< Genesis 34 >
1 And Dina the daughter of Lia went out to see the women of that country.
To, Dina,’yar da Liyatu ta haifa wa Yaƙub, ta je ta ziyarci matan ƙasar.
2 And when Sichem the son of Hemor the Hevite, the prince of that land, saw her, he was in love with her: and took her away, and lay with her, ravishing the virgin.
Sa’ad da Shekem ɗan Hamor Bahiwiye mai mulkin wurin ya gan ta, sai ya kama ta, ya kwana da ita, ya ɓata ta.
3 And his soul was fast knit unto her, and whereas she was sad, he comforted her with sweet words.
Zuciyarsa kuwa ta damu da son Dina’yar Yaƙub, ya kuwa ƙaunaci yarinyar, ya yi mata magana a hankali.
4 And going to Hemor his father, he said: Get me this damsel to wife.
Sai Shekem ya ce wa mahaifinsa Hamor, “Ka auro mini wannan yarinya ta zama matata.”
5 But when Jacob had heard this, his sons being absent, and employed in feeding the cattle, he held his peace till they came back.
Sa’ad da Yaƙub ya ji cewa an ɓata’yarsa Dina, sai ya yi shiru game da batun sai’ya’yansa maza sun dawo gida, gama’ya’yansa suna a jeji tare da dabbobinsa suna kiwo.
6 And when Hemor the father of Sichem was come out to speak to Jacob,
Sai Hamor mahaifin Shekem ya je don yă yi magana da Yaƙub.
7 Behold his sons came from the field: and hearing what had passed, they were exceeding angry, because he had done a foul thing in Israel, and committed an unlawful act, in ravishing Jacob’s daughter,
Da’ya’yan Yaƙub maza suka dawo daga jeji sai suka ji labarin. Abin kuwa ya zafe su ƙwarai, don Shekem ya jawo abin kunya wa jama’ar Isra’ila ta wurin kwana da’yar Yaƙub, don bai kamata wannan abu yă faru ba.
8 And Hemor spoke to them: The soul of my son Sichem has a longing for your daughter: give her him to wife:
Amma Hamor ya ce musu, “Ɗana Shekem ya sa zuciyarsa a kan’yarku. Ina roƙonku ku ba shi ita yă aura.
9 And let us contract marriages one with another: give us your daughters and take you our daughters,
Ku yi auratayya da mu; ku aurar mana da’ya’yanku mata, ku kuma ku auro’ya’yanmu mata wa kanku.
10 And dwell with us: the land is at your command, till, trade, and possess it.
Za ku iya zauna a cikinmu, ƙasar tana nan a buɗe dominku. Ku yi zama a cikinta, ku yi sana’a, ku kuma sami dukiya.”
11 Sichem also said to her father and to her brethren: Let me find favour in your sight: and whatsoever you shall appoint I will give.
Sai Shekem ya ce wa mahaifin Dina da kuma’yan’uwanta. “Bari in sami tagomashi a idanunku, zan kuwa ba ku duk abin da kuka tambaya.
12 Raise the dowry, and ask gifts, and I will gladly give what you shall demand: only give me this damsel to wife.
Ku faɗa mini nawa ne dukiyar aure da kuma sadakin da zan kawo bisa ga yadda kuke so, zan kuwa biya duk abin da kuka ce. Ku dai bar ni in aure yarinyar ta zama matata.”
13 The sons of Jacob answered Sichem and his father deceitfully, being enraged at the deflowering of their sister:
Domin an ɓata’yar’uwansu Dina, sai’ya’yan Yaƙub maza suka amsa a ha’ince yayinda suke wa Shekem da mahaifinsa Hamor magana.
14 We cannot do what you demand, nor give our sister to one that is uncircumcised, which with us is unlawful and abominable.
Suka ce musu, “Ba za mu iya yin wannan abu ba, ba za mu iya ba da’yar’uwarmu ga mutumin da ba shi da kaciya ba. Wannan zai zama abin kunya ne a gare mu.
15 But in this we may be allied with you, if you will be like us, and all the male sex among you be circumcised:
Za mu yarda da wannan kaɗai ta wannan sharaɗi, cewa za ku zama kamar mu ta wurin yin wa dukan’ya’yanku maza kaciya.
16 Then will we mutually give and take your daughters, and ours: and we will dwell with you, and will be one people:
Sa’an nan za mu ba da’ya’yanmu mata aure gare ku, mu kuma mu aure’ya’yanku mata wa kanmu. Za mu zauna a cikinku mu kuma zama mutane ɗaya da ku.
17 But if you will not be circumcised, we will take our daughter and depart:
Amma in ba za ku yarda a yi muku kaciya ba, za mu ɗauki’yar’uwanmu mu tafi.”
18 Their offer pleased Hemor, and Sichem his son:
Sharuɗansu sun gamshi Hamor da ɗansa, Shekem.
19 And the young man made no delay, but forthwith fulfilled what was required, for he loved the damsel exceedingly, and he was the greatest man in all his father’s house.
Saurayin wanda aka fi girmamawa a cikin dukan gidan mahaifinsa, bai ɓata lokaci a yin abin da suka ce ba, domin ya ji daɗin’yar Yaƙub.
20 And going into the gate of the city they spoke to the people:
Saboda haka Hamor da ɗansa Shekem suka tafi ƙofar birninsu don su yi magana da mutanen garinsu.
21 These men are peaceable and willing to dwell with us: let them trade in the land, and till it, which being large and wide wanteth men to till it: we shall take their daughters for wives, and we will give them ours.
Suka ce, “Waɗannan mutane ba su da damuwa, bari su zauna a cikin ƙasarmu, su kuma yi sana’a a ciki; ƙasar tana da isashen fili dominsu. Za mu iya auro’ya’yansu mata, su kuma su auri namu.
22 One thing there is for which so great a good is deferred: We must circumcise every male among us, following the manner of the nation.
Amma mutanen za su yarda su zauna tare da mu kamar mutane ɗaya kawai bisa wannan sharaɗi, cewa a yi wa mazanmu kaciya, kamar yadda su kansu suke.
23 And their substance, and cattle, and all that they possess, shall be ours: only in this let us condescend, and by dwelling together, we shall make one people.
Ashe, shanunsu, dukiyarsu da dukan sauran dabbobinsu, ba za su zama namu ba? Saboda haka mu yarda, za su kuwa zauna a cikinmu.”
24 And they all agreed, and circumcised all the males.
Dukan mazan da suka fito ƙofar birnin suka yarda da Hamor da kuma ɗansa Shekem, aka kuwa yi wa kowane namiji a birnin kaciya.
25 And behold the third day, when the pain of the wound was greatest, two of the sons of Jacob, Simeon and Levi, the brothers of Dina, taking their swords, entered boldly into the city, and slew all the men:
Bayan kwana uku, yayinda dukansu suna cikin zafi mikin kaciya, sai biyu daga cikin’ya’yan Yaƙub maza, Simeyon da Lawi,’yan’uwan Dina, suka ɗauki takubansu suka fāɗa wa birnin ba labari, suka kashe kowane namiji.
26 And they killed also Hemor and Sichem, and took away their sister Dina, out of Sichem’s house.
Suka kashe Hamor da ɗansa Shekem da takobi, suka ɗauko Dina daga gidan Shekem suka tafi.
27 And when they were gone out, the other sons of Jacob came upon the slain; and plundered the city in revenge of the rape.
Sa’an nan’ya’yan Yaƙub maza suka bi kan gawawwakin, suka washe arzikin birni saboda an ɓata’yar’uwarsu.
28 And they took their sheep and their herds and their asses, wasting all they had in their houses and in the fields.
Suka kwashe garkunansu na shanu da jakuna, da kuma kome na mutanen a birnin da kuma cikin gonaki.
29 And their children and wives they took captive,
Suka kwashe dukan dukiyarsu da dukan matansu da’ya’yansu, suka kwashe kome da yake cikin gidaje.
30 And when they had boldly perpetrated these things, Jacob said to Simeon and Levi: You have troubled me, and made me hateful to the Chanaanites and Pherezites, the inhabitants of this land: we are few: they will gather themselves together and kill me; and both I, and my house, shall be destroyed.
Sai Yaƙub ya ce wa Simeyon da Lawi, “Kun jawo mini wahala ta wurin sa in zama abin ƙi ga Kan’aniyawa da Ferizziyawa, mazaunan wannan ƙasa. Mu kima ne, in kuwa suka haɗa kai gāba da ni, suka fāɗa mini, za su hallaka ni da gidana.”
31 They answered: Should they abuse our sister as a strumpet?
Amma’ya’yansa suka amsa, “To, ya dace ke nan da ya yi da’yar’uwarmu kamar karuwa?”