< 1 Samuel 30 >

1 Three days later David and his men arrived back in Ziklag. Some Amalekites had raided the Negev and Ziklag. They had attacked Ziklag and burned it down.
A rana ta uku, Dawuda da mutanensa suka isa Ziklag, sai suka tarar Amalekawa sun riga sun kawo wa Negeb da Ziklag hari. Suka cinye Ziklag, suka ƙone ta,
2 They had captured the women and everyone else there, young and old. They hadn't killed anyone, but they took everyone with them as they left.
suka kwashe mata, yara da tsofaffi da dukan abubuwan da suke cikin garin. Ba su kashe kowa ba, amma suka kwashe su, suka tafi.
3 When David and his men arrived back in town, they found it burned to the ground, and their wives and children captured.
Da Dawuda da mutanensa suka isa Ziklag suka tarar an ƙone garin, an kuma kwashe matansu, da’ya’yansu mata, da kuma’ya’yansu maza ganima,
4 David and his men cried loudly until they couldn't cry any more.
sai Dawuda da mutanensa suka yi kuka, suka yi ta kuka har sai da ƙarfinsu ya ƙare.
5 David's two wives had also been taken as prisoners—Ahinoam from Jezreel and Abigail, Nabal's widow, from Carmel.
An kama matan Dawuda, wato, Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel matar Nabal mutumin Karmel wanda ya rasu.
6 David was in a great deal of trouble, because the men were so upset over losing their children that they began to talk of stoning him. But trusting in the Lord his God,
Dawuda kuwa ya damu ƙwarai domin mutanensa suna niyyar su jajjefe shi da duwatsu, kowannensu ransa ya ɓace saboda’ya’yansa maza da mata, amma Dawuda ya sami ƙarfafawa a cikin Ubangiji Allahnsa.
7 David went to Abiathar the priest, the son of Ahimelech, and said, “Bring me the ephod.” Abiathar brought it to him.
Sai Dawuda ya ce wa Abiyatar firist, ɗan Ahimelek, “Kawo mini efod.” Sai Abiyatar ya kawo masa.
8 David asked the Lord, “Should I chase after these raiders? Will I catch up with them?” “Yes, chase after them,” the Lord replied, “for you will definitely catch up with them and rescue the prisoners.”
Dawuda kuwa ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In bi bayan’yan harin nan? Zan ci musu?” Ubangiji ya ce, “Bi su, gama za ka ci musu, ka ƙwato abin da suka kwashe.”
9 David and six hundred of his men set off for the Besor Valley.
Dawuda da mutanensa ɗari shida suka kama hanya, da suka kai Kwarin Besor, waɗansunsu suka tsaya a can.
10 Two hundred of them remained behind there because they were too tired to cross the valley while David continued on with four hundred men.
Dawuda ya ci gaba da mutane ɗari huɗu, don mutane ɗari biyu sun gaji sosai har sun kāsa ƙetare rafin Besor.
11 They came across an Egyptian in the countryside and they took him to David. They gave him some food to eat and water to drink.
Suka sami wani mutumin Masar a fili suka kawo shi wurin Dawuda. Suka ba shi abinci ya ci, suka kuma ba shi ruwa ya sha.
12 They also gave him a piece of a fig cake and two raisins cakes. He ate them and recovered, because he hadn't had any food or water for three days and nights.
Suka ba shi saura wainan’ya’yan ɓaure da kuma wainan’ya’yan inabi, ya ci ya sami ƙarfi. Gama bai ci ba, bai sha ba, har yini uku da dare uku.
13 “Whose slave are you, and where do you come from?” David asked him. “I'm an Egyptian,” he replied, “the slave of an Amalekite. My master left me behind three days ago when I got sick.
Dawuda ya tambaye shi ya ce, “Wane ne ubangidanka, kuma daga ina ka fito?” Ya ce, “Ni mutumin Masar ne, bawan wani mutumin Amalek. Maigidana ya ƙyale ni sa’ad da na yi rashin lafiya kwanaki ukun da suka wuce.
14 We raided the Kerethites in the Negev, as well as the part that belongs to Judah, and the Negev of Caleb. We burned Ziklag too.”
Mun kai hari a Negeb ta Keretawa ta Yahuda, da Negeb ta Kaleb, muka kuma ƙone Ziklag.”
15 “Can you lead me to these raiders?” David asked. “If you swear to me by God that you won't kill me or hand me over to my master, then I'll take you to them,” the man replied.
Dawuda ya ce masa, “Za ka iya kai ni wurin maharan nan?” Ya ce, “Idan ka rantse mini da Allah, ba za ka kashe ni ba, ba kuwa za ka mai da ni wurin ubangidana ba, sai in kai ka inda maharan suke.”
16 He led David to the Amalekites, where they were spread out all over the place, eating, drinking, and dancing because of the large haul of plunder they had taken from the lands of the Philistines and of Judah.
Ya bi da Dawuda har zuwa can, sai ga su a baje ko’ina a ƙasa, suna ci, suna sha, suna annashuwa saboda yawan ganimar da suka kwashe daga ƙasar Filistiyawa da ƙasar Yahuda.
17 David attacked them from dusk until the following evening. Nobody escaped, except for four hundred men who managed to get away, riding on camels.
Dawuda ya yaƙe su tun daga fāɗuwar rana har yammar kashegari. Ba ko ɗaya da ya tsira sai samari ɗari huɗu waɗanda suka tsere a kan raƙuma.
18 David got back everything the Amalekites had taken, including his two wives.
Dawuda ya ƙwato kome da Amalekawa suka kwashe tare da matarsa biyu.
19 Everything was accounted for—all the adults and children, as well as all the plunder the Amalekites had taken. David brought everything back.
Babu abin da ya ɓace, Dawuda ya dawo da kowa, manya da ƙanana,’yan maza da’yan mata duka, da dukan abubuwan da Amalekawa suka kwashe.
20 He also recovered all the flocks and herds. His men drove them ahead of the other livestock, shouting, “This is David's plunder!”
Ya kuma ƙwato garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu. Mutanensa suka koro shanun, suka yi gaba, suka ce, “Wannan shi ne ganimar Dawuda.”
21 When David got back to the two hundred men who had been too tired to continue with him from the Besor Valley, they came to meet him and the men with him. As David approached the men to greet them,
Da Dawuda ya zo wurin mutum ɗari biyu ɗin nan waɗanda suka tafke, suka kāsa binsa, waɗanda aka bari a bakin Kwarin Besor, sai suka taryi Dawuda da mutanensa da suka tafi tare da shi. Sa’ad da Dawuda ya zo kusa da su, sai ya gaishe su.
22 all the unpleasant, good-for-nothing men of those who had gone with David said, “They weren't with us, so we won't share the plunder that we took, except to give them back their wives and children. They can take them and leave.”
Sai dukan mugaye da marasa kirki daga cikin mutanen da suka tafi tare da Dawuda suka ce, “Tun da yake ba su tafi tare da mu ba, ba za mu ba su kome daga cikin ganimar da muka ƙwato ba, sai dai kowane mutum yă ɗauki matarsa da’ya’yansa yă tafi.”
23 But David intervened, saying, “No, my brothers, you shouldn't do this with what the Lord has given us. He has protected us and handed over to us the raiders that had attacked us.
Dawuda ya ce, “A’a,’yan’uwana ba za ku yi haka da abin da Ubangiji ya ba mu ba. Ya tsare mu, ya kuma bashe sojojin da suka yi gāba da mu a hannuwanmu.
24 Who's going to listen to you when you say such things? Whatever share those who went into battle receive will be the same as those who stayed to guard the supplies.”
Wa zai goyi bayanku a kan wannan al’amari? Wanda ya tafi wurin yaƙi da wanda ya zauna wurin kaya, rabonsu zai zama daidai.”
25 David made this the rule and regulation for Israel from that day until now.
Dawuda ya sa wannan tă zama dawwammamiyar farilla ga Isra’ila tun daga wannan rana har yă zuwa yau.
26 When David got back to Ziklag, he sent some of the plunder to each of his friends among the elders of Judah, saying, “Here's a gift for you from the plunder of the Lord's enemies.”
Da Dawuda ya iso Ziklag, sai ya aika wa abokansa, dattawan Yahuda da rabo daga cikin ganimar ya ce, “Ga kyauta dominku, daga cikin ganimar maƙiyan Ubangiji.”
27 David sent it to those who lived in Bethuel, Ramoth Negev, Jattir,
Kyautar domin waɗanda suke a Betel, da Ramot ta Negeb, da Yattir,
28 Aroer, Siphmoth, Eshtemoa,
da Arower, da Sifmot, da Eshtemowa,
29 Racal, and the towns of the Jerahmeelites and Kenites,
da Rakal, da garuruwan Yerameyelawa, da garuruwan Keniyawa,
30 Hormah, Bor-ashan, Athach,
da Horma, da Bor-Ashan, da Atak,
31 Hebron—all the places David and his men had gone to.
da Hebron, da dukan wuraren da Dawuda da mutanensa suka taɓa zagawa.

< 1 Samuel 30 >