< Psalms 24 >
1 A Psalm of David. The earth is the LORD’s, and the fullness thereof, the world and all who dwell therein.
Zabura ta Dawuda. Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta, duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta;
2 For He has founded it upon the seas and established it upon the waters.
gama ya gina ta a kan tekuna ya kafa ta a kan ruwaye.
3 Who may ascend the hill of the LORD? Who may stand in His holy place?
Wa zai iya hawan tudun Ubangiji? Wa zai iya tsaya a wurinsa mai tsarki?
4 He who has clean hands and a pure heart, who does not lift up his soul to an idol or swear deceitfully.
Sai wanda yake da hannu mai tsabta da kuma tsabtar zuciya, wanda ba ya ba da ransa ga bautar gunki ko ya rantse bisa abin da yake ƙarya.
5 He will receive blessing from the LORD and vindication from the God of his salvation.
Zai sami albarka daga Ubangiji da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.
6 Such is the generation of those who seek Him, who seek Your face, O God of Jacob.
Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan, waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub. (Sela)
7 Lift up your heads, O gates! Be lifted up, O ancient doors, that the King of Glory may enter!
Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga.
8 Who is this King of Glory? The LORD strong and mighty, the LORD mighty in battle.
Wane ne wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai girma a yaƙi.
9 Lift up your heads, O gates! Be lifted up, O ancient doors, that the King of Glory may enter!
Ku ɗaga kawunanku, ya ku ƙofofi; ku ɗagu, ku daɗaɗɗun ƙofofi, don Sarkin ɗaukaka yă shiga.
10 Who is He, this King of Glory? The LORD of Hosts— He is the King of Glory.
Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji Maɗaukaki, shi ne Sarkin ɗaukaka. (Sela)