< Acts 3 >
1 Now Peter and John went up to the temple at the ninth hour of prayer.
Sa'adda Bitrus da Yahaya suna hanya zuwa haikali a lokacin addu'ar karfe uku.
2 And a certain man, who was lame from his mother’s womb, was being carried in. They would lay him every day at the gate of the temple, which is called the Beautiful, so that he might request alms from those entering into the temple.
Wani mutum, gurgu ne tun daga haihuwa, ana daukar sa kulluyomi zuwa kofar haikali da ake kira Kyakkyawa, domin bara gun mutanen da ke shiga haikalin.
3 And this man, when he had seen Peter and John beginning to enter the temple, was begging, so that he might receive alms.
Da ya ga Bitrus da Yahaya suna shiga haikalin, sai ya roke su sadaka.
4 Then Peter and John, gazing at him, said, “Look at us.”
Bitrus da Yahaya kuwa suka zuba masa ido, Bitrus ya ce, ''Ka dube mu.''
5 And he looked intently at them, hoping that he might receive something from them.
Gurgun nan kuwa ya dube su, yana tsammanin zai sami wani abu a wurin su.
6 But Peter said: “Silver and gold is not mine. But what I have, I give to you. In the name of Jesus Christ the Nazarene, rise up and walk.”
Amma Bitrus ya ce, “Azurfa da Zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, zan baka. A cikin sunan Yesu Almasihu Banazare, Yi tafiya''
7 And taking him by the right hand, he lifted him up. And immediately his legs and feet were strengthened.
Bitrus ya kama hannun damarsa, ya daga shi; nan da nan kafafunsa da kashin idon sawayensa suka samu karfi.
8 And leaping up, he stood and walked around. And he entered with them into the temple, walking and leaping and praising God.
Da gurgun ya yunkura, ya mike tsaye sai ya fara takawa; ya shiga haikali tare da Bitrus da Yahaya, yana takawa, yana tsalle, yana kuma girmama Allah.
9 And all the people saw him walking and praising God.
Dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana kuma yabon Allah.
10 And they recognized him, that he was the same one who was sitting for alms at the Beautiful Gate of the temple. And they were filled with awe and amazement at what had happened to him.
Sun lura cewa, shine mutumin da ke zama yana bara a Kyakyawar kofar haikali; sai suka cika da mamaki domin abin da ya faru.
11 Then, as he held on to Peter and John, all the people ran to them at the portico, which is called Solomon’s, in astonishment.
Yayin da yake rike da Bitrus da Yahaya, dukan jama'a suka matso wurinsu, a gefen dakalin Sulaimanu, suna ta mamaki kwarai.
12 But Peter, seeing this, responded to the people: “Men of Israel, why do you wonder at this? Or why do you stare at us, as if it were by our own strength or power that we caused this man to walk?
Da Bitrus ya ga haka ya amsa wa jama'ar, “Ya ku mutanen Isra'ila, don me ku ke mamaki?” Don me ku ka zura mana ido, kamar mu ne muka sa shi ya yi tafiya da ikon kanmu ko adalcin mu?
13 The God of Abraham and the God of Isaac and the God of Jacob, the God of our fathers, has glorified his Son Jesus, whom you, indeed, handed over and denied before the face of Pilate, when he was giving judgment to release him.
Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allah na iyayenmu ya girmama bawansa Yesu. Shi kuka ki kun kuma bashe shi a gaban Bilatus da ya so ya sake shi.
14 Then you denied the Holy and Just One, and petitioned for a murderous man to be given to you.
Kuka ki Mai Tsarkin nan, Mai Adalcin, maimakon haka kuka ce a sakkar maku mai kisan kai.
15 Truly, it was the Author of Life whom you put to death, whom God raised from the dead, to whom we are witnesses.
Kun kashe mai ba da rai, wanda Allah ya tayar daga matattu, mu kuwa shaidu ne ga wannan al'amari.
16 And by faith in his name, this man, whom you have seen and known, has confirmed his name. And faith through him has given this man complete health in the sight of you all.
Yanzu, ta bangaskiya ga sunansa - wannan mutum da kuke gani kuma kun san shi - ta wurin wannan sunan ne ya sami karfi. Bangaskiya cikin Yesu ta ba shi cikakkiyar lafiya, a gabanku duka.
17 And now, brothers, I know that you did this through ignorance, just as your leaders also did.
Ya ku 'yan'uwa, na san kun yi haka ne cikin rashin sani, yadda shugabaninku suka yi.
18 But in this way God has fulfilled the things that he announced beforehand through the mouth of all the Prophets: that his Christ would suffer.
Amma duk abubuwan da Allah ya fada ta bakin dukan anabawansa, cewa Almasihunsa zai sha wahala, yanzu ya cika.
19 Therefore, repent and be converted, so that your sins may be wiped away.
Saboda haka, Ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, domin lokacin sabuntuwa daga wurin Ubangiji ya zo;
20 And then, when the time of consolation will have arrived from the presence of the Lord, he will send the One who was foretold to you, Jesus Christ,
domin a aiko maku da Almasihu wanda aka kaddara wato, Yesu.
21 whom heaven certainly must take up, until the time of the restoration of all things, which God has spoken of by the mouth of his holy prophets, from ages past. (aiōn )
Shine wanda dole sama ta karbe shi har zuwa lokacin komo da dukan abubuwa, game da abubuwan da Allah ya fada tun da ta bakin annabawansa tsarkaka. (aiōn )
22 Indeed, Moses said: ‘For the Lord your God shall raise up a Prophet for you from your brothers, one like me; the same shall you listen to according to everything whatsoever that he shall speak to you.
Musa hakika ya ce, 'Ubangiji Allah zai tayar maku da wani annabi kamar ni daga cikin, 'yan'uwanku. Za ku saurari dukan abin da zai fada maku.
23 And this shall be: every soul who will not listen to that Prophet shall be exterminated from the people.’
Zai kasance kowanne mutum da bai saurari annabin nan ba za a kau da shi gabadaya daga cikin mutanensa.'
24 And all the prophets who have spoken, from Samuel and thereafter, have announced these days.
I, dukan annabawa tun daga Sama'ila da wadanda suka zo bayansa, sun yi magana sun ambaci wadannan kwanaki.
25 You are sons of the prophets and of the testament which God has appointed for our fathers, saying to Abraham: ‘And by your offspring all the families of the earth shall be blessed.’
Kune 'ya'yan annabawa da na alkawari wanda Allah ya yi da kakanninku, yadda ya ce wa Ibrahim, 'Daga zuriyarka dukan al'uman duniya za su sami albarka.'
26 God raised up his Son and sent him first to you, to bless you, so that each one may turn himself away from his wickedness.”
Bayan da Allah ya ta da bawansa, a gareku ne ya fara aiko shi, domin ya albarkace ku tawurin juyadda kowannenku daga muguntarsa.”