< 1 Chronicles 18 >

1 And after this it came to pass, that David smote the Philistines, and subdued them, and took Gath and its towns out of the hand of the Philistines.
Ana nan sai Dawuda ya ci Filistiyawa ya kuma rinjaye su, ya ƙwace Gat da ƙauyukan kewayenta daga mulkin Filistiyawa.
2 And he smote Moab; and the Moabites became servants to David, and brought presents.
Dawuda ya kuma ci Mowabawa, suka zama bayinsa suka kuma biya haraji.
3 And David smote Hadarezer king of Zobah by Hamath, as he went to establish his dominion at the river Euphrates.
Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer sarkin Zoba, har can Hamat, sa’ad da ya je don yă kafa mulkinsa a wajen Kogin Yuferites.
4 And David took from him a thousand chariots, and seven thousand horsemen, and twenty thousand footmen; and David houghed all the chariot horses, but reserved of them for a hundred chariots.
Dawuda ya kame keken yaƙinsa dubu ɗaya, da mahayan kekunan yaƙi dubu bakwai da sojojin kafa guda dubu ashirin. Ya yayyanke dukan agaran dawakansa, amma ya bar dawakai da suka isa jan kekunan yaƙi ɗari.
5 And when the Arameans of Damascus came to succour Hadarezer king of Zobah, David smote of the Arameans two and twenty thousand men.
Da Arameyawan Damaskus suka zo su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya bugi dubu ashirin da biyunsu.
6 Then David put garrisons in Aram Damascus; and the Arameans became servants to David, and brought presents. And the LORD gave victory to David whithersoever he went.
Ya sa ƙungiyoyin sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus. Arameyawan kuwa suka zama bayinsa, suka kuma kawo haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi.
7 And David took the shields of gold that were on the servants of Hadarezer, and brought them to Jerusalem.
Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariyan da shugabannin sojojin Hadadezer suke riƙe, ya kawo su Urushalima.
8 And from Tibhath and from Cun, cities of Hadarezer, David took very much brass, wherewith Solomon made the brazen sea, and the pillars, and the vessels of brass.
Daga Teba da Kun, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Dawuda ya kwashe tagulla da yawa sosai, wanda Solomon ya yi amfani don yă yi Tekun tagulla, ginshiƙai da kuma kayayyakin tagulla dabam-dabam.
9 And when Tou king of Hamath heard that David had smitten all the host of Hadarezer king of Zobah,
Sa’ad da Towu sarkin Hamat ya ji cewa Dawuda ya ci mayaƙan Hadadezer sarkin Zoba gaba ɗaya,
10 he sent Hadoram his son to king David, to salute him, and to bless him — because he had fought against Hadarezer and smitten him; for Hadarezer had wars with Tou — and he had with him all manner of vessels of gold and silver and brass.
sai ya aiki ɗansa Hadoram zuwa wurin Sarki Dawuda yă gaishe shi yă kuma yi masa barka da nasara a yaƙi a kan Hadadezer, wanda yake yaƙi da Towu. Hadoram ya kawo kowane irin kayayyakin zinariya da na azurfa da na tagulla.
11 These also did king David dedicate unto the LORD, with the silver and the gold that he carried away from all the nations; from Edom, and from Moab, and from the children of Ammon, and from the Philistines, and from Amalek.
Sarki Dawuda ya miƙa waɗannan kayayyakin ga Ubangiji, kamar yadda ya yi da azurfa da kuma zinariyan da ya kwaso daga dukan waɗannan al’ummai. Edom da Mowab, Ammonawa da Filistiyawa, da kuma Amalek.
12 Moreover Abishai the son of Zeruiah smote of the Edomites in the Valley of Salt eighteen thousand.
Abishai ɗan Zeruhiya ya bugi mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri.
13 And he put garrisons in Edom; and all the Edomites became servants to David. And the LORD gave victory to David whithersoever he went.
Ya sa ƙungiyoyin sojoji a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi.
14 And David reigned over all Israel; and he executed justice and righteousness unto all his people.
Dawuda ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila, yana yin abin da yake daidai da kuma gaskiya saboda dukan mutanensa.
15 And Joab the son of Zeruiah was over the host; and Jehoshaphat the son of Ahilud was recorder.
Yowab ɗan Zeruhiya shi ne shugaban mayaƙa; Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci;
16 And Zadok the son of Ahitub, and Abimelech the son of Abiathar, were priests; and Shavsha was scribe;
Zadok ɗan Ahitub da Abimelek ɗan Abiyatar su ne firistoci; Shafsha shi ne magatakarda;
17 and Beniah the son of Jehoiada was over the Cherethites and the Pelethites; and the sons of David were chief about the king.
Benahiya ɗan Yehohiyada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa;’ya’yan Dawuda maza su ne manyan ma’aikata a gefen sarki.

< 1 Chronicles 18 >