< Amos 2 >

1 Thus says the Lord: For three wicked deeds of Moab, and for four, I will not convert him, in so far as he has burned the bones of the king of Idumea, all the way to ashes.
Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Mowab, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Gama ya ƙone ƙasusuwan sarkin Edom suka zama sai ka ce toka.
2 And I will send a fire onto Moab, and it will devour the buildings of Kerioth. And Moab will die with a noise, with the blare of a trumpet.
Zan sa wuta a Mowab da za tă ƙone kagarun Keriyot Mowab za tă gangara cikin hayaniya mai girma cikin kururuwar yaƙi da kuma ƙarar ƙaho.
3 And I will destroy the judge in their midst, and I will execute all his leaders with him, says the Lord.
Zan hallaka mai mulkinta zan kuma kashe shugabanninta.”
4 Thus says the Lord: For three wicked deeds of Judah, and for four, I will not convert him, in so far as he has rejected the law of the Lord and has not kept his commandments. For their idols, which their fathers followed, have deceived them.
Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Yahuda, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Gama sun ƙi bin dokar Ubangiji ba su kuma yi biyayya da ƙa’idodinsa ba, domin allolin ƙarya sun ruɗe su, allolin da kakanninsu suka bauta.
5 And I will send a fire onto Judah, and it will devour the buildings of Jerusalem.
Zan sa wuta a Yahuda da za tă ƙone kagarun Urushalima.”
6 Thus says the Lord: For three wicked deeds of Israel, and for four, I will not convert him, in so far as he has sold the just for silver and the poor for shoes.
Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Isra’ila, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun sayar da adalai waɗanda suka kāsa biyan bashinsu. Sun kuma sayar da matalauta waɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba.
7 They grind the heads of the poor into the dust of the earth, and they divert the way of the humble. And the son, as well as his father, have gone to the same girl, so that they outrage my holy name.
Sun tattake kawunan matalauta kamar yadda suke taka laka suka kuma danne wa marasa galihu gaskiya. Uba da ɗa su na kwana da yarinya guda, suna kuma ɓata sunana mai tsarki.
8 And they have lain on garments taken in pledge next to every altar. And they drank the wine of the damned in the house of their God.
Suna kwanciya kurkusa da kowane bagade a kan tufafin da suka karɓe jingina. A gidajen allolinsu sukan sha ruwan inabin da suka karɓo daga wurin waɗanda suka ci wa tara.
9 Yet I exterminated the Amorites before their face, whose height was like the height of cedars, and whose strength was like the oak. And I crushed his fruit from above and his roots below.
“Na hallaka mutumin Amoriyawa a gabansu, ko da yake ya yi dogo kamar itacen al’ul kuma mai ƙarfi kamar itacen oak. Na hallaka’ya’yan itatuwansa daga sama, da kuma jijiyoyinsa daga ƙasa.
10 It is I who caused you to ascend from the land of Egypt, and I led you in the wilderness for forty years, so that you might possess the land of the Amorite.
Na fitar da ku daga ƙasar Masar, na kuma bishe ku tsawon shekaru arba’in a cikin hamada don in ba ku ƙasar Amoriyawa.
11 And I stirred up prophets from your sons, and Nazirites from your young men. Is it not so, sons of Israel, says the Lord?
“Na kuma tā da annabawa daga cikin’ya’yanku maza waɗansu kuma su zama keɓaɓɓu daga cikin samarinku. Ba haka ba ne, mutanen Isra’ila?” In ji Ubangiji.
12 Yet you would offer wine to the Nazirites, and you would command the prophets, saying: “Do not prophesy.”
“Amma kuka sa keɓaɓɓun suka sha ruwan inabi kuka kuma umarci annabawa kada su yi annabci.
13 Behold, I will creak under you, just as a wagon creaks that is laden with hay.
“Saboda haka, yanzu zan murƙushe ku kamar yadda amalanke yakan murƙushe sa’ad da aka yi masa labtun hatsi.
14 And flight will perish from the swift, and the strong will not maintain his strength, and the healthy will not save his life.
Masu gudu da sauri ba za su tsira ba, masu ƙarfi ba za su iya yin amfani da ƙarfinsu ba, jarumi kuma ba zai iya ceton ransa ba.
15 And one holding the bow will not stand firm, and the swift of foot will not be saved, and the rider on the horse will not save his life.
’Yan baka ba za su iya dāgewa ba, masu saurin gudu ba za su tsira ba mahayin dawakai kuma ba zai tsere da ransa ba.
16 And the stout of heart among the strong will flee away naked in that day, says the Lord.
Ko jarumawa mafi jaruntaka za su gudu tsirara a ranan nan,” in ji Ubangiji.

< Amos 2 >