ina roƙo a matsayin ɗan’uwanku dattijo, mashaidin shan wahalar Kiristi wanda kuma shi ma zai sami rabo cikin ɗaukakar da za a bayyana.
2 feed the flock of God that [is] among you, overseeing not by compulsion, but willingly, neither for shameful gain, but eagerly,
Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula, ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima;
3 neither as exercising lordship over the heritages, but becoming patterns for the flock,
ban da nuna iko a kan waɗanda aka danƙa muku amana, sai dai ku zama gurbi ga garken.
4 and the Chief Shepherd having appeared, you will receive the unfading garland of glory.
Sa’ad da kuwa Babban Makiyayin ya bayyana, za ku karɓi rawanin ɗaukaka marar koɗewa.
5 In like manner, you young [ones], be subject to elders, and all subjecting yourselves to one another; clothe yourselves with humble-mindedness, because God resists the proud, but He gives grace to the humble;
Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin, “Allah yana gāba da mai girman kai, amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.”
6 be humbled, then, under the powerful hand of God, that He may exalt you in good time,
Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama.
7 having cast all your care on Him, because He cares for you.
Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.
8 Be sober, vigilant, because your opponent the Devil walks around as a roaring lion, seeking whom he may swallow up,
Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye.
9 whom you must resist, steadfast in the faith, having known the same sufferings of your brotherhood to be accomplished in the world.
Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.
10 And the God of all grace, who called you to His perpetual glory in Christ Jesus, having suffered a little, Himself make you perfect, establish, strengthen, settle [you]; (aiōnios g166)
Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yă kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram. (aiōnios g166)
11 to Him [is] the glory and the power through the ages and the ages! Amen. (aiōn g165)
Gare shi bari iko yă tabbata har abada abadin. Amin. (aiōn g165)
12 Through Silvanus, the faithful brother as I reckon, I wrote through few [words] to you, exhorting and testifying this to be the true grace of God in which you have stood.
Da taimakon Sila, wanda na ɗauka a matsayin ɗan’uwa mai aminci, na rubuta muku a taƙaice, ina ƙarfafa ku ina kuma shaida muku cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske. Ku tsaya daram a cikinsa.
13 She in Babylon chosen with you greets you, and my son Marcus.
Ita wadda take a Babilon, zaɓaɓɓiya tare da ku, tana gaishe ku, haka ma ɗana Markus.
14 Greet one another in a kiss of love. Peace to you all who [are] in Christ Jesus! Amen.
Ku gai da juna da sumbar ƙauna. Salama gare ku duka da kuke cikin Kiristi.

< 1 Peter 5 >