< Psalms 78 >
1 Understanding for Asaph. Attend, O my people, to my law: incline your ears to the words of my mouth.
Maskil na Asaf. Ya mutanena, ku ji koyarwata; ku saurari kalmomin bakina.
2 I will open my mouth in parables: I will utter propositions from the beginning.
Zan buɗe bakina da misalai, zan faɗi ɓoyayyun abubuwa, abubuwan dā,
3 How great things have we heard and known, and our fathers have told us.
abin da muka ji muka kuma sani, abubuwan da kakanninmu suka faɗa mana.
4 They have not been hidden from their children, in another generation. Declaring the praises of the Lord, and his powers, and his wonders which he hath done.
Ba za mu ɓoye su wa’ya’yanmu ba; za mu faɗa wa tsara mai zuwa ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji, ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.
5 And he set up a testimony in Jacob: and made a law in Israel. How great things he commanded our fathers, that they should make the same known to their children:
Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila, wadda ya umarce kakanni-kakanninmu su koya wa’ya’yansu,
6 That another generation might know them. The children that should be born and should rise up, and declare them to their children.
don tsara na biye su san su, har da’ya’yan da ba a riga an haifa ba, su kuma su faɗa wa’ya’yansu.
7 That they may put their hope in God and may not forget the works of God: and may seek his commandments.
Ta haka za su dogara ga Allah ba kuwa za su manta da ayyukansa ba amma za su kiyaye umarnansa.
8 That they may not become like their fathers, a perverse and exasperating generation. A generation that set not their heart aright: and whose spirit was not faithful to God.
Ba za su zama kamar kakanni kakanninsu ba, masu taurinkai da kuma tsara masu tayarwa, waɗanda zukatansu ba su yi biyayya ga Allah ba, waɗanda zukatansu ba su yi aminci ga Allah ba.
9 The sons of Ephraim who bend and shoot with the bow: they have turned back in the day of battle.
Mutanen Efraim, ko da yake suna da bakkuna, suka juya da baya a ranar yaƙi;
10 They kept not the covenant of God: and in his law they would not walk.
ba su kiyaye alkawarin Allah ba suka kuma ƙi su yi rayuwa ta wurin dokarsa.
11 And they forgot his benefits, and his wonders that he had shewn them.
Suka manta da abin da ya aikata, abubuwan banmamakin da ya nuna musu.
12 Wonderful things did he do in the sight of their fathers, in the land of Egypt, in the field of Tanis.
Ya yi mu’ujizai a idanun kakanninsu a ƙasar Masar, a yankin Zowan.
13 He divided the sea and brought them through: and he made the waters to stand as in a vessel.
Ya raba teku ya kuma bi da su ciki; ya sa ruwa ya tsaya daram kamar bango.
14 And he conducted them with a cloud by day: and all the night with a light of fire.
Ya bishe su da girgije da rana da kuma haske daga wuta dukan dare.
15 He struck the rock in the wilderness: and gave them to drink, as out of the great deep.
Ya tsage duwatsu a cikin hamada ya kuma ba su ruwaye a yalwace kamar tekuna;
16 He brought forth water out of the rock: and made streams run down as rivers.
ya fid da rafuffuka daga dutsen da ya tsaga ya sa ruwa ya gudu kamar koguna.
17 And they added yet more sin against him: they provoked the most High to wrath in the place without water.
Amma suka ci gaba da yin masa zunubi, suna tayarwa a cikin hamada a kan Mafi Ɗaukaka.
18 And they tempted God in their hearts, by asking meat for their desires.
Da gangan suka gwada Allah ta wurin neman abincin da suke kwaɗayi.
19 And they spoke ill of God: they said: Can God furnish a table in the wilderness?
Suka yi magana a kan Allah, suna cewa, “Allah zai iya shimfiɗa tebur a cikin hamada?
20 Because he struck the rock, and the waters gushed out, and the streams overflowed. Can he also give bread, or provide a table for his people?
Sa’ad da ya bugi dutse, ruwa ya ɓulɓulo, rafuffuka suka yi gudu a yalwace. Amma zai iya ba mu abinci? Zai iya tanada wa mutanensa nama?”
21 Therefore the Lord heard, and was angry: and a fire was kindled against Jacob, and wrath came up against Israel.
Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; wutarsa ta ɓarke a kan Yaƙub, hasalarsa kuwa ta tashi a kan Isra’ila,
22 Because they believed not in God: and trusted not in his salvation.
gama ba su gaskata ga Allah ba ko su dogara ga cetonsa.
23 And he had commanded the clouds from above, and had opened the doors of heaven.
Duk da haka ya ba da umarni ga sarari a bisa ya kuma buɗe ƙofofin sammai;
24 And had rained down manna upon them to eat, and had given them the bread of heaven.
ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci, ya ba su hatsin sama.
25 Man ate the bread of angels: he sent them provisions in abundance.
Mutane suka ci burodin mala’iku; ya aika musu dukan abincin da za su iya ci.
26 He removed the south wind from heaven: and by his power brought in the southwest wind.
Ya saki iskar gabas daga sammai ya kuma saki iskar yamma ta wurin ikonsa.
27 And he rained upon them flesh as dust: and feathered fowls like as the sand of the sea.
Ya sauko da nama a kansu kamar ƙura, tsuntsaye masu firiya kamar yashi a bakin teku.
28 And they fell in the midst of their camp, round about their pavilions.
Ya sa suka sauka a cikin sansaninsu, ko’ina kewaye da tentunansu.
29 So they did eat, and were filled exceedingly, and he gave them their desire:
Suka ci har suka sami fiye da abin da ya ishe su, gama ya ba su abin da suka yi kwaɗayi.
30 They were not defrauded of that which they craved. As yet their meat was in their mouth:
Amma kafin su juyo daga abincin da suka yi kwaɗayi, kai tun ma yana a bakunansu,
31 And the wrath of God came upon them. And he slew the fat ones amongst them, and brought down the chosen men of Israel.
fushin Allah ya ƙuna a kansu; ya karkashe waɗanda suka fi ƙiba a cikinsu, yana yankan matasan Isra’ila.
32 In all these things they sinned still: and they believed not for his wondrous works.
Duk da haka, suka ci gaba da yin zunubi; duk da abubuwan banmamakinsa, ba su gaskata ba.
33 And their days were consumed in vanity, and their years in haste.
Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza shekarunsu kuma cikin masifa.
34 When he slew them, then they sought him: and they returned, and came to him early in the morning.
A duk sa’ad da Allah ya kashe su, sai su neme shi; sukan juyo a natse gare shi.
35 And they remembered that God was their helper: and the most high God their redeemer.
Sun tuna cewa Allah ne Dutsensu, cewa Allah Mafi Ɗaukaka ne Mai fansarsu.
36 And they loved him with their mouth: and with their tongue they lied unto him:
Amma sai su yi ta yin masa zaƙin baki, suna masa ƙarya da harsunansu;
37 But their heart was not right with him: nor were they counted faithful in his covenant.
zukatansu ba sa biyayya gare shi, ba su da aminci ga alkawarinsa.
38 But he is merciful, and will forgive their sins: and will not destroy them. And many a time did he turn away his anger: and did not kindle all his wrath.
Duk da haka ya kasance mai jinƙai; ya gafarta laifofinsu bai kuwa hallaka su ba. Sau da sau ya janye fushinsa bai kuwa sa fushinsa yă ƙuna ba.
39 And he remembered that they are flesh: a wind that goeth and returneth not.
Ya tuna cewa su naman jiki ne kawai, iska mai wucewa da ba ta dawowa.
40 How often did they provoke him in the desert: and move him to wrath in the place without water?
Sau da yawa sun tayar masa a cikin hamada suka kuma ɓata masa rai a jeji!
41 And they turned back and tempted God: and grieved the holy one of Israel.
Sau da sau suka riƙa gwada Allah; suka tsokane Mai Tsarki na Isra’ila.
42 They remembered not his hand, in the day that he redeemed them from the hand of him that afflicted them:
Ba su tuna da ikonsa, a ranar da ya fanshe su daga mai danniya,
43 How he wrought his signs in Egypt, and his wonders in the field of Tanis.
ranar da ya nuna mu’ujizansa a Masar abubuwan banmamakinsa a yankin Zowan ba.
44 And he turned their rivers into blood, and their showers that they might, not drink.
Ya mai da kogunansu suka zama jini; ba su iya sha daga rafuffuka ba.
45 He sent amongst them divers sores of flies, which devoured them: and frogs which destroyed them.
Ya aika da tarin ƙudajen da suka cinye su, da kwaɗin da suka wahalshe su.
46 And he gave up their fruits to the blast, and their labours to the locust.
Ya ba da hatsinsu ga fāra, amfanin gonakinsu ga ɗango.
47 And he destroyed their vineyards with hail, and their mulberry trees with hoarfrost.
Ya lalace inabinsu da ƙanƙara itatuwan al’ul nasu kuma da jaura.
48 And he gave up their cattle to the hail, and their stock to the fire.
Ya miƙa shanunsu ga ƙanƙara, tumakinsu ga aradun tsawa.
49 And he sent upon them the wrath of his indignation: indignation and wrath and trouble, which he sent by evil angels.
Ya saki musu fushinsa mai zafi, hasalarsa, zafin rai da kuma ɓacin ransa, ƙungiyar mala’iku masu hallakarwa.
50 He made a way for a path to his anger: he spared not their souls from death, and their cattle he shut up in death.
Ya shirya hanya wa fushinsa; bai tsare ransu daga mutuwa ba amma ya miƙa su ga annoba.
51 And he killed all the firstborn in the land of Egypt: the firstfruits of all their labour in the tabernacles of Cham.
Ya bugi kowane ɗan fari na Masar, mafari ƙarfin mazantakansu a tentunan Ham.
52 And he took away his own people as sheep: and guided them in the wilderness like a flock.
Amma ya fitar da mutanensa kamar garke; ya bi da su kamar tumaki ta cikin hamada.
53 And he brought them out in hope, and they feared not: band the sea overwhelmed their enemies.
Ya bi da su lafiya ƙalau, don kada su ji tsoro; amma teku ya cinye abokan gābansu.
54 And he brought them into the mountain of his sanctuary: the mountain which his right hand had purchased. And he cast out the Gentiles before them: and by lot divided to them their land by a line of distribution.
Ta haka ya kawo su iyakar ƙasa mai tsarki, zuwa ƙasar tudun da hannunsa na dama ya kame.
55 And he made the tribes of Israel to dwell in their tabernacles.
Ya kori al’ummai a gabansu ya rarraba ƙasashensu gare su a matsayin gādo; ya zaunar da kabilan Isra’ila a gidajensu.
56 Yet they tempted, and provoked the most high God: and they kept not his testimonies.
Amma suka gwada Allah suka tayar wa Mafi Ɗaukaka; ba su kiyaye ƙa’idodinsa ba.
57 And they turned away, and kept not the covenant: even like their fathers they were turned aside as a crooked bow.
Kamar kakanninsu suka zama marasa biyayya da marasa aminci, marar tabbas kamar tanƙwararren baka.
58 They provoked him to anger on their hills: and moved him to jealousy with their graven things.
Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu; suka tayar da kishinsa da gumakansu.
59 God heard, and despised them, and he reduced Israel exceedingly as it were to nothing.
Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; ya ƙi Isra’ila gaba ɗaya.
60 And he put away the tabernacle of Silo, his tabernacle where he dwelt among men.
Ya yashe tabanakul na Shilo, tentin da ya kafa a cikin mutane.
61 And he delivered their strength into captivity: and their beauty into the hands of the enemy.
Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta, darajarsa zuwa cikin hannuwan abokin gāba.
62 And he shut up his people under the sword: and he despised his inheritance.
Ya ba da mutanensa ga takobi; ya yi fushi ƙwarai da gādonsa.
63 Fire consumed their young men: and their maidens were not lamented.
Wuta ta cinye matasansu maza,’yan matansu kuma ba su da waƙoƙin aure;
64 Their priests fell by the sword: and their widows did not mourn.
aka karkashe firistocinsu, gwaurayensu kuwa ba su iya makoki ba.
65 And the Lord was awaked as one out of sleep, and like a mighty man that hath been surfeited with wine.
Sa’an nan Ubangiji ya farka sai ka ce daga barcinsa, kamar yadda mutum kan farka daga buguwar ruwan inabi.
66 And he smote his enemies on the hinder parts: he put them to an everlasting reproach.
Ya kori abokan gābansa; ya sa suka sha madawwamiyar kunya.
67 And he rejected the tabernacle of Joseph: and chose not the tribe of Ephraim:
Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf, bai zaɓi kabilar Efraim ba;
68 But he chose the tribe of Juda, mount Sion which he loved.
amma ya zaɓi kabilar Yahuda, Dutsen Sihiyona, wanda ya ƙaunaci.
69 And he built his sanctuary as of unicorns, in the land which he founded for ever.
Ya gina wurinsa mai tsarki kamar bisa, kamar duniyar da ya kafa har abada.
70 And he chose his servant David, and took him from the hocks of sheep: he brought him from following the ewes great with young,
Ya zaɓi Dawuda bawansa ya kuma ɗauke shi daga ɗakin tumaki;
71 To feed Jacob his servant, and Israel his inheritance.
daga kiwon tumaki ya kawo shi don yă kuma zama makiyayin mutanensa Yaƙub, na Isra’ila gādonsa.
72 And he fed them in the innocence of his heart: and conducted them by the skillfulness of his hands.
Dawuda kuwa ya zama makiyayinsu da mutuncin zuciya; da hannuwa masu gwaninta ya bi da su.