< James 2 >
1 My brothers, as you hold out your faith in our glorious Lord Jesus Christ, do not show favoritism.
’Yan’uwana, a matsayinmu cikin Ubangiji Yesu Kiristi maɗaukaki, kada ku nuna bambanci.
2 Suppose a man comes into your meeting wearing a gold ring and fine clothes, and a poor man in shabby clothes also comes in.
A ce wani ya shigo cikin taronku saye da zoben zinariya da riguna masu tsada, wani matalauci kuma saye da tsummoki shi ma ya shigo,
3 If you lavish attention on the man in fine clothes and say, “Here is a seat of honor,” but say to the poor man, “You must stand” or “Sit at my feet,”
in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,”
4 have you not discriminated among yourselves and become judges with evil thoughts?
ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ke nan ba, kuka kuma zama alƙalai masu mugayen tunani?
5 Listen, my beloved brothers: Has not God chosen the poor of this world to be rich in faith and to inherit the kingdom He promised those who love Him?
Ku saurara,’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?
6 But you have dishonored the poor. Is it not the rich who oppress you and drag you into court?
Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu?
7 Are they not the ones who blaspheme the noble name by which you have been called?
Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba?
8 If you really fulfill the royal law stated in Scripture, “Love your neighbor as yourself,” you are doing well.
In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.
9 But if you show favoritism, you sin and are convicted by the law as transgressors.
Amma in kuka nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan shari’a kuma ta same ku da laifi a matsayin masu karya doka.
10 Whoever keeps the whole law but stumbles at just one point is guilty of breaking all of it.
Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan.
11 For He who said, “Do not commit adultery,” also said, “Do not murder.” If you do not commit adultery, but do commit murder, you have become a lawbreaker.
Gama shi da ya ce, “Kada ka yi zina,” shi ne kuma ya ce, “Kada ka yi kisankai.” In kuwa ba ka zina amma kana kisankai, ka zama mai karya doka ke nan.
12 Speak and act as those who are going to be judged by the law that gives freedom.
Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da’yanci,
13 For judgment without mercy will be shown to anyone who has not been merciful. Mercy triumphs over judgment.
gama za a yi wa duk wanda bai nuna jinƙai ba hukunci babu jinƙai. Jinƙai yakan yi nasara a kan hukunci!
14 What good is it, my brothers, if someone claims to have faith, but has no deeds? Can such faith save him?
Wanda amfani ne,’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa?
15 Suppose a brother or sister is without clothes and daily food.
A ce wani ɗan’uwa ko’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini,
16 If one of you tells him, “Go in peace; stay warm and well fed,” but does not provide for his physical needs, what good is that?
sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani?
17 So too, faith by itself, if it does not result in action, is dead.
Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce.
18 But someone will say, “You have faith and I have deeds.” Show me your faith without deeds, and I will show you my faith by my deeds.
Amma wani zai ce, “Kai kana da bangaskiya; ni kuma ina da ayyuka.” Ka nuna mini bangaskiyarka ba tare da ayyuka ba, ni kuma zan nuna maka bangaskiyata ta wurin abin da nake yi.
19 You believe that God is one. Good for you! Even the demons believe that—and shudder.
Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan, har da rawan jiki.
20 O foolish man, do you want evidence that faith without deeds is worthless?
Kai wawa, kana son tabbaci cewa bangaskiya marar ayyuka banza ce?
21 Was not our father Abraham justified by what he did when he offered his son Isaac on the altar?
Ashe, ba a mai da kakanmu Ibrahim mai adalci saboda abin da ya yi ba ne sa’ad da ya miƙa ɗansa Ishaku a bisa bagade?
22 You see that his faith was working with his actions, and his faith was perfected by what he did.
Ai, ka gani cewa bangaskiyarsa da ayyukansa sun yi aiki tare, bangaskiyarsa kuma ta zama cikakkiya ta wurin abin da ya yi.
23 And the Scripture was fulfilled that says, “Abraham believed God, and it was credited to him as righteousness,” and he was called a friend of God.
Aka kuma cika nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi,” aka kuma ce da shi abokin Allah.
24 As you can see, a man is justified by his deeds and not by faith alone.
Kun ga cewa ashe mutum zai sami kuɓuta ta wurin abin da ya yi ne ba ta wurin bangaskiya kaɗai ba.
25 In the same way, was not even Rahab the prostitute justified by her actions when she welcomed the spies and sent them off on another route?
Ta haka kuma ashe, Rahab karuwan nan ba a ɗauke ta mai adalci ce saboda abin da ta yi ba ne sa’ad da ta ba wa’yan leƙen asirin nan masauƙi ta kuma sallame su suka tafi ta wata hanya dabam?
26 As the body without the spirit is dead, so faith without deeds is dead.
Kamar yadda jikin da babu ruhu matacce ne, haka ma bangaskiyar da babu ayyuka matacciya ce.