< Micah 4 >

1 In the last days the mountain of the house of the LORD will be established as the chief of the mountains; it will be raised above the hills, and the peoples will stream to it.
A kwanakin ƙarshe za a kafa dutsen haikalin Ubangiji yă zama babba a cikin duwatsu. Za a ɗaga shi sama da tuddai, mutane kuma za su riƙa ɗunguma zuwa gare shi.
2 And many nations will come and say: “Come, let us go up to the mountain of the LORD, to the house of the God of Jacob. He will teach us His ways, so that we may walk in His paths.” For the law will go forth from Zion and the word of the LORD from Jerusalem.
Al’ummai da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, don mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Doka za tă fita daga Sihiyona, maganar Ubangiji kuma daga Urushalima.
3 Then He will judge between many peoples and arbitrate for strong nations far and wide. Then they will beat their swords into plowshares and their spears into pruning hooks. Nation will no longer take up the sword against nation, nor will they train anymore for war.
Zai shari’anta tsakanin mutane yă kuma sulhunta tsakanin manyan al’ummai nesa da kuma kusa. Har su mai da takubansu su zama garemani, māsunsu kuma su zama wuƙaƙen askin itace. Al’umma ba za tă ɗauki takobi gāba da wata al’umma ba, ko a yi horarwa don yaƙi.
4 And each man will sit under his own vine and under his own fig tree, with no one to frighten him. For the mouth of the LORD of Hosts has spoken.
Kowa zai zauna a tushen kuringar inabinsa da tushen ɓaurensa, kuma ba wanda zai tsoratar da su, gama Ubangiji Maɗaukaki ne ya faɗa.
5 Though each of the peoples may walk in the name of his god, yet we will walk in the name of the LORD our God forever and ever.
Dukan al’ummai za su iya tafiya a cikin sunan allolinsu; mu dai za mu yi tafiya a cikin sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.
6 “On that day,” declares the LORD, “I will gather the lame; I will assemble the outcast, even those whom I have afflicted.
“A wannan rana,” in ji Ubangiji, “zan tattara guragu; zan kuma tara masu zaman bauta, da waɗanda na sa suka damu.
7 And I will make the lame into a remnant, and the outcast into a strong nation. Then the LORD will rule over them in Mount Zion from that day and forever.
Zan mai da guragu su zama raguwa, waɗanda aka kora, su zama al’umma mai ƙarfi. Ubangiji zai yi mulkinsu a Dutsen Sihiyona daga wannan rana da kuma har abada.
8 And you, O watchtower of the flock, O stronghold of the Daughter of Zion— the former dominion will be restored to you; sovereignty will come to the Daughter of Jerusalem.”
Game da ke, ya hasumiyar tsaron garke, Ya mafaka Diyar Sihiyona, za a maido miki da mulkinki na dā, sarauta kuma za tă zo wa Diyar Urushalima.”
9 Why do you now cry aloud? Is there no king among you? Has your counselor perished so that anguish grips you like a woman in labor?
Don me yanzu kike kuka da ƙarfi, ba ki da sarki ne? Masu shawararki sun hallaka ne, da zafi ya cika ki kamar mace mai naƙuda?
10 Writhe in agony, O Daughter of Zion, like a woman in labor. For now you will leave the city and camp in the open fields. You will go to Babylon; there you will be rescued; there the LORD will redeem you from the hand of your enemies!
Ki yi birgima cikin zafin azaba, ya Diyar Sihiyona, kamar macen da take naƙuda, don yanzu dole ki bar birni ki kafa sansani a filin Allah. Za ki tafi Babilon; a can za a kuɓutar da ki. A can ne Ubangiji zai fanshe ki daga hannun maƙiyanki.
11 But now many nations have assembled against you, saying, “Let her be defiled, and let us feast our eyes on Zion.”
Amma yanzu al’ummai da yawa suna gāba da ke. Suna cewa, “Bari a ƙazantar da ita, bari mu zuba wa Sihiyona ido.”
12 But they do not know the thoughts of the LORD or understand His plan, for He has gathered them like sheaves to the threshing floor.
Amma ba su san tunanin Ubangiji ba; ba su fahimci shirinsa ba, shi da ya tattara su kamar dammuna a masussuka.
13 Rise and thresh, O Daughter of Zion, for I will give you horns of iron and hooves of bronze to break to pieces many peoples. Then you will devote their gain to the LORD, their wealth to the Lord of all the earth.
“Ki tashi ki yi sussuka, ya Diyar Sihiyona, gama zan ba ki ƙahonin ƙarfe; zan ba ki kofatan tagulla domin ki ragargaje al’ummai masu yawa.” Za ki ba Ubangiji dukan dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba, wadatarsu kuma ga Ubangiji dukan duniya.

< Micah 4 >