< Numbers 15 >

1 Then the LORD said to Moses,
Ubangiji ya ce wa Musa,
2 “Speak to the Israelites and tell them: After you enter the land that I am giving you as a home
“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Bayan kun shiga ƙasar da nake ba ku a matsayin gida,
3 and you present an offering made by fire to the LORD from the herd or flock to produce a pleasing aroma to the LORD—either a burnt offering or a sacrifice, for a special vow or freewill offering or appointed feast—
kuka yi hadayar da akan yi da wuta ga Ubangiji, daga cikin shanu, ko tumaki, abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, ko hadaya ta ƙonawa, ko hadayu don alkawura na musamman, ko hadayar yardar rai, ko kuma hadaya ta biki,
4 then the one presenting his offering to the LORD shall also present a grain offering of a tenth of an ephah of fine flour mixed with a quarter hin of olive oil.
sai shi wanda ya kawo hadayar yă miƙa wa Ubangiji hadaya ta gari mai laushi mai kyau, kashi ɗaya bisa goma na efa wanda aka kwaɓa da kwalaba ɗaya na mai.
5 With the burnt offering or sacrifice of each lamb, you are to prepare a quarter hin of wine as a drink offering.
Da kowane ɗan rago don hadaya ta ƙonawa, a shirya kwalaba ɗaya na ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha.
6 With a ram you are to prepare a grain offering of two-tenths of an ephah of fine flour mixed with a third of a hin of olive oil,
“‘In da rago ne za a miƙa, to, sai a shirya hadaya ta gari mai laushi, garin yă zama kashi biyu bisa goma na efa. A kwaɓa shi da kashi ɗaya bisa uku na garwan mai,
7 and a third of a hin of wine as a drink offering, a pleasing aroma to the LORD.
da kashi ɗaya bisa uku na garwan ruwan inabi, a matsayin hadaya ta sha. A miƙa ta abin ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.
8 When you prepare a young bull as a burnt offering or sacrifice to fulfill a vow or as a peace offering to the LORD,
“‘Sa’ad da kuka shirya rago don hadaya ta ƙonawa saboda alkawari na musamman, ko hadaya ta salama ga Ubangiji,
9 present with the bull a grain offering of three-tenths of an ephah of fine flour mixed with half a hin of olive oil.
sai ku kawo hadaya ta gari tare da bijimi, kashi ɗaya bisa uku na gari mai laushi kwaɓaɓɓe da rabin garwan mai.
10 Also present half a hin of wine as a drink offering. It is an offering made by fire, a pleasing aroma to the LORD.
A kuma kawo rabin garwan ruwan inabi na hadaya ta sha. Za tă zama hadayar da aka yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
11 This is to be done for each bull, ram, lamb, or goat.
Haka za a yi da kowane bijimi, ko rago, ko ɗan rago, ko bunsuru.
12 This is how you must prepare each one, no matter how many.
Haka za a yi da kowannensu bisa ga abin da aka shirya.
13 Everyone who is native-born shall prepare these things in this way when he presents an offering made by fire as a pleasing aroma to the LORD.
“‘Duk wanda yake ɗan ƙasa, ta haka ne dole zai aikata waɗannan abubuwa sa’ad da ya kawo hadaya da akan yi da wuta mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
14 And for the generations to come, if a foreigner residing with you or someone else among you wants to prepare an offering made by fire as a pleasing aroma to the LORD, he is to do exactly as you do.
Idan baƙon da yake baƙunci a cikinku, ko kowane ne da yake tare da ku a dukan zamananku, yana so yă ba da hadayar da akan yi da wuta don a yi ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji, dole yă yi kamar yadda kuke yi.
15 The assembly is to have the same statute both for you and for the foreign resident; it is a permanent statute for the generations to come. You and the foreigner shall be the same before the LORD.
Ƙa’ida ɗaya ce ga jama’a da kuma baƙin da suke zama a cikinku, wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a dukan tsararraki masu zuwa. Da ku, da baƙi, za ku zama ɗaya a gaban Ubangiji.
16 The same law and the same ordinance will apply both to you and to the foreigner residing with you.”
Doka ɗaya da ƙa’ida ɗaya za a yi aiki da ita a kan ku da kuma baƙin da suke zama a cikinku.’”
17 Then the LORD said to Moses,
Ubangiji ya ce wa Musa,
18 “Speak to the Israelites and tell them: When you enter the land to which I am bringing you
“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar da ina kai ku,
19 and you eat the food of the land, you shall lift up an offering to the LORD.
kuka ci abincin ƙasar, ku miƙa wani sashe na amfanin ƙasar a matsayin hadaya ga Ubangiji.
20 From the first of your dough, you are to lift up a cake as a contribution; offer it just like an offering from the threshing floor.
Ku kawo waina daga nunan fari na ɓarzajjen hatsinku, ku kuma miƙa shi a matsayin hadaya daga masussuka.
21 Throughout your generations, you are to give the LORD an offering from the first of your dough.
A duk tsararraki masu zuwa, za ku miƙa wannan hadaya daga nunan fari na ɓarzajjen hatsinku ga Ubangiji.
22 Now if you stray unintentionally and do not obey all these commandments that the LORD has spoken to Moses—
“‘To, in ku a matsayin jama’a, da gangan kuka ƙi kiyaye waɗannan ƙa’idodi da Ubangiji ya ba wa Musa ba,
23 all that the LORD has commanded you through Moses from the day the LORD gave them and continuing through the generations to come—
ko wani daga cikin umarnan da Ubangiji ya ba ku ta wurinsa, daga ranar da Ubangiji ya ba da su, har zuwa tsararraki masu zuwa,
24 and if it was done unintentionally without the knowledge of the congregation, then the whole congregation is to prepare one young bull as a burnt offering, a pleasing aroma to the LORD, with its grain offering and drink offering according to the regulation, and one male goat as a sin offering.
in kuwa aka yi haka ba da gangan ba, kuma da rashin sani, sai duk jama’a su miƙa ɗan bijimi don hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, tare da ƙayyadadden hadaya ta gari, da hadaya ta sha, da kuma bunsuru na hadaya don zunubi.
25 The priest is to make atonement for the whole congregation of Israel, so that they may be forgiven; for the sin was unintentional and they have brought to the LORD an offering made by fire and a sin offering, presented before the LORD for their unintentional sin.
Firist kuwa zai yi kafara domin dukan jama’ar Isra’ilawa, za a kuma gafarta musu, gama ba da gangan ba ne suka aikata, kuma sun kawo wa Ubangiji hadayar da akan yi da wuta da kuma hadaya don zunubi saboda laifinsu.
26 Then the whole congregation of Israel and the foreigners residing among them will be forgiven, since it happened to all the people unintentionally.
Za a gafarta wa dukan jama’ar Isra’ilawa, da baƙin da suke zama a cikinsu, gama duk laifin da aka yi da rashin sani, yakan shafi dukan mutane.
27 Also, if one person sins unintentionally, he is to present a year-old female goat as a sin offering.
“‘Amma in mutum ɗaya ne kaɗai ya yi laifi ba da gangan ba, dole yă kawo akuya domin hadaya don zunubi.
28 And the priest shall make atonement before the LORD on behalf of the person who erred by sinning unintentionally; and when atonement has been made for him, he will be forgiven.
Firist zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin nan da ya aikata laifi ba da gangan ba, in kuwa an yi kafara saboda shi, za a gafarta masa.
29 You shall have the same law for the one who acts in error, whether he is a native-born Israelite or a foreigner residing among you.
Ƙa’ida dai za tă zama ɗaya ga duk wanda ya yi laifi ba da gangan ba, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙon da yake zama a cikinku.
30 But the person who sins defiantly, whether a native or foreigner, blasphemes the LORD. That person shall be cut off from among his people.
“‘Amma duk wanda ya yi zunubi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko baƙo, ya saɓi Ubangiji, dole a ware wannan mutum daga mutanensa,
31 He shall certainly be cut off, because he has despised the word of the LORD and broken His commandment; his guilt remains on him.”
gama ya rena maganar Ubangiji, ya kuma karya umarninsa. Tabbatacce za a kashe wannan mutum, alhakinsa laifinsa kuwa yana wuyansa.’”
32 While the Israelites were in the wilderness, a man was found gathering wood on the Sabbath day.
Yayinda Isra’ilawa suke ciki hamada, sai aka sami wani mutum yana tattara itace a ranar Asabbaci.
33 Those who found the man gathering wood brought him to Moses, Aaron, and the whole congregation,
Waɗanda suka gan shi, suka kawo shi wurin Musa da Haruna da dukan taro,
34 and because it had not been declared what should be done to him, they placed him in custody.
sai suka sa shi a gidan waƙafi don ba su riga sun san abin da za a yi da shi ba tukuna.
35 And the LORD said to Moses, “The man must surely be put to death. The whole congregation is to stone him outside the camp.”
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Dole mutumin yă mutu. Dole dukan taron su jajjefe shi a bayan sansani.”
36 So the whole congregation took the man outside the camp and stoned him to death, as the LORD had commanded Moses.
Saboda haka taron suka ɗauke shi zuwa bayan sansani, suka kuma jajjefe shi har ya mutu, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
37 Later, the LORD said to Moses,
Ubangiji ya ce wa Musa,
38 “Speak to the Israelites and tell them that throughout the generations to come they are to make for themselves tassels for the corners of their garments, with a blue cord on each tassel.
“Ka yi magana da Isra’ilawa, ka ce musu, ‘A dukan tsararraki masu zuwa, za ku sa tuntaye a gefen rigunarku, su sa zare mai ruwan shuɗi a bisan kowane tuntu.
39 These will serve as tassels for you to look at, so that you may remember all the commandments of the LORD, that you may obey them and not prostitute yourselves by following your own heart and your own eyes.
Tuntayen za su zama muku abin dubawa don ku riƙa tunawa da dukan umarnan Ubangiji, don kada ku bi son zuciyarku, da sha’awar idanunku yadda kuka taɓa yi.
40 Then you will remember and obey all My commandments, and you will be holy to your God.
Sa’an nan za ku riƙa tuna, ku kuma aikata dukan umarnaina ku zama tsarkaka ga Allahnku.
41 I am the LORD your God who brought you out of the land of Egypt to be your God. I am the LORD your God.”
Ni ne Ubangiji Allahnku, da ya fitar da ku daga Masar, don in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.’”

< Numbers 15 >