< Isaiah 49 >

1 Listen, O isles, unto me; and hearken, ye peoples from afar. Jehovah hath called me from the womb; from the bowels of my mother hath he made mention of my name.
Ku kasa kunne gare ni, ku tsibirai; ku ji wannan, ku al’ummai masu nesa. Kafin a haife Ni Ubangiji ya kira ni; tun daga haihuwata ya ambaci sunana.
2 And he hath made my mouth like a sharp sword, he hath concealed me under the shadow of his hand, and he hath made me a polished shaft: in his quiver hath he hidden me.
Ya yi bakina kamar takobi mai kaifi, cikin inuwar hannunsa ya ɓoye ni; ya sa na zama kamar kibiya mai tsini ya kuma ɓoye ni cikin kwarinsa.
3 And he said unto me, Thou art my servant, Israel, in whom I will glorify myself.
Ya ce mini, “Kai bawana ne, Isra’ila, a cikinka zan bayyana darajata.”
4 — And I said, I have laboured in vain, I have spent my strength for nought and in vain; nevertheless my judgment is with Jehovah, and my work with my God.
Amma na ce, “Na yi aiki a banza; na kashe duk ƙarfina a banza da wofi. Duk da haka abin da yake nawa yana a hannun Ubangiji, ladana kuma tana a wurin Allahna.”
5 And now, saith Jehovah, that formed me from the womb to be his servant, that I should bring Jacob again to him; (though Israel be not gathered, yet shall I be glorified in the eyes of Jehovah, and my God shall be my strength; )
Yanzu fa Ubangiji ya ce ya siffanta ni a cikin mahaifa don in zama bawansa don in dawo da Yaƙub gare shi in kuma tattara Isra’ila gare shi, gama an girmama ni a gaban Ubangiji Allahna kuma ne ƙarfina
6 — and he saith, It is a small thing that thou shouldest be my servant to raise up the tribes of Jacob, and to restore the preserved of Israel; I have even given thee for a light of the nations, that thou mayest be my salvation unto the end of the earth.
ya ce, “Ɗan ƙaramin abu ne ka zama bawana don ka maido da kabilar Yaƙub ka kuma dawo da waɗannan na Isra’ilawan da na kiyaye. Zan kuma mai da kai haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.”
7 Thus saith Jehovah, the Redeemer of Israel, his Holy One, to him whom man despiseth, to him whom the nation abhorreth, to the servant of rulers: Kings shall see and arise, princes, and they shall worship, because of Jehovah who is faithful, the Holy One of Israel, who hath chosen thee.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki, ga bawan masu mulki. “Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye, sarakuna za su gani su kuma rusuna, saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”
8 Thus saith Jehovah: In a time of acceptance have I answered thee, and in the day of salvation have I helped thee; and I will preserve thee, and give thee for a covenant of the people, to establish the land, to cause to inherit the desolate heritages;
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “A lokacin tagomashina zan amsa muku, kuma a ranar ceto zan taimake ku; zan kiyaye ku zan kuma sa ku zama alkawari ga mutane, don ku maido da ƙasa ku kuma sāke raba gādon kufai,
9 saying to the prisoners, Go forth; to them that are in darkness, Shew yourselves. They shall feed in the ways, and their pasture shall be on all bare hills.
don ku ce wa waɗanda suke cikin kurkuku, ‘Ku fito,’ ga waɗanda suke cikin duhu kuma, ‘Ku’yantu!’ “Za su yi kiwo kusa da hanyoyi su kuma sami wurin kiwo a kowane tudu.
10 They shall not hunger nor thirst, neither shall the heat nor sun smite them; for he that hath mercy on them will lead them, and by the springs of water will he guide them.
Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba, ba kuwa zafin hamada ko rana ta buge su ba. Shi da ya yi musu jinƙai zai jagorance su ya kuma bishe su kusa da maɓulɓulan ruwa.
11 And I will make all my mountains a way, and my highways shall be raised up.
Zan mayar da dukan duwatsu su zama hanyoyi, a kuma gyara manyan hanyoyina.
12 Behold, these shall come from afar; and behold, these from the north and from the west; and these from the land of Sinim.
Duba, za su zo daga nesa waɗansu daga arewa, waɗansu daga yamma, waɗansu daga yankin Aswan.”
13 Shout, ye heavens; and be joyful, thou earth; and break forth into singing, ye mountains: for Jehovah hath comforted his people, and will have mercy upon his afflicted ones.
Ku yi sowa don farin ciki, ya ku sammai; ki yi farin ciki, ya ke duniya; ku ɓarke da waƙa, ya ku duwatsu! Gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa zai kuma ji tausayin mutanensa da suke shan wahala.
14 But Zion said, Jehovah hath forsaken me, and the Lord hath forgotten me.
Amma Sihiyona ta ce, “Ubangiji ya yashe ni, Ubangiji ya manta da ni.”
15 Can a woman forget her sucking child, that she should not have compassion on the son of her womb? Even these forget, but I will not forget thee.
“Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa? Mai yiwuwa ta manta, amma ba zan taɓa manta da ke ba!
16 Lo, I have graven thee upon the palms of [my] hands; thy walls are continually before me.
Duba, na zāna ki a tafin hannuwana; katangarki kullum suna a gabana.
17 Thy sons shall make haste; thy destroyers and they that laid thee waste shall go forth from thee.
’Ya’yanki maza su komo da gaggawa, waɗanda suka lalatar da ke kuwa za su bar ki.
18 Lift up thine eyes round about and behold: they all gather themselves together, they come to thee. As I live, saith Jehovah, thou shalt indeed clothe thee with them all as with an ornament, and bind them on as a bride doth.
Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye; dukan’ya’yanki sun taru suka kuma dawo gare ki. Muddin ina raye,” in ji Ubangiji, “Za ki yafa su duka kamar kayan ado; za ki yi ado da su, kamar amarya.
19 For [in] thy waste and thy desolate places, and thy destroyed land, thou shalt even now be too straitened by reason of the inhabitants, and they that swallowed thee up shall be far away.
“Ko da yake an lalatar da ke aka kuma mai da ke kufai ƙasarki kuma ta zama kango, yanzu za ki kāsa sosai saboda yawan mutanenki, kuma waɗanda suka cinye ki za su kasance can da nisa.
20 The children of thy bereavement shall yet say in thine ears, The place is too narrow for me: make room for me, that I may dwell.
’Ya’yan da aka haifa a lokacin baƙin cikinki za su ce a kunnenki, ‘Wannan wuri ya yi mana kaɗan ƙwarai; ki ƙara mana wurin zama.’
21 And thou shalt say in thy heart, Who hath borne me these, seeing I had lost my children and was desolate, an exile, and driven about? and who hath brought up these? behold, I was left alone; these, where were they?
Sa’an nan za ki ce a zuciyarki, ‘Wa ya haifa waɗannan? Na yi baƙin ciki na kuma zama wadda ba ta haihuwa; an yi mini daurin talala aka kuma ƙi ni. Wane ne ya yi renon waɗannan? An bar ni ni kaɗai, amma waɗannan, ina suka fito?’”
22 Thus saith the Lord Jehovah: Behold, I will lift up my hand to the nations, and set up my banner to the peoples; and they shall bring thy sons in [their] bosom, and thy daughters shall be carried upon the shoulder.
Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Duba, zan yi alama wa Al’ummai, zan ɗaga tutana wa mutane; za su kawo’ya’yanki maza a hannuwansu su riƙe’ya’yanki mata a kafaɗunsu.
23 And kings shall be thy nursing-fathers, and their princesses thy nursing-mothers: they shall bow down to thee with the face toward the earth, and lick up the dust of thy feet. And thou shalt know that I [am] Jehovah; for they shall not be ashamed who wait on me.
Sarakuna za su zama kamar iyayen reno, sarauniyoyinsu kuma za su yi renonku kamar uwaye. Za su rusuna a gabanki da fuskokinsu har ƙasa; za su lashe ƙura a ƙafafunki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji; waɗanda suke sa zuciya gare ni ba za su sha kunya ba.”
24 Shall the prey be taken from the mighty? and shall he that is rightfully captive be delivered?
Za a iya ƙwace ganima daga jarumawa, ko a kuɓutar da kamammu daga hannun marasa tsoro?
25 For thus saith Jehovah: Even the captive of the mighty shall be taken away, and the prey of the terrible shall be delivered; and I will strive with him that striveth with thee, and I will save thy children.
Amma ga abin da Ubangiji yana cewa, “I, za a ƙwace kamammu daga jarumawa, a kuma karɓe ganima daga hannun marasa tsoro; zan gwabza da waɗanda suke gwabzawa da ke, zan kuwa ceci’ya’yanki.
26 And I will feed them that oppress thee with their own flesh; and they shall be drunken with their own blood, as with new wine. And all flesh shall know that I, Jehovah, [am] thy Saviour and thy Redeemer, the Mighty One of Jacob.
Zan sa masu zaluntarki su ci naman jikinsu; za su bugu da jininsu, sai ka ce sun sha ruwan inabi. Sa’an nan dukan mutane za su sani cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki, Mai Fansarki, Maɗaukakin nan na Yaƙub.”

< Isaiah 49 >