< Deuteronomy 15 >
1 At the end of every seven years thou shalt make a release.
A ƙarshen kowace shekara ta bakwai, dole ku yafe basusuwan da kuke bi.
2 And this is the manner of the release: every creditor shall release that which he hath lent unto his neighbour; he shall not exact it of his neighbour and his brother; because the LORD'S release hath been proclaimed.
Ga yadda za ku yafe basusuwan, kowane mai bin bashi, yă yafe bashin da yake bin ɗan’uwansa mutumin Isra’ila. Ba zai bukaci mutumin Isra’ila wanda yake ɗan’uwa yă biya shi bashi ba, gama an yi shelar lokacin da Ubangiji ya ajiye na yafe bashi.
3 Of a foreigner thou mayest exact it; but whatsoever of thine is with thy brother thy hand shall release.
Za ku iya nemi baƙo yă biya ku bashin da kuke binsa, amma dole ku yafe duk wani bashin da kuke bin ɗan’uwa.
4 Howbeit there shall be no needy among you — for the LORD will surely bless thee in the land which the LORD thy God giveth thee for an inheritance to possess it —
Amma bai kamata a sami matalauci a cikinku ba, gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a ƙasar da yake ba ku, ku mallaka a matsayin gādo,
5 if only thou diligently hearken unto the voice of the LORD thy God, to observe to do all this commandment which I command thee this day.
in dai kun yi cikakken biyayya ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuna kiyaye dukan waɗannan umarnan da nake ba ku yau.
6 For the LORD thy God will bless thee, as He promised thee; and thou shalt lend unto many nations, but thou shalt not borrow; and thou shalt rule over many nations, but they shall not rule over thee.
Gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku kamar yadda ya yi alkawari, za ku kuma ba al’ummai masu yawa bashi, amma ba za ku karɓa bashi daga wurin wani ba. Za ku yi mulkin al’ummai masu yawa, babu wata kuwa da za tă yi mulkinku.
7 If there be among you a needy man, one of thy brethren, within any of thy gates, in thy land which the LORD thy God giveth thee, thou shalt not harden thy heart, nor shut thy hand from thy needy brother;
In akwai matalauci a cikin’yan’uwanku, a duk wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku taurara zuciya, ko ku ƙi saki hannu ga ɗan’uwanku matalauci.
8 but thou shalt surely open thy hand unto him, and shalt surely lend him sufficient for his need in that which he wanteth.
A maimakon haka ku bayar hannu sake, ku kuma ba shi bashi gwargwadon abin da yake bukata a sauƙaƙe.
9 Beware that there be not a base thought in thy heart, saying: 'The seventh year, the year of release, is at hand'; and thine eye be evil against thy needy brother, and thou give him nought; and he cry unto the LORD against thee, and it be sin in thee.
Ku yi hankali kada ku riƙe wannan mugun tunani cewa, “Shekara ta bakwai, shekarar yafewar basusuwa, ta yi kusa,” har ku nuna mugun nufi ga ɗan’uwa mabukaci, ku ƙi ba shi wani abu. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku.
10 Thou shalt surely give him, and thy heart shall not be grieved when thou givest unto him; because that for this thing the LORD thy God will bless thee in all thy work, and in all that thou puttest thy hand unto.
Ku bayar hannu sake gare shi, ku kuma yi haka ba tare da gunaguni ba; saboda wannan fa Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan aikinku, da kuma kome da kuka sa hannunku a kai.
11 For the poor shall never cease out of the land; therefore I command thee, saying: 'Thou shalt surely open thy hand unto thy poor and needy brother, in thy land.'
Kullum za ku kasance da matalauta a ƙasar. Saboda haka na umarce ku ku bayar hannu sake ga’yan’uwa da kuma matalauta, da masu bukata a ƙasarku.
12 If thy brother, a Hebrew man, or a Hebrew woman, be sold unto thee, he shall serve thee six years; and in the seventh year thou shalt let him go free from thee.
In ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa, namiji ko ta mace, ya sayar da kansa gare ka, ya kuma bauta maka shekaru shida, a shekara ta bakwai dole ka’yantar da shi.
13 And when thou lettest him go free from thee, thou shalt not let him go empty;
Sa’ad da kuka sake shi, kada ku bar shi yă tafi hannu wofi.
14 thou shalt furnish him liberally out of thy flock, and out of thy threshing-floor, and out of thy winepress; of that wherewith the LORD thy God hath blessed thee thou shalt give unto him.
Ku ba shi kyautai hannu sake daga tumakinku, daga masussukarku, da kuma daga wurin matsewar inabinku. Ku ba shi yadda Ubangiji Allahnku ya albarkace ku.
15 And thou shalt remember that thou wast a bondman in the land of Egypt, and the LORD thy God redeemed thee; therefore I command thee this thing to-day.
Ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku kuma ya fisshe ku. Shi ya sa nake ba ku wannan umarni a yau.
16 And it shall be, if he say unto thee: 'I will not go out from thee'; because he loveth thee and thy house, because he fareth well with thee;
Amma in bawanka ya ce maka, “Ba na so in bar ka,” saboda yana ƙaunarka da iyalinka, ya kuma fiye masa yă zauna da kai,
17 then thou shalt take an awl, and thrust it through his ear and into the door, and he shall be thy bondman for ever. And also unto thy bondwoman thou shalt do likewise.
sai ka ɗauki basilla ka huda kunnensa a bakin ƙofa, zai kuwa zama bawanka dukan rayuwarsa. Ka yi haka ma wa baiwarka.
18 It shall not seem hard unto thee, when thou lettest him go free from thee; for to the double of the hire of a hireling hath he served thee six years; and the LORD thy God will bless thee in all that thou doest.
Sa’ad da kuka’yantar da shi kada ku damu, gama shekara shida ya yi muku bauta wadda ta ninka ta ɗan ƙodago. Ubangiji Allahnku kuwa zai albarkace ku a kome da kuke yi.
19 All the firstling males that are born of thy herd and of thy flock thou shalt sanctify unto the LORD thy God; thou shalt do no work with the firstling of thine ox, nor shear the firstling of thy flock.
Ku keɓe wa Ubangiji Allahnku kowane ɗan fari na garkenku na shanu, da na tumaki. Kada ku sa ɗan fari na shanunku aiki, kada kuma ku aske gashin ɗan fari na tumakinku.
20 Thou shalt eat it before the LORD thy God year by year in the place which the LORD shall choose, thou and thy household.
Kowace shekara, kai da iyalinka za ku ci su a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da ya zaɓa.
21 And if there be any blemish therein, lameness, or blindness, any ill blemish whatsoever, thou shalt not sacrifice it unto the LORD thy God.
In dabbar tana da lahani, gurguntaka ko makantaka, ko kuwa tana da wani mugun lahani, kada ku miƙa ta ga Ubangiji Allahnku.
22 Thou shalt eat it within thy gates; the unclean and the clean may eat it alike, as the gazelle, and as the hart.
Sai ku ci a cikin biranenku. Mutum marar tsabta da mai tsabta zai iya ci kamar yadda ake yi da barewa ko mariri.
23 Only thou shalt not eat the blood thereof; thou shalt pour it out upon the ground as water.
Amma kada fa ku ci jinin, ku zubar da shi a ƙasa kamar ruwa.