< Hosea 8 >
1 Set the horn to thy mouth. As a vulture he cometh against the house of the LORD; because they have transgressed My covenant, and trespassed against My law.
“Ka sa kakaki a leɓunanka! Gaggafa tana a bisan gidan Ubangiji domin mutane sun tā da alkawarina suka kuma tayar wa dokata.
2 Will they cry unto Me: 'My God, we Israel know Thee'?
Isra’ila ta yi mini kuka, ‘Ya Allahnmu, mun yarda da kai!’
3 Israel hath cast off that which is good; the enemy shall pursue him.
Amma Isra’ila sun ƙi abin da yake mai kyau; abokin gāba zai fafare su.
4 They have set up kings, but not from Me, they have made princes, and I knew it not; of their silver and their gold have they made them idols, that they may be cut off.
Suna naɗa sarakuna, ba da izinina ba; sun zaɓa shugabanni ba da yardanta ba. Da azurfa da zinariya sun ƙera gumaka wa kansu wanda zai kai zuwa ga hallakarsu.
5 Thy calf, O Samaria, is cast off; Mine anger is kindled against them; how long will it be ere they attain to innocency?
Ku zubar da gunkin maraƙinku, ya Samariya! Fushina yana ƙuna a kansu. Sai yaushe za su rabu da gumaka?
6 For from Israel is even this: the craftsman made it, and it is no God; yea, the calf of Samaria shall be broken in shivers.
Su daga Isra’ila ne! Wannan maraƙi, mai aikin hannu ne ya yi shi; gunki ne ba Allah ba. Za a farfashe shi kucu-kucu, waccan maraƙin Samariya.
7 For they sow the wind, and they shall reap the whirlwind; it hath no stalk, the bud that shall yield no meal; if so be it yield, strangers shall swallow it up.
“Gama sun shuka iska don haka za su girbe guguwa. Hatsin da yake tsaye ba shi da kai, ba zai yi tsaba ba. Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci.
8 Israel is swallowed up; now are they become among the nations as a vessel wherein is no value.
An haɗiye Isra’ila; yanzu tana cikin al’ummai kamar abin da ba shi da amfani.
9 For they are gone up to Assyria, like a wild ass alone by himself; Ephraim hath hired lovers.
Gama sun haura zuwa Assuriya kamar jakin jejin da yake yawo shi kaɗai. Efraim ya sayar da kansa ga maza.
10 Yea, though they hire among the nations, now will I gather them up; and they begin to be minished by reason of the burden of king and princes.
Ko da yake sun sayar da kansu a cikin al’ummai, yanzu zan tattara su wuri ɗaya. Za su fara lalacewa a ƙarƙashi danniyar babban sarki.
11 For Ephraim hath multiplied altars to sin, yea, altars have been unto him to sin.
“Ko da yake Efraim ya gina bagadai masu yawa don hadayun zunubi, waɗannan sun zama bagade don yin zunubi.
12 Though I write for him never so many things of My Law, they are accounted as a stranger's.
Na rubuta musu abubuwa masu yawa na dokata, amma suka ɗauke su tamƙar wani baƙon abu ne.
13 As for the sacrifices that are made by fire unto Me, let them sacrifice flesh and eat it, for the LORD accepteth them not. Now will He remember their iniquity, and punish their sins; they shall return to Egypt.
Suna miƙa hadayun da aka ba ni su kuma ci nama, amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu. Yanzu zai tuna da muguntarsu yă kuma hukunta zunubansu. Za su koma Masar.
14 For Israel hath forgotten his Maker, and builded palaces, and Judah hath multiplied fortified cities; but I will send a fire upon his cities, and it shall devour the castles thereof.
Isra’ila ya manta da Mahaliccinsa ya kuma gina fadodi; Yahuda ya gina katanga a yawancin garuruwansa. Amma zan aiko da wuta a bisa biranensu da zai cinye kagaransu.”