< Philippians 1 >
1 Paul and Timothy, servants of Christ Jesus, To all the saints in Christ Jesus at Philippi, together with the overseers and deacons:
Bulus da Timoti bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan wadan da aka kebe cikin Almasihu Yesu da ke a Filibi, tare da masu kula da ikilisiya da dikinoni.
2 Grace and peace to you from God our Father and the Lord Jesus Christ.
Bari alheri ya kasance tare da ku da salama daga Allah Ubanmu da Ubagijinmu Yesu Almasihu.
3 I thank my God every time I remember you.
Ina godiya ga Allahna duk lokacin da na tuna da ku.
4 In every prayer for all of you, I always pray with joy,
Ko yaushe cikin addu'a ta dominku duka, da farin ciki na ke addu'a.
5 because of your partnership in the gospel from the first day until now,
Ina godiya domin tarayyar ku a cikin bishara tun daga rana ta fari har ya zuwa yanzu.
6 being confident of this, that He who began a good work in you will carry it on to completion until the day of Christ Jesus.
Na tabbata game da wannan abu, shi wanda ya fara aiki mai kyau a cikinku zai ci gaba da shi har ya kai ga kammala zuwa ranar Yesu Almasihu.
7 It is right for me to feel this way about all of you, since I have you in my heart. For in my chains and in my defense and confirmation of the gospel, you are all partners in grace with me.
Daidai ne in ji haka game da dukanku domin kuna zuciya ta. Dukanku abokan tarayya ta ne cikin alherin Allah wajen dauri na da kuma kariyar bishara, da tabbatar da bishara.
8 God is my witness how I long for all of you with the affection of Christ Jesus.
Domin Allah mashaidi na ne, a kan yadda ina da marmarin ku duka cikin zurfin kaunar Almasihu Yesu.
9 And this is my prayer: that your love may abound more and more in knowledge and depth of insight,
Ina yin wannan addu'a: kaunar ku ta habaka gaba gaba a cikin sani da dukan fahimta.
10 so that you may be able to test and prove what is best and may be pure and blameless for the day of Christ,
Ina addu'a a kan haka domin ku gwada ku zabi mafifitan abubuwa. Ina addu'a domin ku zama sahihai marasa abin zargi a ranar Almasihu.
11 filled with the fruit of righteousness that comes through Jesus Christ, to the glory and praise of God.
Wannan kuma domin a cika ku da 'ya'yan adalci da ake samu ta wurin Yesu Almasihu, zuwa ga daukaka da yabon Allah.
12 Now I want you to know, brothers, that my circumstances have actually served to advance the gospel.
Yanzu ina so ku sani, 'yan'uwa, cewa al'amuran da suka faru da ni sun zama dalilan cin gaban bishara kwarai da gaske.
13 As a result, it has become clear throughout the whole palace guard and to everyone else that I am in chains for Christ.
Sakamakon haka, sarkokina cikin Almasihu sun zama sanannu ga dukan sojojin fada da kuma sauran jama'a,
14 And most of the brothers, confident in the Lord by my chains, now dare more greatly to speak the word without fear.
har galibin 'yan'uwa cikin Ubangiji suka karfafa kwarai sabili da sarkokina, suka fito a fili suka yi shelar maganar Allah gabagadi.
15 It is true that some preach Christ out of envy and rivalry, but others out of goodwill.
Lalle wadansu suna shelar Almasihu cikin kishi da husuma, wadansu kuwa domin kyakyawar manufa.
16 The latter do so in love, knowing that I am appointed for the defense of the gospel.
Masu shelar Almasihu domin kauna sun sani cewa an ajiye ni nan domin in kare bishara.
17 The former, however, preach Christ out of selfish ambition, not sincerely, supposing that they can add to the distress of my chains.
Amma wadansu kuwa suna shelar Almasihu saboda sonkai da rashin gaskiya. A zaton su suna wahalar da ni cikin sarkokina.
18 What then is the issue? Just this: that in every way, whether by false motives or true, Christ is preached. And in this I rejoice. Yes, and I will continue to rejoice,
Sai kuma me? Ta kowace hanya, ko da gangan ko da gaske, shelar Almasihu ake yi, ina kuma murna da wannan! I, zan yi murna.
19 because I know that through your prayers and the provision of the Spirit of Jesus Christ, my distress will turn out for my deliverance.
Domin na sani wannan zai kai ga sanadiyar kubuta ta. Wannan zai faru sabili da addu'ar ku, da kuma taimakon Ruhun Yesu Almasihu.
20 I eagerly expect and hope that I will in no way be ashamed, but will have complete boldness so that now as always Christ will be exalted in my body, whether by life or by death.
Bisa ga abin da hakikance nake tsammani da tabbaci cewa ba zan kunyata ba. Maimakon haka, da dukan karfin hali kamar kullum, da yanzu kuma, ina da burin kawo daukaka ga Almasihu a cikin jikina. Ina da begen Almasihu ya sami daukaka a cikin jikina ko cikin rayuwa ko cikin mutuwa.
21 For to me, to live is Christ, and to die is gain.
Domin ni a gare ni rai Almasihu ne, mutuwa kuwa riba ce.
22 But if I go on living in the body, this will mean fruitful labor for me. So what shall I choose? I do not know.
Amma idan ya zamanto rayuwata cikin jiki za ta kawo amfanin hidima to, ban san wanda zan zaba ba.
23 I am torn between the two. I desire to depart and be with Christ, which is far better indeed.
Amma dukansu biyu suna jan hankali na. Ina da burin in bar nan in kasance tare da Almasihu, wannan ya fiye mani kwarai!
24 But it is more necessary for you that I remain in the body.
Duk da haka rayuwata cikin jiki wajibi ne sabili da ku.
25 Convinced of this, I know that I will remain and will continue with all of you for your progress and joy in the faith,
Tunda shike ina da tabbas a kan wannan, na kuma sani zan rayu, in cigaba da kasancewa da ku duka domin cigaban ku, da farincikin ku, cikin bangaskiya.
26 so that through my coming to you again your exultation in Christ Jesus will resound on account of me.
Sakamakon haka, takamar ku cikin Almasihu Yesu za ta bunkasa sabili da dawowa ta a gare ku.
27 Nevertheless, conduct yourselves in a manner worthy of the gospel of Christ. Then, whether I come and see you or only hear about you in my absence, I will know that you stand firm in one spirit, contending side by side for the faith of the gospel,
Ku tafiyar da al'amuran ku kamar yadda ya cancanci bisharar Almasihu, ku yi haka domin ko na zo in duba ku, ko bana nan inji yadda kuke tsaye daram cikin ruhu guda. Ina fatan in ji cewa da nufi daya kuke fama tare saboda bangaskiyar nan ta bishara.
28 without being frightened in any way by those who oppose you. This is a clear sign of their destruction but of your salvation, and it is from God.
Kada ku tsorata da kome da magabtanku za su yi. Alama ce a gare su ta hallakar su. Amma ku kuwa alama ce ta ceton ku, wannan kuwa daga Allah ne.
29 For it has been granted to you on behalf of Christ not only to believe in Him, but also to suffer for Him,
Gama an yi maku alheri, sabo da Almasihu, ba gaskantawa da Almasihu kawai ba, amma har ma shan wuya dominsa.
30 since you are encountering the same struggle you saw I had, and now hear that I still have.
Kuna da shan wuya irin tawa wanda kuka gani, wanda kun ji nake sha har yanzu.