< John 7 >
1 After this, Jesus traveled throughout Galilee. He did not want to travel in Judea, because the Jews there were trying to kill Him.
Bayan wadannan abubuwa Yesu ya zagaya cikin Gallili, saboda baya so ya shiga cikin Yahudiya domin Yahudawa suna shirin su kashe shi.
2 However, the Jewish Feast of Tabernacles was near.
To Idin Bukkoki na Yahudawa ya kusa.
3 So Jesus’ brothers said to Him, “Leave here and go to Judea, so that Your disciples there may see the works You are doing.
Sai 'yan'uwansa suka ce da shi, “ka tashi ka tafi Yahudiya, domin almajiranka su ga ayyukan da kake yi su ma.
4 For no one who wants to be known publicly acts in secret. Since You are doing these things, show Yourself to the world.”
Ba wanda ya ke yin wani abu a boye idan dai yana so kowa da kowa ya san shi. Da yake ka na yin wadannan abubuwa sai ka nuna kan ka a fili ga duniya.
5 For even His own brothers did not believe in Him.
Domin ko 'yan'uwansa ma basu bada gaskiya gare shi ba.
6 Therefore Jesus told them, “Although your time is always at hand, My time has not yet come.
Yesu ya ce dasu, “lokaci na bai yi ba tukuna, amma ku koyaushe lokacin ku ne.
7 The world cannot hate you, but it hates Me, because I testify that its works are evil.
Duniya baza ta iya kin ku ba, amma ta ki ni saboda ina fadin cewa ayyukanta ba su da kyau.
8 Go up to the feast on your own. I am not going up to this feast, because My time has not yet come.”
Ku ku je wurin idin, ni ba zan je wurin idin ba domin lokacina bai yi ba tukuna.
9 Having said this, Jesus remained in Galilee.
Bayan da ya gaya masu wadannan abubuwa, ya tsaya a cikin Gallili.
10 But after His brothers had gone up to the feast, He also went—not publicly, but in secret.
Amma bayan da 'yan'uwansa su ka tafi wurin idin shi ma ya tafi, amma a asirce ba a fili ba.
11 So the Jews were looking for Him at the feast and asking, “Where is He?”
Saboda Yahudawa suna neman sa a wurin idin, su na cewa “Ina yake?”
12 Many in the crowds were whispering about Him. Some said, “He is a good man.” But others replied, “No, He deceives the people.”
Akwai maganganu dayawa a kansa cikin taron. Wadansu suna cewa, “shi mutumin kirki ne.” Wadansu kuma suna cewa,”A'a yana karkatar da hankalin jama'a.”
13 Yet no one would speak publicly about Him for fear of the Jews.
Amma duk da haka ba wanda ya yi magana a fili a kansa saboda suna jin tsoron Yahudawa.
14 About halfway through the feast, Jesus went up to the temple courts and began to teach.
Sa'anda aka kai rabin idin, sai Yesu ya shiga cikin haikali ya fara koyarwa.
15 The Jews were amazed and asked, “How did this man attain such learning without having studied?”
Yahudawa suna mamaki suna cewa,”Yaya aka yi wannan mutum ya sami ilimi dayawa haka? Shi kuwa bai je makaranta ba.”
16 “My teaching is not My own,” Jesus replied. “It comes from Him who sent Me.
Yesu ya ba su amsa ya ce,”Koyarwata ba tawa ba ce, amma ta wanda ya aiko ni ce.”
17 If anyone desires to do His will, he will know whether My teaching is from God or whether I speak on My own.
Idan wani yana so ya yi nufinsa, za ya gane koyarwannan ko daga wurin Allah ta zo, ko ko tawa ce ta kaina.
18 He who speaks on his own authority seeks his own glory, but He who seeks the glory of the One who sent Him is a man of truth; in Him there is no falsehood.
Ko wanene yake maganar kansa, yana neman darajar kansa kenan, amma ko wanene ya nemi darajar wanda ya aiko ni, wannan mutum mai gaskiya ne, babu rashin adalci a cikin sa.
19 Has not Moses given you the law? Yet not one of you keeps it. Why are you trying to kill Me?”
Ba Musa ya baku dokoki ba? Amma duk da haka ba mai aikata dokokin. Me yasa ku ke so ku kashe ni?
20 “You have a demon,” the crowd replied. “Who is trying to kill You?”
Taron suka ba shi amsa, “Ka na da aljani. Wanene yake so ya kashe ka?”
21 Jesus answered them, “I did one miracle, and you are all amazed.
Yesu ya amsa ya ce masu, “Nayi aiki daya, dukan ku kuna mamaki da shi.
22 But because Moses gave you circumcision, you circumcise a boy on the Sabbath (not that it is from Moses, but from the patriarchs.)
Musa ya baku kaciya, (ba kuwa daga Musa take ba, amma daga kakannin kakanni ta ke), kuma a ranar Asabar kukan yi wa mutum kaciya.
23 If a boy can be circumcised on the Sabbath so that the law of Moses will not be broken, why are you angry with Me for making the whole man well on the Sabbath?
Idan mutum ya karbi kaciya ranar Asabar, domin kada a karya dokar Musa, don me kuka ji haushi na saboda na mai da mutum lafiyayye sarai ranar Asabar?
24 Stop judging by outward appearances, and start judging justly.”
Kada ku yi shari'a ta ganin ido, amma ku yi shari'a mai adalci.”
25 Then some of the people of Jerusalem began to say, “Isn’t this the man they are trying to kill?
Wadansun su daga Urushalima suka ce, “wannan ba shine wannan da suke nema su kashe ba?”
26 Yet here He is, speaking publicly, and they are not saying anything to Him. Have the rulers truly recognized that this is the Christ?
Kuma duba, yana magana a fili, sannan ba wanda ya ce da shi komai. Ba zai yiwu ba mahukunta su sani cewa wannan Kristi ne, ko ba haka ba?
27 But we know where this man is from. When the Christ comes, no one will know where He is from.”
da haka, mun san inda wannan mutum ya fito. Amma sa'anda Kristi za ya zo, ba wanda zai san inda ya fito.”
28 Then Jesus, still teaching in the temple courts, cried out, “You know Me, and you know where I am from. I have not come of My own accord, but He who sent Me is true. You do not know Him,
Yesu yayi magana da karfi a haikali, yana koyarwa ya na cewa, “Kun san ni kuma kun san inda na fito. Ban zo domin kaina ba, amma wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, ku kuwa baku san shi ba.
29 but I know Him, because I am from Him and He sent Me.”
Ni na san shi domin daga wurinsa na fito, kuma shine ya aiko ni.”
30 So they tried to seize Him, but no one laid a hand on Him, because His hour had not yet come.
Suna kokari su kama shi, amma ba wanda ya iya sa masa hannu domin sa'arsa ba ta yi ba tukuna.
31 Many in the crowd, however, believed in Him and said, “When the Christ comes, will He perform more signs than this man?”
Duk da haka wadansu dayawa a cikin taron suka bada gaskiya gare shi suka ce,”Sa'anda Kristi ya zo, zai yi alamu fiye da wadanda wannan mutum ya yi?”
32 When the Pharisees heard the crowd whispering these things about Jesus, they and the chief priests sent officers to arrest Him.
Farisawa suka ji tattarmukan suna yin rada a kan wadannan abubuwa game da Yesu, Sai manyan malamai da Farisawa su ka aika jami'ai su kama shi.
33 So Jesus said, “I am with you only a little while longer, and then I am going to the One who sent Me.
Sa'annan Yesu yace ma su,” jimawa kadan ina tare ku, sa'annan in tafi wurin wanda ya aiko ni.
34 You will look for Me, but you will not find Me; and where I am, you cannot come.”
Za ku neme ni ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba.”
35 At this, the Jews said to one another, “Where does He intend to go that we will not find Him? Will He go where the Jews are dispersed among the Greeks, and teach the Greeks?
Yahudawa fa su ka cewa junan su, “Ina wannan mutum zai je inda ba za mu iya samun sa ba? Ko za ya tafi wurin Helinawa na warwatsuwa ya koyawa Helinawa?
36 What does He mean by saying, ‘You will look for Me, but you will not find Me,’ and, ‘Where I am, you cannot come’?”
Wace kalma ya ke fadi haka, 'za ku neme ni amma ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba'?”
37 On the last and greatest day of the feast, Jesus stood up and called out in a loud voice, “If anyone is thirsty, let him come to Me and drink.
To a rana ta karshe, babbar rana ta idin, Yesu ya mike ya yi magana da karfi cewa, “Idan kowa yana jin kishi, ya zo wuri na ya sha.
38 Whoever believes in Me, as the Scripture has said: ‘Streams of living water will flow from within him.’”
Shi wanda ya bada gaskiya gare ni kamar yadda nassi ya fadi, daga cikin sa rafukan ruwa na rai za su bulbulo.”
39 He was speaking about the Spirit, whom those who believed in Him were later to receive. For the Spirit had not yet been given, because Jesus had not yet been glorified.
Amma ya fadi haka a kan Ruhu, wanda wadanda suka bada gaskiya gare shi za su karba; ba a ba da Ruhun ba tukuna, saboda ba a rigaya an daukaka Yesu ba.
40 On hearing these words, some of the people said, “This is truly the Prophet.”
Wadansu a cikin taron, sa'anda suka ji wadannan kalmomi, suka ce, “Wannan lallai annabi ne.”
41 Others declared, “This is the Christ.” But still others asked, “How can the Christ come from Galilee?
Wadansu suka ce, “Wannan Almasihu ne.” Amma wadansu suka ce, “Almasihu zai fito daga Gallili ne?
42 Doesn’t the Scripture say that the Christ will come from the line of David and from Bethlehem, the village where David lived?”
Ba nassi ya ce Almasihu zai fito daga cikin dangin Dauda daga Baitalami ba, daga kauyen da Dauda ya fito?”
43 So there was division in the crowd because of Jesus.
Sai aka sami rabuwa a cikin taron saboda shi.
44 Some of them wanted to seize Him, but no one laid a hand on Him.
Da wadansun su sun kama shi, amma ba wanda ya sa masa hannu.
45 Then the officers returned to the chief priests and Pharisees, who asked them, “Why didn’t you bring Him in?”
Sa'annan jami'an suka dawo wurin manyan Fristoci da Farisawa, wadanda suka ce,” me yasa ba ku kawo shi ba?”
46 “Never has anyone spoken like this man!” the officers answered.
Jami'an su ka amsa, “Ba mutumin da ya taba yin magana kamar haka.”
47 “Have you also been deceived?” replied the Pharisees.
Farisawa suka amsa masu, “kuma an karkatar da ku?
48 “Have any of the rulers or Pharisees believed in Him?
Ko wani daga cikin mahukunta ya bada gaskiya gare shi, ko kuwa daga cikin Farisawa?
49 But this crowd that does not know the law, they are under a curse.”
Amma wannan taro da basu san shari'a ba, la'anannu ne.”
50 Nicodemus, who had gone to Jesus earlier and who himself was one of them, asked,
Nikodimus ya ce masu, (shi wanda ya zo wurin Yesu da, daya daga cikin Farisawa),
51 “Does our law convict a man without first hearing from him to determine what he has done?”
“Ko shari'armu bata hana hukunta mutum ba, sai ta ji daga gare shi ta kuma san abin da ya aikata ba?”
52 “Aren’t you also from Galilee?” they replied. “Look into it, and you will see that no prophet comes out of Galilee.”
Suka amsa masa suka ce,”kai ma daga Galili ka fito? Ka yi bincike ka gani ba annanbin da zai fito daga Galili.”
53 Then each went to his own home.
Daga nan sai kowa ya tafi gidansa.