< Acts 12 >

1 Now about that time Herod the king stretched forth [his] hands to vex certain of the church.
A lokacin nan Sarki Hiridus ya sa wa wasu masu bi hannu domin ya musguna masu.
2 And he killed James the brother of John with the sword.
Ya kashe Yakubu dan'uwan Yahaya da takobi.
3 And because he saw it pleased the Jews, he proceeded further to take Peter also. (Then were the days of unleavened bread.)
Bayan da ya ga hakan ya gamshi Yahudawa, sai ya kama Bitrus ma.
4 And when he had apprehended him, he put [him] in prison, and delivered [him] to four quaternions of soldiers to keep him; intending after Easter to bring him forth to the people.
Bayan ya kama shi, sai ya tsare shi a kurkuku ya kuwa sa sojoji hudu su dinga tsaron sa; yana niyyar kawo shi gaban mutanen a bayan Idin katarewa.
5 Peter therefore was kept in prison: but prayer was made without ceasing of the church unto God for him.
To, Bitrus na tsare a kurkuku, amma 'yan'uwa na iklisiya suna yin addu'a ga Allah sosai domin sa.
6 And when Herod would have brought him forth, the same night Peter was sleeping between two soldiers, bound with two chains: and the keepers before the door kept the prison.
Ana kamar gobe Hiridus zai fitar da shi, a wannan daren, Bitrus yana barci a tsakanin sojoji biyu, daure da sarkoki biyu; sojoji kuma na gadi a bakin kurkukun.
7 And, behold, the angel of the Lord came upon [him], and a light shined in the prison: and he smote Peter on the side, and raised him up, saying, Arise up quickly. And his chains fell off from [his] hands.
Ba zato, sai ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gareshi, haske ya haskaka dakin. Ya taba Bitrus a gefe ya tashe shi kuma ya ce, “Tashi da sauri.” Sai ga sarkokin suka zube daga hannunsa.
8 And the angel said unto him, Gird thyself, and bind on thy sandals. And so he did. And he saith unto him, Cast thy garment about thee, and follow me.
Mala'ikan ya ce masa, “Yi damara ka sa takalmanka.” Bitrus kuwa yayi haka. Mala'ikan ce ma sa, “Yafa mayafinka, ka biyo ni.”
9 And he went out, and followed him; and wist not that it was true which was done by the angel; but thought he saw a vision.
Bitrus kuwa ya bi mala'ikan suka fita waje. Bai gane abin da mala'ikan ke yi zahiri ne ba. Yana zaton ko yana ganin wahayi ne.
10 When they were past the first and the second ward, they came unto the iron gate that leadeth unto the city; which opened to them of his own accord: and they went out, and passed on through one street; and forthwith the angel departed from him.
Bayan da suka wuce masu tsaron fari da na biyu, sun kai kofar da aka yi da karfe wadda ta mike zuwa cikin gari; ta bude masu da kanta. Suka fita sun bi titin, kuma nan take kuma sai mala'ikan ya bar shi.
11 And when Peter was come to himself, he said, Now I know of a surety, that the Lord hath sent his angel, and hath delivered me out of the hand of Herod, and [from] all the expectation of the people of the Jews.
Da Bitrus ya komo hayyacin sa, ya ce, “Hakika yanzu na gane Ubangiji ya aiko da mala'ikansa don ya kubutar da ni daga hannun Hiridus da abin da Yahudawa suke zato.”
12 And when he had considered [the thing], he came to the house of Mary the mother of John, whose surname was Mark; where many were gathered together praying.
Da ya gane haka, ya zo gidan Maryamu mahaifiyar Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus; masu bi da yawa sun taru a can suna addu'a.
13 And as Peter knocked at the door of the gate, a damsel came to hearken, named Rhoda.
Da ya kwankwasa kofar gidan, sai baiwar gidan mai suna Roda ta zo don ta bude kofar.
14 And when she knew Peter’s voice, she opened not the gate for gladness, but ran in, and told how Peter stood before the gate.
Da ta gane muryar Bitrus, don farin ciki ta kasa bude kofar; maimakon haka, ta koma daki a guje, don ta basu labari Bitrus na tsaye a bakin kofa.
15 And they said unto her, Thou art mad. But she constantly affirmed that it was even so. Then said they, It is his angel.
Suka ce mata, “Kin haukace.” Amma ta nace da cewa haka ne. Suka ce, “Mala'ikansa ne.”
16 But Peter continued knocking: and when they had opened [the door], and saw him, they were astonished.
Amma Bitrus ya ci gaba da kwankwasawa, da suka bude kofar, sai suka ga ai shine, suka sha mamaki kwarai.
17 But he, beckoning unto them with the hand to hold their peace, declared unto them how the Lord had brought him out of the prison. And he said, Go shew these things unto James, and to the brethren. And he departed, and went into another place.
Bitrus kuwa ya yi masu hannu yana, masu alama su yi shuru. Sai ya gaya masu labarin yadda Ubangiji ya kubutar da shi daga kurkukun. Ya ce, “Ku gaya wa Yakubu da dukan 'yan'uwa abin da ya faru.” Sai ya bar su, ya tafi wani wuri.
18 Now as soon as it was day, there was no small stir among the soldiers, what was become of Peter.
Sa'anda gari ya waye ba karamar hargowa ce ta tashi a cikin sojojin ba, game da abin da ya faru da Bitrus.
19 And when Herod had sought for him, and found him not, he examined the keepers, and commanded that [they] should be put to death. And he went down from Judæa to Cæsarea, and [there] abode.
Bayan da Hiridus ya neme shi kuma bai same shi ba, sai ya tambayi masu tsaron kuma ya bada umarni a kashe su. Sai ya gangara daga Yahudiya zuwa Kaisariya ya yi zamansa a can.
20 And Herod was highly displeased with them of Tyre and Sidon: but they came with one accord to him, and, having made Blastus the king’s chamberlain their friend, desired peace; because their country was nourished by the king’s [country].
Yanzu kuwa Hiridus ya yi fushi sosai da mutanen Taya da Sidon. Suka tafi wurinsa tare. Suka roki Bilastasa, mataimakin sarkin, ya taimake su. Sai suka nemi sasantawa don suna samun abinci daga kasarsa ne.
21 And upon a set day Herod, arrayed in royal apparel, sat upon his throne, and made an oration unto them.
A ranan da aka kayyade, Hirudus ya sha damara da kayan saurata kuma ya zauna akan kursiyi; ya yi masu jawabi.
22 And the people gave a shout, [saying, It is] the voice of a god, and not of a man.
Mutanen suka yi ihu, “Wannan muryar allahce, ba ta mutum ba!”
23 And immediately the angel of the Lord smote him, because he gave not God the glory: and he was eaten of worms, and gave up the ghost.
Nan take mala'ika Ubangiji ya buge shi don bai ba Allah daukaka ba, nan take tsutsotsi suka cinye shi har ya mutu.
24 But the word of God grew and multiplied.
Maganar Allah ta yadu tana ta ribabbanya.
25 And Barnabas and Saul returned from Jerusalem, when they had fulfilled [their] ministry, and took with them John, whose surname was Mark.
Bayan Barnaba da Shawulu sun gama aikin su a Urushalima. Suna dawowa, suka zo tare da Yahaya wanda sunan mahaifinsa Markus ne. [Barnaba da Shawulu suka koma Urushalima.]

< Acts 12 >