< Ephesians 1 >

1 Pavl an Apostle of Jesvs Christ by the will of God, to the Saints, which are at Ephesus, and to ye faithfull in Christ Iesus:
Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, Zuwa ga tsarkaka da suke a Afisa, da kuma suke amintattu cikin Kiristi Yesu.
2 Grace be with you, and peace from God our Father, and from the Lord Iesus Christ.
Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.
3 Blessed be God, and the Father of our Lord Iesus Christ, which hath blessed vs with all spirituall blessing in heauenly thinges in Christ,
Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama.
4 As hee hath chosen vs in him, before the foundation of the worlde, that we should be holy, and without blame before him in loue:
Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa.
5 Who hath predestinate vs, to be adopted through Iesus Christ in him selfe, according to the good pleasure of his will,
A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri.
6 To the prayse of the glory of his grace, wherewith he hath made vs freely accepted in his beloued,
Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne.
7 By whom we haue redemption through his blood, euen the forgiuenes of sinnes, according to his rich grace:
A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah
8 Whereby he hath bene aboundant toward vs in all wisedome and vnderstanding,
wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta.
9 And hath opened vnto vs the mysterie of his will according to his good pleasure, which he had purposed in him,
Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yă cika ta wurin Kiristi.
10 That in the dispensation of the fulnesse of the times, he might gather together in one all things, both which are in heauen, and which are in earth, euen in Christ:
Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa.
11 In whom also we are chosen when we were predestinate according to ye purpose of him, which worketh all things after the counsell of his owne will,
A cikinsa ne kuma aka zaɓe mu mu sami gādo daga Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi.
12 That we, which first trusted in Christ, should be vnto the praise of his glorie:
Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi, mu yi zaman yabon ɗaukakar Allah.
13 In whom also ye haue trusted, after that ye heard the worde of trueth, euen the Gospel of your saluation, wherein also after that ye beleeued, ye were sealed with the holy Spirite of promise,
An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki.
14 Which is the earnest of our inheritance, for the redemption of that libertie purchased vnto the prayse of his glory.
Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne.
15 Therefore also after that I heard of the faith, which ye haue in the Lord Iesus, and loue toward all the Saints,
Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan mutanen Allah,
16 I cease not to giue thankes for you, making mention of you in my prayers,
ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina.
17 That the God of our Lord Iesus Christ, that Father of glory, might giue vnto you the Spirit of wisedome, and reuelation through the acknowledging of him,
Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau.
18 That the eyes of your vnderstanding may be lightened, that ye may knowe what the hope is of his calling, and what the riches of his glorious inheritance is in the Saints,
Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa.
19 And what is the exceeding greatnesse of his power toward vs, which beleeue, according to the working of his mightie power,
Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan
20 Which he wrought in Christ, when he raised him from the dead, and set him at his right hand in the heauenly places,
da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya.
21 Farre aboue al principalitie, and power, and might, and domination, and euery Name, that is named, not in this world only, but also in that that is to come, (aiōn g165)
Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa. (aiōn g165)
22 And hath made all things subiect vnder his feete, and hath giuen him ouer all things to be the head to the Church,
Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi iko a kan kome don amfanin ikkilisiya.
23 Which is his body, euen the fulnesse of him that filleth all in all things.
Kuma ikkilisiya ce jikinsa; ta kuma cika da Kiristi, wanda ya cika kome ta kowace hanya.

< Ephesians 1 >