< Psalms 20 >

1 For the choirmaster. A Psalm of David. May the LORD answer you in the day of trouble; may the name of the God of Jacob protect you.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ubangiji ya amsa maka sa’ad da ka yi kira cikin wahala; bari sunan Allah na Yaƙub yă kiyaye ka.
2 May He send you help from the sanctuary and sustain you from Zion.
Bari yă aiko maka da taimako daga wuri mai tsarki yă kuma ba ka gudummawa daga Sihiyona.
3 May He remember all your gifts and look favorably on your burnt offerings.
Bari yă tuna da dukan sadakokinka yă kuma karɓi hadayunka na ƙonawa. (Sela)
4 May He give you the desires of your heart and make all your plans succeed.
Bari yă biya maka bukatan ranka yă kuma sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.
5 May we shout for joy at your victory and raise a banner in the name of our God. May the LORD grant all your petitions.
Za mu yi sowa ta farin ciki sa’ad da ka yi nasara mu kuma ɗaga tutotinmu a cikin sunan Allahnmu. Bari Ubangiji yă biya maka dukan bukatunka.
6 Now I know that the LORD saves His anointed; He answers him from His holy heaven with the saving power of His right hand.
Yanzu na san cewa, Ubangiji yakan cece shafaffensa. Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki da ikon ceto na hannun damansa.
7 Some trust in chariots and others in horses, but we trust in the name of the LORD our God.
Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai, amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.
8 They collapse and fall, but we rise up and stand firm.
Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi, amma mu za mu tashi mu tsaya daram.
9 O LORD, save the king. Answer us on the day we call.
Ya Ubangiji, ka ba da nasara ga sarki! Ka amsa mana sa’ad da muka yi kira!

< Psalms 20 >