< Matthew 24 >
1 As Jesus was leaving the Temple his disciples came to him, pointing proudly to the Temple buildings.
Yesu ya fita daga cikin haikalin ya kama hanyar sa. Almajiran sa suka zo suna nuna masa ginin haikali.
2 But Jesus replied, “You see all these buildings? I tell you the truth: there won't be one stone left upon another. Every last one will come crashing down!”
Amma ya amsa masu yace, “kun ga dukkan wadannan abubuwan? Ina gaya maku gaskiya, ba ko dutse daya da za'a bari akan dan'uwansa wanda ba za'a rushe shi ba.”
3 As Jesus sat on the Mount of Olives, the disciples came to him in private, and asked, “Please tell us when this will happen. What will be the sign of your coming and the end of the world?” (aiōn )
Yayin da ya zauna a kan dutsen zaitun, almajiran sa suka zo wurin sa a boye suka ce, “me zai zama alamar zuwanka da kuma na karshen duniya?” (aiōn )
4 “Make sure no one misleads you,” Jesus replied.
Yesu ya amsa yace dasu, “Ku kula kada wani yasa ku kauce.”
5 “Many will come claiming to be me, saying, ‘I'm the Messiah,’ and they will deceive many people.
Gama da yawa za su zo da sunana. Za su ce, “ni ne almasihu,” kuma za su sa da yawa su kauce.
6 You'll hear about wars, and rumors about wars, but don't be anxious. These things have to happen, but this isn't the end.
Za ku ji labarin yake-yake da kuma shelar yake-yake. Ku kula kar ku tsorata, domin dole abubuwan nan su faru; amma karshen dai tukunna.
7 Nations will attack other nations, and kingdoms will fight against other kingdoms. There will be famines and earthquakes in various places,
Gama al'umma zata tayarwa al'umma, kuma mulki zai tayarwa mulki. Za'a yi yunwa da girgizar kasa a wurare dabam dabam.
8 but all these things are just the beginnings of birth pains.
Amma dukkan wadannan farkon ciwon haihuwa ne kawai.
9 Then they will arrest you, they will persecute you, and they will kill you. All people will hate you because of me.
Bayan haka za'a bada ku ga tsanani a kuma kashe ku. Dukkan al'ummai za su tsane ku saboda sunana.
10 At that time many believers will give up believing. They will betray one another and hate one another.
Daga nan da yawa za su yi tuntube, kuma su ci amanar juna, su kuma tsani juna.
11 Many false prophets will come and deceive many people.
Annabawan karya da yawa za su taso kuma susa da yawa su kauce.
12 The increasing evil will lead the love of many to grow cold,
Domin mugunta zata ribambanya, kaunar masu yawa zata yi sanyi.
13 but those who hold out to the end will be saved.
Amma duk wanda ya jure har karshe, zai sami ceto.
14 The good news of the kingdom will be proclaimed around the whole world so everyone will be able to hear it, and then the end will come.
Za'a yi wa'azin wannan bisharar mulkin a dukkan duniya don ya zama shaida akan dukkan al'ummai. Daganan karshen zai zo.
15 So when you see the ‘idolatry that defiles’ standing in the holy place that the prophet Daniel spoke about (those who read this please consider carefully),
Don haka, idan kun ga abin kyama mai lalatarwa, wanda Annabi Daniyel ya yi maganar sa, Ya tsaya a wuri mai tsarki (bari mai karatu ya fahimta),
16 then the people living in Judea should run away to the mountains.
bari wadanda ke yahudiya su gudu zuwa kan duwatsu,
17 Anyone who is on the housetop must not go down and fetch what's in the house.
Bari wanda yake kan bene kada ya sauko don daukar wani abu a cikin gidansa,
18 Anyone who is out in the fields must not go back to get a coat.
kuma wanda yake gona kar ya dawo gida domin daukar babbar rigarsa.
19 How awful it will be for those who are pregnant, and those who are nursing babies at that time!
Amma kaito ga wadanda suke dauke da yaro, ko masu shayarwa a wannan kwanakin!
20 Pray that you don't have to run away in winter, or on the Sabbath day.
Ku yi addu'a kada gudun ku ya zama lokacin hunturu, ko ranan asabaci.
21 For at that time there will be terrible persecution—more terrible than anything that has happened from the beginning of the world up till now, and won't ever happen again.
Domin za'ayi tsanani mai girma, wanda ba'a taba yin irin shi ba, tun farkon duniya har ya zuwa yau, a'a ba za ayi irin shi ba kuma.
22 Unless those days are cut short, nobody will be saved, but for the sake of the chosen those days will be cut short.
In ba don an rage kwanakin ba, da ba mahalukin da zai tsira. Amma albarkacin zababbun, za a rage kwanakin.
23 So if anyone tells you, ‘Look, here's the Messiah,’ or, ‘There he is,’ don't believe it.
Sa'annan idan wani yace maku, duba, “ga Almasihu a nan!” ko, “ga Almasihu a can!” kar ku gaskata.
24 For false messiahs will appear, and false prophets too, and they will perform incredible signs and miracles in order to deceive the chosen, if that were possible.
Gama annabawan karya da almasihan karya za su zo suna nuna alamu da al'ajibai, don su yaudari masu yawa zuwa ga bata, in ya yiwuma har da zababbun.
25 Notice that I've told you this before it even happens.
Kun gani, na gaya maku kafin lokacin ya zo.
26 So if they tell you, ‘Look, he's out in the desert,’ don't go looking there; or if they say, ‘Look, he's secretly here,’ don't believe it.
Saboda haka, idan suka ce maku, “ga shi a jeji,” kar ku je jejin. Ko, “ga shi a can cikin kuryar daki,” kar ku gaskata.
27 For the coming of the Son of man will be like the lightning that flashes brightly from east to west.
Yadda walkiya ke haskakawa daga gabas zuwa yamma, haka nan zuwan Dan mutum zai zama.
28 ‘Vultures gather where the carcass is.’
Duk inda mushe yake, nan ungulai suke taruwa.
29 But right after those days of persecution the sun will be darkened, the moon will not shine, the stars will fall from heaven, and the powers of heaven will be shaken.
Amma nan da nan bayan kwanakin tsananin nan, rana za ta duhunta, wata kuma ba zai ba da haskensa ba, taurari kuma za su fado daga sama, ikokin sammai za su girgiza.
30 Then the sign of the Son of man will appear in heaven, and all the peoples of the earth will mourn. They will see the Son of man coming on the clouds of heaven with power and in brilliant glory.
Sa'annan alamar Dan Mutum za ta bayyana a sararin sama, kuma dukkan kabilun duniya za su yi bakin ciki. Za su ga Dan Mutun na zuwa a gajimarai da iko da daukaka mai girma.
31 With a blast from a trumpet he will send his angels to gather his chosen ones from every place, from one end of heaven and earth to the other.
Zai aiki mala'ikunsa, da karar kaho mai karfi, kuma za su tattara dukkan zababbu daga dukkan kusurwoyi hudu, daga karshen sararin sama har zuwa wani karshen.
32 Learn an illustration from the fig tree. When its shoots become tender and leaves begin to sprout, you know that summer is coming.
Kuyi koyi da itacen baure. Da zaran reshen sa ya yi toho ya fara bada ganye, za ku sani bazara ta kusa.
33 In the same way when you see all these things happening, you know that his coming is near, in fact it's right at the door!
Haka kuma, idan kun ga dukkan wadannan abubuwa, ya kamata ku sani, Ya yi kusa, ya na bakin kofa.
34 I tell you the truth: this generation won't pass away until all these things have happened.
Ina gaya maku gaskiya, wannan zamanin ba zai wuce ba, sai dukkan wadannan abubuwan sun faru.
35 Heaven and earth may pass away, but my words won't pass away.
Sama da kasa za su shude, amma kalmomina ba za su shude ba.
36 But no one knows the day or hour when this will take place, not the angels in heaven, nor the Son. Only the Father knows.
Amma game da ranan nan ko sa'a ba wanda ya sani, ko mala'ikun sama, ko Dan, sai Uban kadai.
37 When the Son of man comes it will be like it was during the time of Noah.
Kamar yadda kwanakin Nuhu suke, haka zai zama game da zuwan Dan Mutum.
38 It will be as in the days before the flood, when they were eating and drinking, marrying and giving in marriage, right up until the day that Noah went into the ark.
A wadannan kwankin kafin zuwan ruwan tsufana suna ci suna sha, suna aure suna aurarwa har ranar da Nuhu ya shiga jirgin,
39 They didn't realize what was going to happen until the flood came and swept them all away. That's how the coming of the Son of man will be.
ba su san kome ba har ruwan ya zo ya cinye su haka ma zuwan Dan Mutun zai zama.
40 Two men will be working in the fields. One will be taken, the other left.
Sa'annan mutane biyu zasu kasance a gona za a dauke daya, a bar daya a baya.
41 Two women will be grinding grain with a mill. One will be taken, the other left.
Mata biyu na nika a manika za a dauke daya, za a bar dayar.
42 So stay alert, because you don't know what day your Lord is coming.
Don haka sai ku yi zaman tsaro, domin baku san ranar da Ubangijinku zai zo ba.
43 But consider this: if the house-owner knew what time a thief was coming, he would keep watch. He would not allow his house to be broken into and robbed.
Amma ku san wannan, idan maigida ya san lokacin da barawo zai zo, zai zauna a shirye ba zai bar gidan sa har a balle a shiga ba.
44 You also need to be ready, because the Son of man is coming at a time when you're not expecting him.
Don haka sai ku shirya, domin Dan Mutum zai zo a sa'ar da ba ku yi zato ba.
45 For who is the trustworthy and thoughtful servant? It's the one his master puts in charge of his household to provide them with food at the proper time.
To wanene amintaccen bawannan mai hikima, wanda maigidan sa ya sa ya kula mar da gida, domin ya ba su abinci a kan lokaci?
46 How good it will be for that servant to be found doing that when his master returns!
Mai albarka ne bawan, da mai gidan zai same shi a kan aikin sa a lokacin da ya dawo.
47 I tell you the truth: the master will put that servant in charge over everything he has.
Ina gaya maku gaskiya mai gidan zai dora shi a kan dukkan a binda yake da shi.
48 But if he was evil, the servant would say to himself, ‘My master is taking a long time,’
Amma idan mugun bawa ya ce a zuciyarsa, “maigida na ya yi jinkiri,”
49 and would start beating the other servants, feasting and drinking with the drunks.
sai ya fara dukan sauran barorin, ya yi ta ci da sha tare da mashaya,
50 Then that servant's master will return when the man doesn't expect him, at a time he doesn't know.
uban gidan bawan zai dawo a ranar da bawan bai zata ba, a lokacin da bai sani ba.
51 He'll cut him to pieces, and treat him in the same way as the hypocrites, sending him to a place where there's crying and gnashing of teeth.
Uban gidansa zai datsa shi biyu, karshen sa zai zama daidai da na munafukai, za a sashi inda a ke kuka da cizon hakora.