< Ezekiel 2 >

1 And he said unto me, Son of man, stand upon thy feet, and I will speak unto thee.
Ya ce mini, “Ɗan mutum, tashi ka tsaya a ƙafafunka zan kuma yi maka magana.”
2 And the spirit entered into me when he spake unto me, and set me upon my feet, that I heard him that spake unto me.
Yayinda yake magana, sai Ruhu ya sauko mini ya kuma tā da ni a ƙafafuna, na kuma ji shi yana mini magana.
3 And he said unto me, Son of man, I send thee to the children of Israel, to a rebellious nation that hath rebelled against me: they and their fathers have transgressed against me, [even] unto this very day.
Ya ce, “Ɗan mutum, ina aikan ka zuwa ga Isra’ilawa, zuwa ga al’ummar’yan tawayen nan da suka yi mini tayarwa; su da kakanninsu sun yi mini tawaye har yă zuwa yau.
4 For [they are] impudent children and stiffhearted. I do send thee unto them; and thou shalt say unto them, Thus saith the Lord GOD.
Mutanen da nake aikan ka masu ƙin ji ne da kuma taurinkai. Ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’
5 And they, whether they will hear, or whether they will forbear, (for they [are] a rebellious house, ) yet shall know that there hath been a prophet among them.
Kuma ko su ji ko kada su ji, gama su gida ne mai tawaye, za su san cewa akwai annabi a cikinsu.
6 And thou, son of man, be not afraid of them, neither be afraid of their words, though briers and thorns [be] with thee, and thou dost dwell among scorpions: be not afraid of their words, nor be dismayed at their looks, though they [be] a rebellious house.
Kai kuwa, ɗan mutum, kada ka ji tsoro, ko da sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa duk sun kewaye ka kana kuma zama a cikin kunamai. Kada ka ji tsoron abin da za ka faɗa ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gida ne mai tawaye.
7 And thou shalt speak my words unto them, whether they will hear, or whether they will forbear: for they [are] most rebellious.
Dole ka yi maganata gare su, ko su ji ko kada su ji, gama su’yan tawaye ne.
8 But thou, son of man, hear what I say unto thee; Be not thou rebellious like that rebellious house: open thy mouth, and eat that I give thee.
Amma kai, ɗan mutum, ka saurari abin da zan faɗa maka. Kada ka yi tawaye kamar wannan gidan’yan tawaye; ka buɗe bakinka ka kuma ci abin da na ba ka.”
9 And when I looked, behold, an hand [was] sent unto me; and, lo, a roll of a book [was] therein;
Sai na duba, na kuma ga hannu ya miƙe zuwa wurina. A cikinsa akwai littafi,
10 And he spread it before me; and it [was] written within and without: and [there was] written therein lamentations, and mourning, and woe.
wanda ya nannaɗe a gabana. A kowane gefensa akwai rubutun kalmomin makoki da kuka da kuma kaito.

< Ezekiel 2 >