< Haggai 2 >
1 In the seventh month, in the one and twentieth day of the month, came the word of the LORD by Haggai the prophet, saying:
a ranar ashirin da ɗaya ga watan bakwai, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai cewa,
2 'Speak now to Zerubbabel the son of Shealtiel, governor of Judah, and to Joshua the son of Jehozadak, the high priest, and to the remnant of the people, saying:
“Ka yi magana da Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel wanda yake gwamna a Yahuda, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da kuma dukan raguwar mutane. Ka tambaye su ka ce,
3 Who is left among you that saw this house in its former glory? and how do ye see it now? is not such a one as nothing in your eyes?
‘Wane ne a cikinku ya ragu da ya ga wannan gida a darajarsa ta dā? Yaya yake a gare ku a yanzu? Bai yi kamar a bakin kome ba, ko ba haka ba?
4 Yet now be strong, O Zerubbabel, saith the LORD; and be strong, O Joshua, son of Jehozadak, the high priest; and be strong, all ye people of the land, saith the LORD, and work; for I am with you, saith the LORD of hosts.
Amma yanzu ka ƙarfafa, ya Zerubbabel,’ in ji Ubangiji. ‘Ka ƙarfafa, ya Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist. Ku ƙarfafa, dukanku mutanen ƙasar,’ in ji Ubangiji, ‘ku yi aiki. Gama ina tare da ku,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
5 The word that I covenanted with you when ye came out of Egypt have I established, and My spirit abideth among you; fear ye not.
‘Wannan shi ne alkawarin da na yi da ku a lokacin da kuka fito daga Masar. Ruhuna kuwa yana tare da ku. Kada ku ji tsoro.’
6 For thus saith the LORD of hosts: Yet once, it is a little while, and I will shake the heavens, and the earth, and the sea, and the dry land;
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ba da jimawa ba zan sāke girgiza sammai da kuma ƙasa, teku da busasshiyar ƙasa.
7 and I will shake all nations, and the choicest things of all nations shall come, and I will fill this house with glory, saith the LORD of hosts.
Zan girgiza dukan al’ummai, marmarin kowace al’umma kuma zai taso, sa’an nan zan cika gidan nan da ɗaukaka,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
8 Mine is the silver, and Mine the gold, saith the LORD of hosts.
‘Da zinariya da azurfa duka nawa ne,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
9 The glory of this latter house shall be greater than that of the former, saith the LORD of hosts; and in this place will I give peace, saith the LORD of hosts.'
‘Ɗaukakar gidan nan na yanzu za tă fi ɗaukakar gidan nan na dā,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘A wannan wuri kuma zan ba da salama,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.”
10 In the four and twentieth day of the ninth month, in the second year of Darius, came the word of the LORD by Haggai the prophet, saying:
A ranar ashirin da huɗu ga watan tara, a shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubangiji ta zo wa annabi Haggai cewa,
11 'Thus saith the LORD of hosts: Ask now the priests for instruction, saying:
“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ku tambayi firist abin da doka ta ce.
12 If one bear hallowed flesh in the skirt of his garment, and with his skirt do touch bread, or pottage, or wine, or oil, or any food, shall it be holy?' And the priests answered and said: 'No.'
Idan mutum yana riƙe da naman da aka keɓe a rigarsa, sa’an nan kuma wannan rigar ta taɓa burodi, ko dafaffen abinci, ko ruwan inabi, ko mai, ko kowane irin abinci, wannan zai sa abin yă zama tsarkake?’” Firistoci suka amsa, suka ce, “A’a.”
13 Then said Haggai: 'If one that is unclean by a dead body touch any of these, shall it be unclean?' And the priests answered and said: 'It shall be unclean.'
Sa’an nan Haggai ya ce, “In mutumin da ya ƙazantar da kansa ta wurin taɓa gawa, ya taɓa wani daga cikin waɗannan abubuwa, za su ƙazantu?” Firistoci suka amsa, suka ce, “I, zai ƙazantu.”
14 Then answered Haggai, and said: 'So is this people, and so is this nation before me, saith the LORD; and so is every work of their hands; and that which they offer there is unclean.
Sai annabi Haggai ya ce, “‘Haka yake da wannan mutane da kuma wannan al’umma a gabana,’ in ji Ubangiji. ‘Duk abin da suke yi da kuma dukan abin da suke miƙawa ƙazantattu ne.
15 And now, I pray you, consider from this day and forward — before a stone was laid upon a stone in the temple of the LORD,
“‘Yanzu kuwa sai ku yi la’akari da wannan daga wannan rana zuwa gaba, ku tuna yadda al’amura suke kafin a ɗora wani dutse bisa wani a haikalin Ubangiji.
16 through all that time, when one came to a heap of twenty measures, there were but ten; when one came to the winevat to draw out fifty press-measures, there were but twenty;
A lokacin, idan wani ya tafi wurin tsibin da zai auna mudu ashirin, sai yă iske mudu goma kawai. Idan kuma wani ya tafi wurin matse ruwan inabi don yă ɗebo lita hamsin, sai yă tarar da lita ashirin kawai.
17 I smote you with blasting and with mildew and with hail in all the work of your hands; yet ye turned not to Me, saith the LORD —
Na mai da aikin da kuka sha wahala kuka yi ya zama banza ta wurin saukar da burtuntuna, da fumfuna, da ƙanƙara, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,’ in ji Ubangiji.
18 consider, I pray you, from this day and forward, from the four and twentieth day of the ninth month, even from the day that the foundation of the LORD'S temple was laid, consider it;
‘Daga wannan rana zuwa gaba, wato, rana ta ashirin da huɗu ga watan tara, ku lura da ranar da aka kafa harsashin haikalin Ubangiji. Ku lura da kyau.
19 is the seed yet in the barn? yea, the vine, and the fig-tree, and the pomegranate, and the olive-tree hath not brought forth — from this day will I bless you.'
Akwai sauran irin da ya rage a rumbu? Har yanzu, kuringar inabi da itacen ɓaure, rumman da itacen zaitun ba su ba da’ya’ya ba tukuna. “‘Amma daga wannan rana zuwa gaba zan sa muku albarka.’”
20 And the word of the LORD came the second time unto Haggai in the four and twentieth day of the month, saying:
Maganar Ubangiji ta zo wa annabi Haggai sau na biyu a rana ta ashirin da huɗu ga wata cewa,
21 'Speak to Zerubbabel, governor of Judah, saying: I will shake the heavens and the earth;
“Ka faɗa wa Zerubbabel gwamnan Yahuda cewa zan girgiza sammai da ƙasa.
22 and I will overthrow the throne of kingdoms, and I will destroy the strength of the kingdoms of the nations; and I will overthrow the chariots, and those that ride in them; and the horses and their riders shall come down, every one by the sword of his brother.
Zan hamɓarar da gadajen mulki in kuma ragargaza ƙarfin ƙasashen al’ummai. Zan tumɓuke kekunan yaƙi da mahayansu; dawakai da mahayansu za su mutu, kowane ta wurin takobin ɗan’uwansu.
23 In that day, saith the LORD of hosts, will I take thee, O Zerubbabel, My servant, the son of Shealtiel, saith the LORD, and will make thee as a signet; for I have chosen thee, saith the LORD of hosts.'
“‘A wannan rana,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘Zan ɗauke ka, bawana Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel,’ in ji Ubangiji, ‘in kuma maishe ka kamar zoben hatimi, gama na zaɓe ka,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.”