< Psalms 32 >
1 Of David. A Maskil. Blessed is he whose transgressions are forgiven, whose sins are covered.
Ta Dawuda. Maskil ne. Mai farin ciki ne shi wanda aka gafarta masa laifofinsa, wanda aka shafe zunubansa.
2 Blessed is the man whose iniquity the LORD does not count against him, in whose spirit there is no deceit.
Mai farin ciki ne mutumin da Ubangiji ba ya lissafin zunubinsa a kansa wanda kuma babu ruɗu a ruhunsa.
3 When I kept silent, my bones became brittle from my groaning all day long.
Sa’ad da na yi shiru, ƙasusuwana sun yi ta mutuwa cikin nishina dukan yini.
4 For day and night Your hand was heavy upon me; my strength was drained as in the summer heat.
Gama dare da rana hannunka yana da nauyi a kaina; an shanye ƙarfina ƙaf sai ka ce a zafin bazara. (Sela)
5 Then I acknowledged my sin to You and did not hide my iniquity. I said, “I will confess my transgressions to the LORD,” and You forgave the guilt of my sin.
Sa’an nan na furta zunubina a gare ka ban kuwa ɓoye laifina ba. Na ce, “Zan furta laifofina ga Ubangiji.” Ka kuwa gafarta laifin zunubina. (Sela)
6 Therefore let all the godly pray to You while You may be found. Surely when great waters rise, they will not come near.
Saboda haka bari duk mai tsoron Allah yă yi addu’a gare ka yayinda kake samuwa; tabbatacce sa’ad da manyan ruwaye suka taso, ba za su kai wurinsa ba.
7 You are my hiding place. You protect me from trouble; You surround me with songs of deliverance.
Kai ne wurin ɓuyata; za ka tsare ni daga wahala ka kewaye ni da waƙoƙin ceto. (Sela)
8 I will instruct you and teach you the way you should go; I will give you counsel and watch over you.
Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi; Zan ba ka shawara in kuma lura da kai.
9 Do not be like the horse or mule, which have no understanding; they must be controlled with bit and bridle to make them come to you.
Kada ka zama kamar doki ko doki, wanda ba su da azanci wanda dole sai an bi da su da linzami da ragama in ba haka ba, ba za su zo wurinka ba.
10 Many are the sorrows of the wicked, but loving devotion surrounds him who trusts in the LORD.
Azaban mugu da yawa suke, amma ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa kan kewaye mutumin da ya dogara gare shi.
11 Be glad in the LORD and rejoice, O righteous ones; shout for joy, all you upright in heart.
Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji ku kuma yi murna, ku adalai; ku rera, dukanku waɗanda zuciyarku take daidai!