< Genesis 33 >

1 Then Jacob, lifting up his eyes, saw Esau coming with his four hundred men. So he made a division of the children between Leah and Rachel and the two women-servants.
Yaƙub ya ɗaga ido ke nan, sai ga Isuwa yana zuwa tare da mutanensa ɗari huɗu; saboda haka sai ya rarraba’ya’yan wa Liyatu, Rahila da kuma matan nan biyu masu hidima.
2 He put the servants and their children in front, Leah and her children after them, and Rachel and Joseph at the back.
Ya sa matan nan biyu masu hidima da’ya’yansu a gaba, Liyatu da’ya’yanta biye, sa’an nan Rahila da Yusuf a baya.
3 And he himself, going before them, went down on his face to the earth seven times till he came near his brother.
Shi kansa ya sha gabansu, ya rusuna har ƙasa sau bakwai, kafin ya kai kusa da inda ɗan’uwansa Isuwa yake.
4 Then Esau came running up to him, and folding him in his arms, gave him a kiss: and the two of them were overcome with weeping.
Amma Isuwa ya ruga a guje ya sadu da Yaƙub ya rungume shi; ya faɗa a wuyansa ya sumbace shi. Suka kuma yi kuka.
5 Then Esau, lifting up his eyes, saw the women and the children, and said, Who are these with you? And he said, The children whom God in his mercy has given to your servant.
Sa’an nan Isuwa ya ɗaga ido ya ga mata da’ya’ya. Ya yi tambaya, “Su wane ne waɗannan tare da kai?” Yaƙub ya amsa, “Su ne’ya’yan da Allah cikin alheri ya ba bawanka.”
6 Then the servants and their children came near, and went down on their faces.
Sai matan nan biyu masu hidima da’ya’yansu suka matso kusa suka durƙusa.
7 And Leah came near with her children, and then Joseph and Rachel, and they did the same.
Biye da su, Liyatu da’ya’yanta suka zo suka rusuna. A ƙarshe duka, sai Yusuf da Rahila suka zo, su ma suka rusuna.
8 And he said, What were all those herds which I saw on the way? And Jacob said, They were an offering so that I might have grace in my lord's eyes.
Isuwa ya yi tambaya, “Me kake nufi da dukan abubuwan nan da na sadu da su ana korarsu?” Sai Yaƙub ya ce, “Don in sami tagomashi a idanunka ne, ranka yă daɗe.”
9 But Esau said, I have enough; keep what is yours, my brother, for yourself.
Amma Isuwa ya ce, “Na riga na sami abin da ya ishe ni, ɗan’uwana. Riƙe abin da kake da shi don kanka.”
10 And Jacob said, Not so; but if I have grace in your eyes, take them as a sign of my love, for I have seen your face as one may see the face of God, and you have been pleased with me.
Sai Yaƙub ya ce, “A’a, ina roƙonka, in na sami tagomashi a idanunka, sai ka karɓi wannan kyautai daga gare ni. Gama ganin fuskarka kamar ganin fuskar Allah ne, yanzu da ka karɓe ni da farin ciki.
11 Take my offering then, with my blessing; for God has been very good to me and I have enough: so at his strong request, he took it.
Ina roƙonka ka karɓi kyautar da aka kawo maka, gama Allah ya yi mini alheri kuma ina da kome da nake bukata.” Ganin yadda Yaƙub ya nace, sai Isuwa ya karɓa.
12 And he said, Let us go on our journey together, and I will go in front.
Sa’an nan Isuwa ya ce, “Bari mu tafi, zan yi maka rakiya.”
13 But Jacob said, My lord may see that the children are only small, and there are young ones in my flocks and herds: one day's over-driving will be the destruction of all the flock.
Amma Yaƙub ya ce masa, “Ranka yă daɗe, ka san cewa’ya’yan ƙanana ne, dole in lura da tumaki da shanun da suke shayar da jariransu. In aka kore su da gaggawa a rana guda kaɗai, dukan dabbobin za su mutu.
14 Do you, my lord, go on before your servant; I will come on slowly, at the rate at which the cattle and the children are able to go, till I come to my lord at Seir.
Saboda haka bari ranka yă daɗe yă sha gaban bawansa, ni kuma in tafi a hankali bisa ga saurin abin da ake kora a gabana da kuma saurin’ya’yan, sai na iso wurinka ranka yă daɗe, a Seyir.”
15 And Esau said, Then keep some of my men with you. And he said, What need is there for that, if my lord is pleased with me?
Sai Isuwa ya ce, “To, bari in bar waɗansu mutanena tare da kai.” Yaƙub ya ce, “Amma me ya sa za ka yi haka? Bari dai in sami tagomashi a idanunka ranka yă daɗe.”
16 So Esau, turning back that day, went on his way to Seir.
Saboda haka a wannan rana Isuwa ya kama hanyar komawa zuwa Seyir.
17 And Jacob went on to Succoth, where he made a house for himself and put up tents for his cattle: for this reason the place was named Succoth.
Yaƙub kuwa, ya tafi Sukkot, inda ya gina wuri domin kansa, ya kuma yi bukkoki domin dabbobinsa. Shi ya sa aka kira wurin Sukkot.
18 So Jacob came safely from Paddan-aram to the town of Shechem in the land of Canaan, and put up his tents near the town.
Bayan Yaƙub ya zo daga Faddan Aram, ya iso lafiya a birnin Shekem a Kan’ana, ya kuma kafa sansani a ƙofar birni.
19 And for a hundred bits of money he got from the children of Hamor, the builder of Shechem, the field in which he had put up his tents.
Ya sayi fili daga’ya’yan Hamor maza, mahaifin Shekem inda ya kafa tentinsa, a bakin azurfa ɗari.
20 And there he put up an altar, naming it El, the God of Israel.
A can ya kafa bagade ya kuma kira shi El Elohe Isra’ila.

< Genesis 33 >