< Joshua 14 >

1 Now these are the portions that the Israelites inherited in the land of Canaan, as distributed by Eleazar the priest, Joshua son of Nun, and the heads of the families of the tribes of Israel.
Ga wuraren da Isra’ilawa suka sami gādo a ƙasar Kan’ana waɗanda Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun da kuma shugabannin iyalai kabila-kabila na Isra’ila suka raba musu.
2 Their inheritance was assigned by lot for the nine and a half tribes, as the LORD had commanded through Moses.
Ta wurin yin ƙuri’a aka raba wa kabilan nan tara da rabi, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.
3 For Moses had given the inheritance east of the Jordan to the other two and a half tribes. But he granted no inheritance among them to the Levites.
Musa ya ba wa kabilan biyu da rabin nan gādonsu gabashin Urdun, amma bai ba wa Lawiyawa gādo a cikin sauran ba,
4 The descendants of Joseph became two tribes, Manasseh and Ephraim. And no portion of the land was given to the Levites, except for cities in which to live, along with pasturelands for their flocks and herds.
gama’ya’yan Yusuf sun zama kabilu biyu, Manasse da Efraim. Ba a ba Lawiyawa gādon ba sai dai garuruwan da aka ba su su zauna a ciki, da wurin kiwo mai kyau domin dabbobinsu.
5 So the Israelites did as the LORD had commanded Moses, and they divided the land.
Haka Isra’ilawa suka raba ƙasar, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
6 Then the sons of Judah approached Joshua at Gilgal, and Caleb son of Jephunneh the Kenizzite said to him, “You know what the LORD said to Moses the man of God at Kadesh-barnea about you and me.
Mutanen Yahuda kuma suka je wurin Yoshuwa a Gilgal, sai Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze ya ce wa Yoshuwa, “Ka san abin da Ubangiji ya gaya wa Musa, mutumin Allah a Kadesh Barneya game da kai da ni.
7 I was forty years old when Moses the servant of the LORD sent me from Kadesh-barnea to spy out the land, and I brought back to him an honest report.
Ina da shekara arba’in lokacin da Musa bawan Ubangiji ya aike ni zuwa Kadesh Barneya in leƙi asirin ƙasar. Na kuwa kawo masa rahoto daidai yadda na ga ƙasar,
8 Although my brothers who went with me made the hearts of the people melt with fear, I remained loyal to the LORD my God.
amma’yan’uwana waɗanda muka je tare su suka ba da rahoton da ya sa zukatan mutane suka narke don tsoro. Ni kam na bi Ubangiji Allah da dukan zuciyata.
9 On that day Moses swore to me, saying, ‘Surely the land on which you have set foot will be an inheritance to you and your children forever, because you have wholly followed the LORD my God.’
Saboda haka a ranan nan Musa ya rantse mini cewa, ‘Ƙasar da ka taka za tă zama ƙasarka ta gādo kai da’ya’yanka har abada, domin ka bi Ubangiji Allahna da dukan zuciyarka.’
10 Now behold, as the LORD promised, He has kept me alive these forty-five years since He spoke this word to Moses, while Israel wandered in the wilderness. So here I am today, eighty-five years old,
“Ga shi, kamar yadda Ubangiji ya yi alkawari, ya bar ni da rai har na ƙara shekaru arba’in da biyar tun daga lokacin da ya gaya wa Musa wannan, a lokacin da Isra’ilawa suke yawo a cikin jeji. Ga ni nan yau shekaruna tamanin da biyar!
11 still as strong today as I was the day Moses sent me out. As my strength was then, so it is now for war, for going out, and for coming in.
Ina nan da ƙarfina kamar yadda nake da ƙarfi a lokacin da Musa ya aike ni; zan iya fita zuwa yaƙi da ƙwazo yanzu kamar yadda nake zuwa a dā.
12 Now therefore give me this hill country that the LORD promised me on that day, for you yourself heard then that the Anakim were there, with great and fortified cities. Perhaps with the LORD’s help I will drive them out, as the LORD has spoken.”
Yanzu sai ka ba ni wannan ƙasar da take kan tudu wadda Ubangiji ya yi alkawari zai ba ni a ranan nan. Kai ma ka ji a lokacin, yadda Anakawa suke a can, biranensu manya ne kuma sun kewaye su sosai, amma na sani Ubangiji zai taimake ni, zan kore su kamar yadda ya faɗa.”
13 Then Joshua blessed Caleb son of Jephunneh and gave him Hebron as his inheritance.
Sai Yoshuwa ya sa wa Kaleb ɗan Yefunne albarka, ya ba shi Hebron.
14 Therefore Hebron belongs to Caleb son of Jephunneh the Kenizzite as an inheritance to this day, because he wholly followed the LORD, the God of Israel.
Saboda haka Hebron ta zama ƙasar Kaleb ɗan Yefunne Bakenizze tun daga lokacin nan, domin ya bi Ubangiji, Allah na Isra’ila da dukan zuciyarsa.
15 (Hebron used to be called Kiriath-arba, after Arba, the greatest man among the Anakim.) Then the land had rest from war.
(Dā a kan kira wannan Hebron, Kiriyat Arba. Wannan Arba kuwa shi ne wani katon mutum a cikin Anakawa.) Sa’an nan ƙasar ta huta daga yaƙi.

< Joshua 14 >