< Revelation 4 >
1 After these things I saw, and behold, a door opened in heaven, and the first voice which I heard as of a trumpet speaking with me, saying, Come up here, and I will shew thee the things which must take place after these things.
Bayan wannan sai na duba, a can kuma a gabana ga ƙofa a buɗe a sama. Sai muryar da na ji da fari da take magana da ni mai kama da busar ƙaho ta ce, “Hauro nan, zan kuma nuna maka abin da lalle zai faru bayan wannan.”
2 Immediately I became in [the] Spirit; and behold, a throne stood in the heaven, and upon the throne one sitting,
Nan da nan sai ga ni cikin Ruhu, a can a gabana kuwa ga kursiyi a cikin sama da wani zaune a kansa.
3 and he [that was] sitting like in appearance to a stone [of] jasper and a sardius, and a rainbow round the throne like in appearance to an emerald.
Wannan mai zama a can kuwa yana da kamannin dutsen yasfa da karneliya. Bakan gizo, mai kama da zumurrudu, ya kewaye kursiyin.
4 And round the throne twenty-four thrones, and on the thrones twenty-four elders sitting, clothed with white garments; and on their heads golden crowns.
Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu.
5 And out of the throne go forth lightnings, and voices, and thunders; and seven lamps of fire, burning before the throne, which are the seven Spirits of God;
Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah.
6 and before the throne, as a glass sea, like crystal. And in the midst of the throne, and around the throne, four living creatures, full of eyes, before and behind;
Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi. A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya.
7 and the first living creature like a lion, and the second living creature like a calf, and the third living creature having the face as of a man, and the fourth living creature like a flying eagle.
Halitta ta fari tana kama da zaki, ta biyun kuwa tana kama da bijimi, ta ukun kuma tana da fuska kamar ta mutum, ta huɗun kuma tana kama da gaggafa mai tashi sama.
8 And the four living creatures, each one of them having respectively six wings; round and within they are full of eyes; and they cease not day and night saying, Holy, holy, holy, Lord God Almighty, who was, and who is, and who is to come.
Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa,
9 And when the living creatures shall give glory and honour and thanksgiving to him that sits upon the throne, who lives to the ages of ages, (aiōn )
Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, (aiōn )
10 the twenty-four elders shall fall before him that sits upon the throne, and do homage to him that lives to the ages of ages; and shall cast their crowns before the throne, saying, (aiōn )
sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa, (aiōn )
11 Thou art worthy, O our Lord and [our] God, to receive glory and honour and power; for thou hast created all things, and for thy will they were, and they have been created.
“Ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka cancanci ɗaukaka da girma da iko, domin ka halicci dukan abubuwa, kuma ta wurin nufinka aka halicce su suka kuma kasance.”