< Isaiah 56 >

1 This is what the LORD says: “Maintain justice and do what is right, for My salvation is coming soon, and My righteousness will be revealed.
Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku riƙe gaskiya ku yi abin da yake daidai, gama cetona yana kusa za a kuma bayyana adalcina nan da nan.
2 Blessed is the man who does this, and the son of man who holds it fast, who keeps the Sabbath without profaning it and keeps his hand from doing any evil.”
Mai albarka ne mutumin da ya aikata wannan, mutumin da ya riƙe kam yana kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba, yana kuma kiyaye kansa daga yin mugun abu.”
3 Let no foreigner who has joined himself to the LORD say, “The LORD will utterly exclude me from His people.” And let the eunuch not say, “I am but a dry tree.”
Kada baƙon da ya miƙa kansa ga Ubangiji ya ce, “Ai Ubangiji zai ware ni daga mutanensa.” Kada kuma wani bābā ya yi gunaguni cewa, “Ni busasshen itace ne kawai.”
4 For this is what the LORD says: “To the eunuchs who keep My Sabbaths, who choose what pleases Me and hold fast to My covenant—
Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Wa bābānnin da suna kiyaye Asabbatai, waɗanda suka zaɓi yin abin da ya gamshe ni suna kuma riƙe da alkawarina kankan,
5 I will give them, in My house and within My walls, a memorial and a name better than that of sons and daughters. I will give them an everlasting name that will not be cut off.
a gare su cikin haikalina da kuma bangayensa zan ba da matuni da kuma suna mafi kyau fiye da’ya’ya maza da kuma’ya’ya mata; zan ba su madawwamin sunan da ba za a raba su da shi ba.
6 And the foreigners who join themselves to the LORD to minister to Him, to love the name of the LORD, and to be His servants— all who keep the Sabbath without profaning it and who hold fast to My covenant—
Baƙin da suka miƙa kansu ga Ubangiji don su bauta masa, su kuma ƙaunaci sunan Ubangiji, waɗanda kuma suke yin masa sujada, duk waɗanda suka kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba suka kuma riƙe alkawarina kankan,
7 I will bring them to My holy mountain and make them joyful in My house of prayer. Their burnt offerings and sacrifices will be accepted on My altar, for My house will be called a house of prayer for all the nations.”
waɗannan ne zan kai tsattsarkan dutsena in sa su yi farin ciki a gidana na addu’a. Hadayunsu na ƙonawa da sadakokinsu za su zama abin karɓa a bagadena; gama za a ce da gidana gidan addu’a domin dukan al’ummai.”
8 Thus declares the Lord GOD, who gathers the dispersed of Israel: “I will gather to them still others besides those already gathered.”
Ubangiji Mai Iko Duka ya furta cewa, zai tattara korarru na Isra’ila, “Zan ƙara tattaro waɗansu bayan waɗanda na riga na tattara.”
9 Come, all you beasts of the field; eat greedily, all you beasts of the forest.
Ku zo, dukanku namun jeji, ku zo ku ci, dukanku namun jeji!
10 Israel’s watchmen are blind, they are all oblivious; they are all mute dogs, they cannot bark; they are dreamers lying around, loving to slumber.
Matsaran Isra’ila makafi ne, dukansu jahilai ne; dukansu bebayen karnuka ne ba za su iya haushi ba; suna kwance ne kawai suna mafarki, suna son barci ba dama.
11 Like ravenous dogs, they are never satisfied. They are shepherds with no discernment; they all turn to their own way, each one seeking his own gain:
Su karnuka ne masu kwaɗayi; ba su taɓa ƙoshi. Su makiyaya ne marasa ganewa; duk sun nufi inda suka ga dama, kowa yana nemar wa kansa riba.
12 “Come, let me get the wine, let us imbibe the strong drink, and tomorrow will be like today, only far better!”
Kowanne yakan ce, “Zo, bari in samo ruwan inabi! Bari mu cika cikinmu da barasa! Gobe ma zai zama kamar yau, ko ma fiye da haka.”

< Isaiah 56 >