< Hebrews 12 >

1 Furthermore, since we also have so great a cloud of witnesses over us, let us set aside every burden and sin which may surround us, and advance, through patience, to the struggle offered to us.
Da shike muna kewaye da wannan irin kasaitaccen taro na shaidu, sai mu watsar da dukkan abubuwan dake nawaita mana da kuma zunubin da zai saurin makale ma na. Bari a cikin hakuri mu yi tseren da ke gabanmu.
2 Let us gaze upon Jesus, as the Author and the completion of our faith, who, having joy laid out before him, endured the cross, disregarding the shame, and who now sits at the right hand of the throne of God.
Bari mu kafa idonmu ga Yesu, wanda shine mafarin bangaskiyarmu da cikarta. Wanda sabili da murnar da a ka sa a gabansa ya jimre giciye, ya kuma yi watsi da kunyarsa, wanda kuma ya zauna a hannun dama na kursiyin Allah.
3 So then, meditate upon him who endured such adversity from sinners against himself, so that you may not become weary, failing in your souls.
Ku dube shi wanda ya jimre irin wannan adawa daga masu zunubi, domin kada ku gaji ko ku karai.
4 For you have not yet resisted unto blood, while striving against sin.
Ba ku yi tsayayya ko jayayya da zunubi har ta kai ga zub da jininku ba tukunna. Kun kuma manta da gargadin da a ka yi maku a matsayin 'ya'ya:
5 And you have forgotten the consolation which speaks to you like sons, saying: “My son, do not be willing to neglect the discipline of the Lord. Neither should you become weary, while being rebuked by him.”
''Dana, kada ka dauki horon Ubangiji da wasa, kadda kuma ka yi suwu lokacin da ka sami horonsa,''
6 For whomever the Lord loves, he chastises. And every son whom he accepts, he scourges.
Domin kuwa Ubangiji yana horon dukkan wadanda yake kauna, yana kuma hukunta duk wadanda ya karba.
7 Persevere in discipline. God presents you to himself as sons. But what son is there, whom his father does not correct?
Ku daure wahala a matsayin horo. Allah yana yi da ku kamar 'ya'yansa, domin kuwa wanne da ne wanda ubansa bazai yi masa horo ba?
8 But if you are without that discipline in which all have become sharers, then you are of adultery, and you are not sons.
Amma idan baku da horo kamar yadda sauran mutane ke da shi, kun zama shegu kenan ba 'ya'ya ba.
9 Then, too, we have certainly had the fathers of our flesh as instructors, and we reverenced them. Should we not obey the Father of spirits all the more, and so live?
Hakannan kuma kamar yadda muke da iyaye a duniya wadanda suke yi mana horo, kuma muna basu daraja. To ba sai mu yiwa Ubanmu na Ruhaniya biyayya don mu rayu ba?
10 And indeed, for a few days and according to their own wishes, they instructed us. But he does so to our benefit, so that we may receive his sanctification.
Ta wani fanni kuwa iyayenmu suna yi mana horo na kwanaki kadan bisa ga yadda suka ga ya dace, Amma Allah kuwa yana yi mana horo domin anfanin kanmu, domin kuma mu sami rabo daga cikin tsarkinsa.
11 Now every discipline, in the present time, does not seem a gladness, of course, but a grief. But afterwards, it will repay a most peaceful fruit of justice to those who become trained in it.
Ba horon da ke da dadi a lokacin yinsa, amma sai zafi. Sai dai kuma bayan haka yakan haifar da 'ya'ya na ruhaniya da kuma adalci ga dukkan wadanda aka yi rainonsu a ciki.
12 Because of this, lift up your lazy hands and your lax knees,
Don haka sai ku karfafa hannayenku da ke reto, da kuma guwawunku da ke kaduwa.
13 and straighten the path of your feet, so that no one, being lame, may wander astray, but instead may be healed.
Ku bi hanyoyi mikakku domin abin da ya gurgunce kada ya karye amma ya warke.
14 Pursue peace with everyone. Pursue sanctity, without which no one shall see God.
Ku bidi salama da kowa, da kuma rayuwar tsarki wanda in ba tare da shi, babu wanda zai ga Allah.
15 Be contemplative, lest anyone lack the grace of God, lest any root of bitterness spring up and impede you, and by it, many might be defiled,
Ku mai da hankali domin kada waninku ya rasa, alherin Allah, kuma kada wani tushe mai daci ya tsiro a cikinku har ya haifar da fitina, domin kada da dama daga cikinku su gurbata ta wurinsa.
16 lest any fornicator or worldly person be like Esau, who, for the sake of one meal, sold his birthright.
Ku yi hankali kuma kada a sami mazinanci ko marar ibada a cikinku, kamar Isuwa, wanda sabili da abinci ya sayar da 'yancinsa na dan fari.
17 For you know that afterwards, when he desired to inherit the benediction, he was rejected. For he found no place for repentance, even though he had sought it with tears.
Kun kuwa san cewa sa'adda ya yi marmarin ya gaji albarka a gaba, an kishi, domin kuwa bai sami damar tuba ba, ko da shike ya nema har da hawaye.
18 But you have not drawn near to a tangible mountain, or a burning fire, or a whirlwind, or a mist, or a storm,
Domin kuwa baku zo ga dusen da ake tabawa da hannu ba, dutse ne mai ci da wuta, da tukuki da bakin hayaki da hadari.
19 or the sound of a trumpet, or a voice of words. Those who had experienced these things excused themselves, lest the Word be spoken to them.
Ba Ku zo ga karar kaho mai ban razana da murya mai firgitarwa ba, da masu sauraro suka yi roko kar su sake jinta.
20 For they could not bear what was said, and so, if even a beast would have touched the mountain, it would have been stoned.
Don basu iya jimre abin da aka yi doka a kan saba: ''koma dabba ce ta taba dutsen, sai a jejjefe ta.''
21 And what was seen was so terrible that even Moses said: “I am terrified, and so, I tremble.”
Abin tsoro ne kuwa kwarai, har Musa yace, ''A tsoroce nake kwarai har na firgita.''
22 But you have drawn near to mount Zion, and to the city of the living God, to the heavenly Jerusalem, and to the company of many thousands of Angels,
Maimakon haka kun zone ga Dutsen Sihiyona da kuma birni na Allah mai Rai, kuma na Urushalima ta Samniya, da kuma dubun dubban mala'iku cikin murna da farin ciki.
23 and to the Church of the first-born, those who have been inscribed in the heavens, and to God, the judge of all, and to the spirits of the just made perfect,
Kun zo taro na dukkan 'ya'yan fari, rubuttatu a sama, kuma kun zo ga Allah wanda shine alkalin dukka, hakannan kuma zuwa ga ruhu na adalai wanda a ka rigaya aka tsarkake.
24 and to Jesus, the Mediator of the New Testament, and to a sprinkling of blood, which speaks better than the blood of Abel.
Kun zo ga Yesu, wanda shine matsakancin sabon alkawari, kuma ga jinin yayyafawa da ke magana fiye da na jinin Habila.
25 Be careful not to reject the One who is speaking. For if those who rejected him who was speaking upon the earth were not able to escape, so much more we who might turn away from the One who is speaking to us from heaven.
Ku yi lura kada ku ki wannan da ke yi mu ku magana. Gama in har basu kubuta yayin da su ka yi jayayya da wanda ya yi mu su gargadi a duniya ba, balle ma mu ba za mu kubuta ba in mun ki wanda ke mana gargadi daga sama.
26 Then, his voice moved the earth. But now, he makes a promise, saying: “There is still one more time, and then I will move, not only the earth, but also heaven itself.”
A wani karo, muryar sa ta girgiza duniya. Amma yanzu yayi alkawari da cewa, ''Har'ila yau ba duniyar kadai zan girgiza ba, amma har da sammai.''
27 And so, in saying, “There is still one more time,” he declares the transfer of the moveable things of creation, so that those things which are immoveable may remain.
Wannan kalma, ''Harl'ila yau,'' ta bayyana cirewar abubuwan nan da za su girgizu, wato abubuwan da a ka halitta, domin abubuwan da ba zasu girgizu ba su kasance.
28 Thus, in receiving an immoveable kingdom, we have grace. So, through grace, let us be of service, by pleasing God with fear and reverence.
Don haka, samun mulkin da ba za ya girgizu ba, sai mu zama masu godiya, kuma a cikin wannan yanayi mu yi wa Allah sujada cikin daraja da tsaninin gimamawa.
29 For our God is a consuming fire.
Domin kuwa Allahnmu wuta ne mai konewa.

< Hebrews 12 >