< Matthew 21 >
1 And when they drew near to Jerusalem and came to Bethphage, at the mount of Olives, then Jesus sent two disciples,
Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu,
2 saying to them, Go into the village over against you, and immediately ye will find an ass tied, and a colt with it; loose [them] and lead [them] to me.
yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a daure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini.
3 And if any one say anything to you, ye shall say, The Lord has need of them, and straightway he will send them.
In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa mai da su nan da nan.”
4 But all this came to pass, that that might be fulfilled which was spoken through the prophet, saying,
Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa,
5 Say to the daughter of Zion, Behold thy King cometh to thee, meek, and mounted upon an ass, and upon a colt the foal of an ass.
“Ku ce wa Diyar Sihiyona, ‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki, mai tawali’u yana a kan jaki, a kan aholaki, ɗan jaki.’”
6 But the disciples, having gone and done as Jesus had ordered them,
Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su.
7 brought the ass and the colt and put their garments upon them, and he sat on them.
Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu.
8 But a very great crowd strewed their own garments on the way, and others kept cutting down branches from the trees and strewing them on the way.
Wani babban taron mutane suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, yayinda waɗansu suka sassari rassan itatuwa suka shisshimfiɗa a kan hanya.
9 And the crowds who went before him and who followed cried, saying, Hosanna to the Son of David; blessed [be] he who comes in the name of [the] Lord; hosanna in the highest.
Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Hosanna a cikin sama!”
10 And as he entered into Jerusalem, the whole city was moved, saying, Who is this?
Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?”
11 And the crowds said, This is Jesus the prophet who is from Nazareth of Galilee.
Taron mutane suka amsa, “Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili.”
12 And Jesus entered into the temple [of God], and cast out all that sold and bought in the temple, and overthrew the tables of the money-changers and the seats of those that sold the doves.
Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai.
13 And he says to them, It is written, My house shall be called a house of prayer, but ye have made it a den of robbers.
Ya ce musu, “A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’amma kuna mai da shi ‘kogon’yan fashi.’”
14 And blind and lame came to him in the temple, and he healed them.
Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su.
15 And when the chief priests and the scribes saw the wonders which he wrought, and the children crying in the temple and saying, Hosanna to the Son of David, they were indignant,
Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su.
16 and said to him, Hearest thou what these say? And Jesus says to them, Yea; have ye never read, Out of the mouth of babes and sucklings thou hast perfected praise?
Suka tambaye shi suka ce, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu ya amsa ya ce, “I, ba ku taɓa karanta ba cewa, “‘Daga leɓunan yara da jarirai kai, Ubangiji, ka shirya wa kanka yabo’?”
17 And leaving them he went forth out of the city to Bethany, and there he passed the night.
Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana.
18 But early in the morning, as he came back into the city, he hungered.
Kashegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa.
19 And seeing one fig-tree in the way, he came to it and found on it nothing but leaves only. And he says to it, Let there be never more fruit of thee for ever. And the fig-tree was immediately dried up. (aiōn )
Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, “Kada ka ƙara yin’ya’ya!” Nan da nan itacen ya yanƙwane. (aiōn )
20 And when the disciples saw [it], they wondered, saying, How immediately is the fig-tree dried up!
Sa’ad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?”
21 And Jesus answering said to them, Verily I say unto you, If ye have faith, and do not doubt, not only shall ye do what [is done] to the fig-tree, but even if ye should say to this mountain, Be thou taken away and be thou cast into the sea, it shall come to pass.
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru.
22 And all things whatsoever ye shall ask in prayer, believing, ye shall receive.
In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a.”
23 And when he came into the temple, the chief priests and the elders of the people came to him [as he was] teaching, saying, By what authority doest thou these things? and who gave thee this authority?
Sai Yesu ya shiga filin haikali, yayinda yake koyarwa, sai manyan firistoci da dattawan mutane suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Kuma wa ya ba ka wannan iko?”
24 And Jesus answering said to them, I also will ask you one thing, which if ye tell me, I also will tell you by what authority I do these things:
Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku tambaya guda. In kuka ba ni amsa, ni ma zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa.
25 The baptism of John, whence was it? of heaven or of men? And they reasoned among themselves, saying, If we should say, Of heaven, he will say to us, Why then have ye not believed him?
Baftismar Yohanna, daga ina ta fito? Daga sama ce, ko daga mutane?” Sai suka tattauna a junansu suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama,’ zai ce, ‘To, me ya sa ba mu gaskata shi ba?’
26 but if we should say, Of men, we fear the crowd, for all hold John for a prophet.
In kuma muka ce, ‘Daga mutane,’ muna tsoron mutane, gama duk sun ɗauka Yohanna annabi ne.”
27 And answering Jesus they said, We do not know. He also said to them, Neither do I tell you by what authority I do these things.
Saboda haka suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Sai ya ce, “Ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”
28 But what think ye? A man had two children, and coming to the first he said, Child, go to-day, work in [my] vineyard.
“Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da’ya’ya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’
29 And he answering said, I will not; but afterwards repenting himself he went.
“Ya amsa ya ce, ‘Ba zan tafi ba,’ amma daga baya ya sāke tunani, ya tafi.
30 And coming to the second he said likewise; and he answering said, I [go], sir, and went not.
“Sai mahaifin ya tafi waje na biyun ya faɗa masa iri magana guda. Sai ya amsa ya ce, ‘Zan tafi, ranka yă daɗe,’ amma bai tafi ba.
31 Which of the two did the will of the father? They say [to him], The first. Jesus says to them, Verily I say unto you that the tax-gatherers and the harlots go into the kingdom of God before you.
“Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?” Suka amsa, “Na farin.” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah.
32 For John came to you in the way of righteousness, and ye believed him not; but the tax-gatherers and the harlots believed him; but ye when ye saw [it] repented not yourselves afterwards to believe him.
Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yă nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.”
33 Hear another parable: There was a householder who planted a vineyard, and made a fence round it, and dug a winepress in it, and built a tower, and let it out to husbandmen, and left the country.
“Ku saurari wani misali. An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Sa’an nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya.
34 But when the time of fruit drew near, he sent his bondmen to the husbandmen to receive his fruits.
Da lokacin girbi ya yi kusa, sai ya aiki bayinsa wajen’yan hayan, su karɓo masa’ya’yan inabi.
35 And the husbandmen took his bondmen, and beat one, killed another, and stoned another.
“Amma’yan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun.
36 Again he sent other bondmen more than the first, and they did to them in like manner.
Sai ya sāke aiken waɗansu bayi wurinsu, fiye da na dā yawa, amma’yan hayan suka yi musu kamar yadda suka yi wa na farin.
37 And at last he sent to them his son, saying, They will have respect for my son.
A ƙarshe, sai ya aiki ɗansa a wurinsu. Ya ce, ‘Za su girmama ɗana.’
38 But the husbandmen, seeing the son, said among themselves, This is the heir; come, let us kill him and possess his inheritance.
“Amma da’yan hayan suka hangi ɗan, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo, mu kashe shi, mu ci gādonsa.’
39 And they took him, and cast him forth out of the vineyard, and killed him.
Saboda haka suka kama shi, suka jefar da shi bayan katangar gonar inabin, suka kashe shi.
40 When therefore the lord of the vineyard comes, what shall he do to those husbandmen?
“To, idan mai gonar inabin ya zo, me zai yi da’yan hayan nan?”
41 They say to him, He will miserably destroy those evil [men], and let out the vineyard to other husbandmen, who shall render him the fruits in their seasons.
Suka amsa suka ce, “Zai yi wa banzan mutanen nan mugun kisa, yă ba da hayar gonar inabin ga waɗansu’yan haya, waɗanda za su ba shi rabonsa na amfanin gona a lokacin girbi.”
42 Jesus says to them, Have ye never read in the scriptures, The stone which they that builded rejected, this has become the corner-stone: this is of [the] Lord, and it is wonderful in our eyes?
Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi cewa, “‘Dutsen da magina suka ƙi shi ne ya zama dutsen kusurwar gini. Ubangiji ne ya aikata wannan, kuma abin mamaki ne a idanunmu’?
43 Therefore I say to you, that the kingdom of God shall be taken from you and shall be given to a nation producing the fruits of it.
“Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani.
44 And he that falls on this stone shall be broken, but on whomsoever it shall fall, it shall grind him to powder.
Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Amma duk wanda dutsen nan ya fāɗi a kansa, za a murƙushe shi.”
45 And the chief priests and the Pharisees, having heard his parables, knew that he spoke about them.
Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan Yesu, sai suka gane cewa da su yake.
46 And seeking to lay hold of him, they were afraid of the crowds, because they held him for a prophet.
Suka nemi hanyar kama shi, amma suka ji tsoron taron, don mutane sun ɗauka shi annabi ne.