< Numbers 34 >
1 Then the LORD said to Moses,
Ubangiji ya ce wa Musa,
2 “Command the Israelites and say to them: When you enter the land of Canaan, it will be allotted to you as an inheritance with these boundaries:
“Ka umarci Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga Kan’ana, ƙasar da aka ba ku gādo za tă kasance da waɗannan iyakoki.
3 Your southern border will extend from the Wilderness of Zin along the border of Edom. On the east, your southern border will run from the end of the Salt Sea,
“‘Gefenku na kudu zai haɗa da wani sashin Hamadan Zin ta iyakar Edom. A gabas, iyakarku ta kudu za tă fara daga ƙarshen Tekun Gishiri,
4 cross south of the Ascent of Akrabbim, continue to Zin, and go south of Kadesh-barnea. Then it will go on to Hazar-addar and proceed to Azmon,
tă ƙetare Mashigin Kunama a kudu, tă ci gaba zuwa Zin, sa’an nan tă nufi kudu da Kadesh Barneya. Sa’an nan za tă zarce zuwa Hazar Addar, tă nausa zuwa Azmon,
5 where it will turn from Azmon, join the Brook of Egypt, and end at the Sea.
inda za tă juya tă haɗu da Rafin Masar, tă kuma ƙarasa a Bahar Rum.
6 Your western border will be the coastline of the Great Sea; this will be your boundary on the west.
“‘Iyakarku a yammanci, za tă kasance bakin Bahar Rum. Wannan ce za tă zama iyakarku a yamma.
7 Your northern border will run from the Great Sea directly to Mount Hor,
“‘Iyakarku a arewanci kuwa za tă tashi daga Bahar Rum zuwa Dutsen Hor,
8 and from Mount Hor to Lebo-hamath, then extend to Zedad,
za tă kuma tashi daga Dutsen Hor, zuwa Lebo Hamat. Sa’an nan tă miƙe zuwa Zedad,
9 continue to Ziphron, and end at Hazar-enan. This will be your boundary on the north.
tă ci gaba zuwa Zifron, sa’an nan tă ƙarasa a Hazar-Enan. Wannan ce za tă zama iyakarku a arewa.
10 And your eastern border will run straight from Hazar-enan to Shepham,
“‘Iyakarku a gabashi, za tă tashi daga Hazar-Enan zuwa Shefam.
11 then go down from Shepham to Riblah on the east side of Ain and continue along the slopes east of the Sea of Chinnereth.
Iyakar za tă gangara daga Shefam zuwa Ribla a gefen gabashin Ayin, sa’an nan tă ci gaba a gangaren gabashin Tekun Kinneret.
12 Then the border will go down along the Jordan and end at the Salt Sea. This will be your land, defined by its borders on all sides.”
Sa’an nan tă gangara ta Urdun, tă ƙarasa a Tekun Gishiri. “‘Wannan za tă zama ƙasarku, tare da iyakokinta a kowane gefe.’”
13 So Moses commanded the Israelites, “Apportion this land by lot as an inheritance. The LORD has commanded that it be given to the nine and a half tribes.
Sai Musa ya umarci Isra’ilawa ya ce, “Ku raba wannan ƙasa da za ku gāda ta hanyar jefa ƙuri’a. Ubangiji ya umarta cewa a ba da ita ga kabilu tara da rabi,
14 For the tribes of the Reubenites and Gadites, along with the half-tribe of Manasseh, have already received their inheritance.
saboda iyalan kabilar Ruben, kabilar Gad da rabin kabilar Manasse sun riga sun sami gādonsu.
15 These two and a half tribes have received their inheritance across the Jordan from Jericho, toward the sunrise.”
Waɗannan kabilu biyu da rabi, sun sami gādonsu a wancan hayin Urdun a gabashin Yeriko wajen fitowar rana.”
16 Then the LORD said to Moses,
Ubangiji ya ce wa Musa,
17 “These are the names of the men who are to assign the land as an inheritance for you: Eleazar the priest and Joshua son of Nun.
“Waɗannan su ne sunayen mutanen da za su raba muku ƙasar gādo. Eleyazar firist, da Yoshuwa ɗan Nun.
18 Appoint one leader from each tribe to distribute the land.
Ka kuma naɗa shugaba guda ɗaya daga kowace kabila domin yă taimaka a rabon ƙasar.
19 These are their names: Caleb son of Jephunneh from the tribe of Judah;
“Ga sunayensu. “Kaleb ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuda;
20 Shemuel son of Ammihud from the tribe of Simeon;
Shemuyel ɗan Ammihud, daga kabilar Simeyon
21 Elidad son of Chislon from the tribe of Benjamin;
Elidad ɗan Kislon, daga kabilar Benyamin;
22 Bukki son of Jogli, a leader from the tribe of Dan;
Bukki ɗan Yogli, shugaba daga kabilar Dan;
23 Hanniel son of Ephod, a leader from the tribe of Manasseh son of Joseph;
Hanniyel ɗan Efod, shugaba daga kabilar Manasse ɗan Yusuf;
24 Kemuel son of Shiphtan, a leader from the tribe of Ephraim;
Kemuwel ɗan Shiftan, shugaba daga kabilar Efraim ɗan Yusuf;
25 Eli-zaphan son of Parnach, a leader from the tribe of Zebulun;
Elizafan ɗan Farnak, shugaba daga kabilar Zebulun;
26 Paltiel son of Azzan, a leader from the tribe of Issachar;
Faltiyel ɗan Azzan, shugaba daga kabilar Issakar;
27 Ahihud son of Shelomi, a leader from the tribe of Asher;
Ahihud ɗan Shelomi, shugaba daga kabilar Asher;
28 and Pedahel son of Ammihud, a leader from the tribe of Naphtali.”
Fedahel ɗan Ammihud, shugaba daga kabilar Naftali.”
29 These are the ones whom the LORD commanded to apportion the inheritance to the Israelites in the land of Canaan.
Waɗannan su ne mutanen da Ubangiji ya umarta su raba gādo ga Isra’ilawa a ƙasar Kan’ana.