< Numbers 17 >

1 AND the Lord spake unto Moses, saying,
Ubangiji ya ce wa Musa,
2 Speak unto the children of Israel, and take of every one of them a rod according to the house of their fathers, of all their princes according to the house of their fathers twelve rods: write thou every man’s name upon his rod.
“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka kuma karɓi sanduna goma sha biyu daga wurinsu, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu. Ka rubuta sunan kowa a sandansa.
3 And thou shalt write Aaron’s name upon the rod of Levi: for one rod shall be for the head of the house of their fathers.
A kan sandan Lawi kuwa ka rubuta sunan Haruna, gama dole a sami sanda ɗaya saboda shugaban gidan kakanninsu.
4 And thou shalt lay them up in the tabernacle of the congregation before the testimony, where I will meet with you.
Ka ajiye su a Tentin Sujada, a gaba akwatin Alkawari, inda zan sadu da kai.
5 And it shall come to pass, that the man’s rod, whom I shall choose, shall blossom: and I will make to cease from me the murmurings of the children of Israel, whereby they murmur against you.
Sandan mutumin da na zaɓa zai yi toho, da haka zan raba kaina da gunagunin da Isra’ilawa suke yi.”
6 And Moses spake unto the children of Israel, and every one of their princes gave him a rod apiece, for each prince one, according to their fathers’ houses, even twelve rods: and the rod of Aaron was among their rods.
Saboda haka Musa ya yi magana da Isra’ilawa, sai shugabanninsu suka ba shi sanduna goma sha biyu, sanda ɗaya don shugaba, bisa ga gidajen kakanninsu, sandan Haruna kuma yana a cikinsu.
7 And Moses laid up the rods before the Lord in the tabernacle of witness.
Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada.
8 And it came to pass, that on the morrow Moses went into the tabernacle of witness; and, behold, the rod of Aaron for the house of Levi was budded, and brought forth buds, and bloomed blossoms, and yielded almonds.
Kashegari da Musa ya shiga cikin Tentin Sujada sai ga sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi’ya’yan almon.
9 And Moses brought out all the rods from before the Lord unto all the children of Israel: and they looked, and took every man his rod.
Sai Musa ya fitar wa dukan Isra’ilawa dukan sandunan da suke daga gaban Ubangiji. Suka duba, kowa kuma ya ɗauki sandansa.
10 And the Lord said unto Moses, Bring Aaron’s rod again before the testimony, to be kept for a token against the rebels; and thou shalt quite take away their murmurings from me, that they die not.
Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka mayar da sandan Haruna a akwatin Alkawari, don a ajiye shi alama ga masu tawaye. Wannan zai kawo ƙarshen gunaguninsu a kaina, domin kada su mutu.”
11 And Moses did so: as the Lord commanded him, so did he.
Musa kuwa ya aikata kamar dai yadda Ubangiji ya umarce shi.
12 And the children of Israel spake unto Moses, saying, Behold, we die, we perish, we all perish.
Sai Isra’ilawa suka ce wa Musa, “To, ai in haka ne, mun ƙare ke nan!
13 Whosoever cometh any thing near unto the tabernacle of the Lord shall die: shall we be consumed with dying?
Idan an ce duk wanda ya zo kusa da tabanakul na Ubangiji zai mutu, ai rayuwarmu kamar mun mutu ke nan.”

< Numbers 17 >