< 1 Timothy 6 >

1 Whoever are servants under the yoke, let them consider their masters to be worthy of every honor, lest the name and doctrine of the Lord be blasphemed.
Duk waɗanda suke ƙarƙashin bauta, ya kamata su ɗauki iyayengijinsu a kan sun cancanci girmamawa matuƙa, don kada a ɓata sunan Allah da kuma koyarwarmu.
2 But those who have believing masters, let them not despise them because they are brothers, but rather serve them all the more because they are believing and beloved, participants of the same service. Teach and exhort these things.
Waɗanda suke da iyayengiji masu bi, to, kada su yi musu reni domin su’yan’uwa ne. A maimako, sai ma su fi bauta musu, saboda waɗanda suke cin moriyar hidimarsu masu bi ne, ƙaunatattu ne kuma a gare su. Waɗannan su ne abubuwan da za ka koya musu ka kuma gargaɗe su.
3 If anyone teaches otherwise, and does not consent to the sound words of our Lord Jesus Christ, and to that doctrine which is in accord with piety,
In wani yana koyarwar ƙarya bai kuma yarda da sahihiyar koyarwar Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma koyarwa ta tsoron Allah ba,
4 then he is arrogant, knowing nothing, yet languishing amid the questions and quarrels of words. From these arise envy, contention, blasphemy, evil suspicions:
yana cike da girman kai bai kuma san kome ba. Yana da mugun halin son gardama da muhawwara game da kalmomin da suke kawo kishi, rikici, maganar ƙeta, da mugayen zace-zace
5 the conflicts of men who have been corrupted in mind and deprived of truth, who consider profit to be piety.
da yawan tankiya tsakanin mutane masu mugun hali, waɗanda aka raba su da gaskiya, suke kuma tsammani cewa bin Allah wata hanya ce ta samun kuɗi.
6 But piety with sufficiency is great gain.
Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa.
7 For we brought nothing into this world, and there is no doubt that we can take nothing away.
Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba.
8 But, having nourishment and some kind of covering, we should be content with these.
In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su.
9 For those who want to become rich fall into temptation and into the snare of the devil and into many useless and harmful desires, which submerge men in destruction and in perdition.
Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka.
10 For desire is the root of all evils. Some persons, hungering in this way, have strayed from the faith and have entangled themselves in many sorrows.
Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.
11 But you, O man of God, flee from these things, and truly pursue justice, piety, faith, charity, patience, meekness.
Amma kai, mutumin Allah, ka guji duk wannan, ka kuma nemi adalci, tsoron Allah, bangaskiya, ƙauna, jimrewa da kuma hankali.
12 Fight the good fight of faith. Take hold of the eternal life to which you have been called, and make a good profession of faith in the sight of many witnesses. (aiōnios g166)
Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa. (aiōnios g166)
13 I charge you, in the sight of God, who enlivens all things, and in the sight of Christ Jesus, who gave the testimony of a good profession under Pontius Pilate,
Na umarce ka, a gaban Allah mai ba da rai ga kome, da kuma Kiristi Yesu wanda yayinda yake ba da shaida a gaban Buntus Bilatus ya yi kyakkyawar shaida,
14 to observe the commandment, immaculately, irreproachably, unto the return of our Lord Jesus Christ.
ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yă bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi,
15 For at the proper time, he shall reveal the blessed and only Power, the King of kings and the Lord of lords,
wanda Allah zai kawo a daidai lokaci, Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji,
16 who alone holds immortality, and who inhabits the inaccessible light, whom no man has seen, nor even is able to see, to whom is honor and everlasting dominion. Amen. (aiōnios g166)
wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin. (aiōnios g166)
17 Instruct the wealthy of this age not to have a superior attitude, nor to hope in the uncertainty of riches, but in the living God, who offers us everything in abundance to enjoy, (aiōn g165)
Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu. (aiōn g165)
18 and to do good, to become rich in good works, to donate readily, to share,
Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako.
19 to gather for themselves the treasure of a good foundation for the future, so that they may obtain true life.
Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.
20 O Timothy, guard what has been deposited with you, avoiding the voice of profane novelties and of opposing ideas, which are falsely called knowledge.
Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi,
21 Certain persons, promising these things, have perished from the faith. May grace be with you. Amen.
wanda waɗansu suka furta kuma ta yin haka suka bauɗe daga bangaskiya. Alheri yă kasance tare da ku.

< 1 Timothy 6 >