< Deuteronomy 29 >
1 These are the words of the covenant which the LORD commanded Moses to make with the children of Israel in the land of Moab, beside the covenant which He made with them in Horeb.
Waɗannan su ne sharuɗan alkawarin da Ubangiji ya umarci Musa yă yi da Isra’ilawa a Mowab, wato, ban da alkawarin da ya yi da su a Dutsen Horeb.
2 And Moses called unto all Israel, and said unto them: Ye have seen all that the LORD did before your eyes in the land of Egypt unto Pharaoh, and unto all his servants, and unto all his land;
Sai Musa ya tara dukan Isra’ila, ya ce musu, Idanunku sun ga dukan abin da Ubangiji ya yi a Masar ga Fir’auna, ga kuma dukan shugabanninsa da kuma ga dukan ƙasarsa.
3 the great trials which thine eyes saw, the signs and those great wonders;
Da idanunku kun ga waɗannan gwaje-gwaje, waɗannan alamu masu banmamaki, da al’ajabai masu girma.
4 but the LORD hath not given you a heart to know, and eyes to see, and ears to hear, unto this day.
Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku hankalin ganewa, ko idanun da za su gani, ko kunnuwan da za su ji ba.
5 And I have led you forty years in the wilderness; your clothes are not waxen old upon you, and thy shoe is not waxen old upon thy foot.
Shekaru arba’in da na jagorance ku cikin hamada, tufafinku ba su yage ba, haka kuwa takalman da suke a ƙafafunku.
6 Ye have not eaten bread, neither have ye drunk wine or strong drink; that ye might know that I am the LORD your God.
Ba ku ci burodi ba, ba ku kuwa sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa jiri ba. Ya yi haka don ku san cewa shi ne Ubangiji Allahnku.
7 And when ye came unto this place, Sihon the king of Heshbon, and Og the king of Bashan, came out against us unto battle, and we smote them.
Sa’ad da kuka kai wannan wuri, Sihon sarkin Heshbon, da Og sarkin Bashan, suka fito don su yi yaƙi da mu, amma muka ci su da yaƙi.
8 And we took their land, and gave it for an inheritance unto the Reubenites, and to the Gadites, and to the half-tribe of the Manassites.
Muka ƙwace ƙasarsu, muka ba da ita gādo ga mutanen Ruben, mutanen Gad, da kuma rabin mutanen Manasse.
9 Observe therefore the words of this covenant, and do them, that ye may make all that ye do to prosper.
Saboda haka sai ku kiyaye, ku bi sharuɗan wannan alkawari, don ku yi nasara a cikin kome da kuke yi.
10 Ye are standing this day all of you before the LORD your God: your heads, your tribes, your elders, and your officers, even all the men of Israel,
Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabanninku da manyan mutanenku, dattawanku da hafsoshinku, da kuma dukan sauran mutanen Isra’ila,
11 your little ones, your wives, and thy stranger that is in the midst of thy camp, from the hewer of thy wood unto the drawer of thy water;
tare da’ya’yanku da matanku, da baƙin da suke zama sansanoninku, har ma da waɗanda suke muku faskare, da waɗanda suke ɗiba muku ruwa.
12 that thou shouldest enter into the covenant of the LORD thy God — and into His oath — which the LORD thy God maketh with thee this day;
Kuna tsaye a nan don ku yi alkawari da Ubangiji Allahnku, alkawarin da Ubangiji yake yi ta wurin rantsuwa da ku a wannan rana,
13 that He may establish thee this day unto Himself for a people, and that He may be unto thee a God, as He spoke unto thee, and as He swore unto thy fathers, to Abraham, to Isaac, and to Jacob.
don yă mai da ku jama’arsa yau, shi kuwa yă zama Allahnku kamar yadda ya yi muku alkawari, da yadda kuma ya rantse wa kakanninku, Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub.
14 Neither with you only do I make this covenant and this oath;
Ina yin wannan alkawari da rantsuwar, ba da ku kaɗai da
15 but with him that standeth here with us this day before the LORD our God, and also with him that is not here with us this day —
kuke tsattsaye a nan tare da mu a yau a gaban Ubangiji Allahnmu ba, amma har da waɗanda ba sa nan yau.
16 for ye know how we dwelt in the land of Egypt; and how we came through the midst of the nations through which ye passed;
Ku kanku kun san yadda muka yi zama a Masar, da yadda muka yi ta ratsawa ta tsakiyar al’ummai muka wuce.
17 and ye have seen their detestable things, and their idols, wood and stone, silver and gold, which were with them —
A cikinsu, kun ga siffofi masu banƙyama da gumaka na itace da dutse, na azurfa da zinariya.
18 lest there should be among you man, or woman, or family, or tribe, whose heart turneth away this day from the LORD our God, to go to serve the gods of those nations; lest there should be among you a root that beareth gall and wormwood;
Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, tă koma ga bauta wa gumakan waɗannan al’ummai. Kada a sami wani tushe mai ba da’ya’ya masu dafi, masu ɗaci a cikinku.
19 and it come to pass, when he heareth the words of this curse, that he bless himself in his heart, saying: 'I shall have peace, though I walk in the stubbornness of my heart — that the watered be swept away with the dry';
Idan kuma wani mutum ya ji kalmomi na wannan rantsuwa, ya kuma sa wa kansa albarka yana tunani cewa, “Ba abin da zai same ni, ko da na nace a taurinkaina.” Wannan zai jawo lalacewar dukan Isra’ila tare da kai.
20 the LORD will not be willing to pardon him, but then the anger of the LORD and His jealousy shall be kindled against that man, and all the curse that is written in this book shall lie upon him, and the LORD shall blot out his name from under heaven;
Ubangiji ba zai gafarce shi ba, fushinsa da kishinsa za su ƙuna a kan wannan mutum. Dukan la’anonin da aka rubuta a wannan littafi za su fāɗo a kansa, Ubangiji kuwa zai shafe sunansa daga ƙarƙashin sama.
21 and the LORD shall separate him unto evil out of all the tribes of Israel, according to all the curses of the covenant that is written in this book of the law.
Ubangiji zai ware shi daga dukan kabilan Isra’ila don yă hukunta shi bisa ga dukan la’anonin alkawarin da aka rubuta a wannan Littafin Doka.
22 And the generation to come, your children that shall rise up after you, and the foreigner that shall come from a far land, shall say, when they see the plagues of that land, and the sicknesses wherewith the LORD hath made it sick;
Tsararraki masu zuwa nan gaba, wato,’ya’yan da za su gāje ku, da baƙon da ya zo daga ƙasa mai nisa, za su ga annobar ƙasar, da cuce-cucen da Ubangiji ya buge ta da su.
23 and that the whole land thereof is brimstone, and salt, and a burning, that it is not sown, nor beareth, nor any grass groweth therein, like the overthrow of Sodom and Gomorrah, Admah and Zeboiim, which the LORD overthrew in His anger, and in His wrath;
Ƙasar gaba ɗaya za tă zama gishiri mai ƙuna marar amfani da kuma kibiritu, babu shuki, babu abin da yake tsirowa, babu itatuwan da suke girma a cikinta. Za tă zama kamar yadda aka hallaka Sodom da Gomorra, Adma da Zeboyim, waɗanda Ubangiji ya hallaka cikin zafin fushinsa.
24 even all the nations shall say 'Wherefore hath the LORD done thus unto this land? what meaneth the heat of this great anger?'
Dukan al’ummai za su yi tambaya su ce, “Me ya sa Ubangiji ya yi haka da wannan ƙasa? Me ya jawo wannan fushi mai tsanani haka?”
25 then men shall say: 'Because they forsook the covenant of the LORD, the God of their fathers, which He made with them when He brought them forth out of the land of Egypt;
Amsar kuwa za tă zama, “Wannan ya zama haka domin wannan mutane, sun yi watsi da alkawarin Ubangiji Allah na kakanninsu, alkawarin da ya yi da su sa’ad da ya fitar da su daga Masar.
26 and went and served other gods, and worshipped them, gods that they knew not, and that He had not allotted unto them;
Sun juya, suka bauta wa waɗansu alloli, suka rusuna musu, allolin da ba su sani ba, allolin da Ubangiji bai ba su ba.
27 therefore the anger of the LORD was kindled against this land, to bring upon it all the curse that is written in this book;
Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan wannan ƙasa, har ya kawo dukan la’anoni da aka rubuta a wannan littafi a kanta.
28 and the LORD rooted them out of their land in anger, and in wrath, and in great indignation, and cast them into another land, as it is this day'. —
Cikin zafin fushi da babbar hasala Ubangiji ya tumɓuke su daga ƙasarsu, ya watsar da su cikin wata ƙasa dabam, kamar yadda suke a yau.”
29 The secret things belong unto the LORD our God; but the things that are revealed belong unto us and to our children for ever, that we may do all the words of this law.
Ubangiji Allahnmu bai bayyana abubuwa na yanzu da na nan gaba ba, amma ya umarce mu mu kiyaye kalmomin dokar da ya ba mu, mu da kuma’ya’yanmu har abada.