< Isaiah 19 >

1 This is the burden against Egypt: Behold, the LORD rides on a swift cloud; He is coming to Egypt. The idols of Egypt will tremble before Him, and the hearts of the Egyptians will melt within them.
Abin da Allah ya faɗa game da Masar, Duba, Ubangiji yana a kan girgije a sukwane yana kuwa zuwa Masar. Gumakan Masar sun firgita a gabansa, zukatan Masarawa sun karai.
2 “So I will incite Egyptian against Egyptian; brother will fight against brother, neighbor against neighbor, city against city, and kingdom against kingdom.
“Zan tā da hargitsi tsakanin mutumin Masar da mutumin Masar, ɗan’uwa zai yi gāba da ɗan’uwa maƙwabci ya yi gāba da maƙwabci, birni ya yi gāba da birni, mulki ya yi gāba da mulki.
3 Then the spirit of the Egyptians will be emptied out from among them, and I will frustrate their plans, so that they will resort to idols and spirits of the dead, to mediums and spiritists.
Masarawa za su karai, zan kuma sa shirye-shiryensu su zama banza; za su nemi shawarar gumaka da kuma ruhohin matattu, za su nemi shawarar mabiya da na masu duba.
4 I will deliver the Egyptians into the hands of harsh masters, and a fierce king will rule over them,”
Zan ba da Masarawa ga ikon azzalumi shugaba, mugun sarki kuma zai yi mulki a kansu,” in ji mai girma, Ubangiji Maɗaukaki.
5 The waters of the Nile will dry up, and the riverbed will be parched and empty.
Ruwayen kogi za su ƙafe, bakin kogi zai shanye yă kuma bushe.
6 The canals will stink; the streams of Egypt will trickle and dry up; the reeds and rushes will wither.
Wuriyoyi za su yi wari; rafuffukan Masar za su yi ta raguwa har su ƙafe. Iwa da jema za su bushe,
7 The bulrushes by the Nile, by the mouth of the river, and all the fields sown along the Nile, will wither, blow away, and be no more.
haka ma tsire-tsire kusa da Nilu, a bakin kogi. Kowane abin da aka shuka a gefen Nilu zai bushe, iska ta kwashe su ƙaf.
8 Then the fishermen will mourn, all who cast a hook into the Nile will lament, and those who spread nets on the waters will pine away.
Masu kamun kifi za su yi nishi su kuma yi makoki, dukan waɗanda suke jefan ƙugiyoyi a Nilu; waɗanda suke jefan abin kamun kifi a ruwa abin kamun kifin za su zama marasa amfani.
9 The workers in flax will be dismayed, and the weavers of fine linen will turn pale.
Waɗanda suke aiki da kaɗin auduga za su karai, masu yin lilin mai kyau za su fid da zuciya.
10 The workers in cloth will be dejected, and all the hired workers will be sick at heart.
Masu aikin tufafi ransu zai ɓace, kuma dukan masu samun albashi za su damu.
11 The princes of Zoan are mere fools; Pharaoh’s wise counselors give senseless advice. How can you say to Pharaoh, “I am one of the wise, a son of eastern kings”?
Shugabannin Zowan ba kome ba ne, wawaye ke kawai; mashawarta masu hikima na Fir’auna suna ba da shawarwari marasa amfani. Yaya za ka ce wa Fir’auna, “Ni ɗaya ne cikin masu hikima, almajirin sarakuna na dā can”?
12 Where are your wise men now? Let them tell you and reveal what the LORD of Hosts has planned against Egypt.
Ina masu hikima suke yanzu? Bari su nuna maka su kuma sanar da abin da Ubangiji Maɗaukaki ya shirya a kan Masar.
13 The princes of Zoan have become fools; the princes of Memphis are deceived. The cornerstones of her tribes have led Egypt astray.
Shugabannin Zowan sun zama wawaye, an ruɗe shugabannin Memfis dutsen kan kusurwa na mutanenta su sa Masar ta kauce.
14 The LORD has poured into her a spirit of confusion. Egypt has been led astray in all she does, as a drunkard staggers through his own vomit.
Ubangiji ya sa zuba musu ruhun jiri; suka sa Masar ta yi tangaɗi cikin kome da take yi, kamar yadda mutumin da ya bugu yake tangaɗi cikin amansa.
15 There is nothing Egypt can do— head or tail, palm or reed.
Babu abin da Masar za tă yi, kai ko wutsiya, reshen dabino ko iwa.
16 In that day the Egyptians will be like women. They will tremble with fear beneath the uplifted hand of the LORD of Hosts, when He brandishes it against them.
A wannan rana Masarawa za su zama kamar mata. Za su yi rawar jiki lokacin da Ubangiji Maɗaukaki ya ɗaga hannu a kansu.
17 The land of Judah will bring terror to Egypt; whenever Judah is mentioned, Egypt will tremble over what the LORD of Hosts has planned against it.
Ƙasar Yahuda kuma za kawo fargaba ga Masarawa; kowanne da Yahuda ya ambace zai firgita, saboda abin da Ubangiji Maɗaukaki yake shiri a kansu.
18 In that day five cities in the land of Egypt will speak the language of Canaan and swear allegiance to the LORD of Hosts. One of them will be called the City of the Sun.
A wannan rana birane biyar a Masar za su yi yaren Kan’ana su kuma miƙa kai cikin yarjejjeniya ga Ubangiji Maɗaukaki. Za a ce da ɗayansu Birnin Hallaka.
19 In that day there will be an altar to the LORD in the center of the land of Egypt, and a pillar to the LORD near her border.
A wannan rana za a kasance da bagade ga Ubangiji a tsakiyar Masar, da kuma ginshiƙin dutse Ubangiji a iyakarta.
20 It will be a sign and a witness to the LORD of Hosts in the land of Egypt. When they cry out to the LORD because of their oppressors, He will send them a savior and defender to rescue them.
Zai zama alama da kuma shaida ga Ubangiji Maɗaukaki a ƙasar Masar. Sa’ad da suka yi kuka ga Ubangiji saboda masu zaluntarsu, zai aiko musu mai ceto da mai kāriya, zai kuma cece su.
21 The LORD will make Himself known to Egypt, and on that day Egypt will acknowledge the LORD. They will worship with sacrifices and offerings; they will make vows to the LORD and fulfill them.
Saboda haka Ubangiji zai sanar da kansa ga Masarawa, kuma a wannan rana za su yarda da Ubangiji. Za su yi masa sujada da hadayu da hadayun hatsi; za su yi alkawura ga Ubangiji su kuma kiyaye su.
22 And the LORD will strike Egypt with a plague; He will strike them but heal them. They will turn to the LORD, and He will hear their prayers and heal them.
Ubangiji zai bugi Masar da annoba; zai buge su ya kuma warkar da su. Za su juyo wurin Ubangiji, zai amsa roƙonsu ya kuma warkar da su.
23 In that day there will be a highway from Egypt to Assyria. The Assyrians will go to Egypt, and the Egyptians to Assyria. The Egyptians and Assyrians will worship together.
A wannan rana za a kasance da babban hanya daga Masar zuwa Assuriya. Assuriyawa za su tafi Masar, Masarawa kuma za su tafi Assuriya. Masarawa da Assuriyawa za su yi sujada tare.
24 In that day Israel will join a three-party alliance with Egypt and Assyria—a blessing upon the earth.
A wannan rana Isra’ila za tă zama na uku, tare da Masar da Assuriya, abin albarka ga duniya.
25 The LORD of Hosts will bless them, saying, “Blessed be Egypt My people, Assyria My handiwork, and Israel My inheritance.”
Ubangiji Maɗaukaki zai albarkace su, yana cewa, “Albarka ta tabbata ga Masar, mutanena, Assuriya aikin hannuna, da kuma Isra’ila gādona.”

< Isaiah 19 >