< 2 Corinthians 11 >
1 Would that ye would bear with me [in] a little folly; but indeed bear with me.
Ina fata za ku yi haƙuri da’yar wautata. Amma, ai, kun riga kun yi haƙuri.
2 For I am jealous as to you with a jealousy [which is] of God; for I have espoused you unto one man, to present [you] a chaste virgin to Christ.
Ina kishinku da kishi irin na Allah. Na yi muku alkawarin aure ga miji ɗaya, Kiristi, domin in miƙa ku a gare shi kamar budurwa zalla.
3 But I fear lest by any means, as the serpent deceived Eve by his craft, [so] your thoughts should be corrupted from simplicity as to the Christ.
Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi.
4 For if indeed he that comes preaches another Jesus, whom we have not preached, or ye get a different Spirit, which ye have not got, or a different glad tidings, which ye have not received, ye might well bear with [it].
Gama in wani ya zo wurinku yana wa’azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa’azinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai.
5 For I reckon that in nothing I am behind those who are in surpassing degree apostles.
Amma a ganina waɗancan da kuke ce da su “manyan manzanni” ba su fi ni da wani abu ba.
6 But if [I am] a simple person in speech, yet not in knowledge, but in everything making [the truth] manifest in all things to you.
Mai yiwuwa ni ba horarre ba ne a magana, amma ina da sani. Mun kuwa bayyana muku wannan a sarari, ta kowace hanya.
7 Have I committed sin, abasing myself in order that ye might be exalted, because I gratuitously announced to you the glad tidings of God?
Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku wa’azin bisharar Allah kyauta?
8 I spoiled other assemblies, receiving hire for ministry towards you.
Na yi wa waɗansu ikkilisiyoyi ƙwace ta wurin karɓar taimako daga wurinsu, domin in yi muku hidima.
9 And being present with you and lacking, I did not lazily burden any one, (for the brethren who came from Macedonia supplied what I lacked, ) and in everything I kept myself from being a burden to you, and will keep myself.
Sa’ad da nake tare da ku kuma nake zaman rashi, ban nawaita wa kowa ba, gama’yan’uwan da suka zo daga Makidoniya sun biya bukata. Na kiyaye kaina daga nawaita muku ta kowace hanya, zan kuma ci gaba da yin haka.
10 [The] truth of Christ is in me that this boasting shall not be stopped as to me in the regions of Achaia.
Ba shakka, kamar yadda gaskiyar Kiristi take a cikina, babu wani a yankunan Akayya da zai iya hana yin taƙaman nan tawa.
11 Why? because I do not love you? God knows.
Don me? Don ba na ƙaunar ku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku!
12 But what I do, I will also do, that I may cut off the opportunity of those wishing [for] an opportunity, that wherein they boast they may be found even as we.
Zan kuma ci gaba da yin abin da nake yi, domin in toshe kafar mutanen nan da suke fariya, suna nema mu daidaita da su.
13 For such [are] false apostles, deceitful workers, transforming themselves into apostles of Christ.
Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, ma’aikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne.
14 And [it is] not wonderful, for Satan himself transforms himself into an angel of light.
Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne.
15 It is no great thing therefore if his ministers also transform themselves as ministers of righteousness; whose end shall be according to their works.
Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.
16 Again I say, Let not any one think me to be a fool; but if otherwise, receive me then even as a fool, that I also may boast myself some little.
Ina sāke faɗa, kada wani yă ɗauka ni wawa ne. Amma in kun ɗauke ni haka, to, sai ku karɓe ni kamar yadda kuke karɓan wawa, domin in ɗan in yi taƙama.
17 What I speak I do not speak according to [the] Lord, but as in folly, in this confidence of boasting.
A wannan taƙamata ba na magana yadda Ubangiji zai yi ba ne, sai dai magana ce irin ta wawa.
18 Since many boast according to flesh, I also will boast.
Da yake mutane da yawa suna taƙama irin ta duniya, ni ma haka zan yi.
19 For ye bear fools readily, being wise.
Ku kam kuna da wayo sosai, har kuna jimre wa wawaye da murna!
20 For ye bear if any one bring you into bondage, if any one devour [you], if any one get [your money], if any one exalt himself, if any one beat you on the face.
Gaskiyar ita ce, kuna haƙuri da duk wanda ya sa ku bauta ko ya cuce ku ko ya more ku ko ya nuna muku isa ko kuma ya mare ku a fuska.
21 I speak as to dishonour, as though we had been weak; but wherein any one is daring, (I speak in folly, ) I also am daring.
Ina jin kunya in ce mun nuna kāsawa da ba mu yi waɗannan abubuwan ba! Abin da wani yake da ƙarfin hali yin taƙama a kai, shi ne ni ma nake ƙarfin hali yin taƙama a kai. Ina magana kamar wawa ne.
22 Are they Hebrews? I also. Are they Israelites? I also. Are they seed of Abraham? I also.
In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra’ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka.
23 Are they ministers of Christ? (I speak as being beside myself) I above measure [so]; in labours exceedingly abundant, in stripes to excess, in prisons exceedingly abundant, in deaths oft.
In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri.
24 From the Jews five times have I received forty [stripes], save one.
Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu.
25 Thrice have I been scourged, once I have been stoned, three times I have suffered shipwreck, a night and day I passed in the deep:
Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni.
26 in journeyings often, in perils of rivers, in perils of robbers, in perils from [my own] race, in perils from [the] nations, in perils in [the] city, in perils in [the] desert, in perils on [the] sea, in perils among false brethren;
Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin’yan’uwa na ƙarya.
27 in labour and toil, in watchings often, in hunger and thirst, in fastings often, in cold and nakedness.
Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara.
28 Besides those things that are without, the crowd [of cares] pressing on me daily, the burden of all the assemblies.
Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi.
29 Who is weak, and I am not weak? Who is stumbled, and I burn not?
Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji shi a jikina ba? Wane ne ya fāɗi cikin zunubi, da ban ji zafin wannan ba?
30 If it is needful to boast, I will boast in the things which concern my infirmity.
In ma lalle ne in yi taƙama, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suka nuna rashin ƙarfina.
31 The God and Father of the Lord Jesus knows — he who is blessed for ever — that I do not lie. (aiōn )
Allah Uban Ubangiji Yesu Kiristi, wanda yabo ta tabbata a gare shi har abada, ya san cewa ba ƙarya nake yi ba. (aiōn )
32 In Damascus the ethnarch of Aretas the king kept the city of the Damascenes shut up, wishing to take me;
A Damaskus, gwamnan da yake ƙarƙashin Sarki Aretas, ya sa tsare ƙofofin birnin Damaskus, don yă kama ni.
33 and through a window in a basket I was let down by the wall, and escaped his hands.
Amma aka saukar da ni cikin kwando ta tagar katanga, na kuɓuce masa.