< Isaiah 13 >

1 This is the burden against Babylon that Isaiah son of Amoz received:
Abubuwan da Allah ya yi magana a kai game da Babilon da Ishaya ɗan Amoz ya gani.
2 Raise a banner on a barren hilltop; call aloud to them. Wave your hand, that they may enter the gates of the nobles.
A tā da tuta a kan tudun da yake mai fili, ka tā da murya gare su; ka ɗaga hannu ka ba su alama don su shiga ƙofofi masu alfarma.
3 I have commanded My sanctified ones; I have even summoned My warriors to execute My wrath and exult in My triumph.
Na umarci tsarkakana; na umarci jarumawan yaƙina su gamsar da fushina, waɗanda suke farin ciki a nasarata.
4 Listen, a tumult on the mountains, like that of a great multitude! Listen, an uproar among the kingdoms, like nations gathered together! The LORD of Hosts is mobilizing an army for war.
Ka saurara, akwai surutu a kan duwatsu, sai ka ce na babban taron jama’a! Ka saurara, akwai hayaniya a cikin mulkoki, sai ka ce al’ummai ne suna ta tattaruwa! Ubangiji Maɗaukaki yana shirya mayaƙa don yaƙi.
5 They are coming from faraway lands, from the ends of the heavens— the LORD and the weapons of His wrath— to destroy the whole country.
Suna zuwa daga ƙasashe masu nesa, daga iyakokin duniya, Ubangiji da kuma fushinsa, zai hallaka dukan ƙasar.
6 Wail, for the Day of the LORD is near; it will come as destruction from the Almighty.
Ku yi ihu, gama ranar Ubangiji ta yi kusa za tă zo kamar hallaka daga Maɗaukaki.
7 Therefore all hands will fall limp, and every man’s heart will melt.
Saboda wannan, hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa.
8 Terror, pain, and anguish will seize them; they will writhe like a woman in labor. They will look at one another, their faces flushed with fear.
Tsoro zai kama su, zafi da azaba za su ci ƙarfinsu; za su yi ta murɗewa kamar mace mai naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu a ɓace.
9 Behold, the Day of the LORD is coming— cruel, with fury and burning anger— to make the earth a desolation and to destroy the sinners within it.
Duba, ranar Ubangiji tana zuwa, muguwar rana, mai hasala da zafin fushi, don ta mai da ƙasar kango ta kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta.
10 For the stars of heaven and their constellations will not give their light. The rising sun will be darkened, and the moon will not give its light.
Taurarin sama da ƙungiyoyinsu ba za su ba da haskensu ba. Rana za tă yi duhu wata kuma ba zai ba da haskensa ba.
11 I will punish the world for its evil and the wicked for their iniquity. I will end the haughtiness of the arrogant and lay low the pride of the ruthless.
Zan hukunta duniya saboda muguntarta, mugaye saboda zunubansu. Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi.
12 I will make man scarcer than pure gold, and mankind rarer than the gold of Ophir.
Zan sa mutum yă fi zinariya zalla wuyar samuwa, fiye da zinariyar Ofir wuyan gani.
13 Therefore I will make the heavens tremble, and the earth will be shaken from its place at the wrath of the LORD of Hosts on the day of His burning anger.
Saboda haka zan sa sammai su yi rawar jiki; duniya kuma za tă girgiza daga inda take a fushin Ubangiji Maɗaukaki, a ranar fushinsa mai ƙuna.
14 Like a hunted gazelle, like a sheep without a shepherd, each will return to his own people, each will flee to his native land.
Kamar barewar da ake farautarta kamar tumaki marasa makiyayi, haka nan kowane mutum zai koma ga mutanensa, kowane mutum zai gudu zuwa ƙasarsa.
15 Whoever is caught will be stabbed, and whoever is captured will die by the sword.
Duk wanda aka kama za a soke shi yă mutu; dukan waɗanda aka kama za su mutu ta takobi.
16 Their infants will be dashed to pieces before their eyes, their houses will be looted, and their wives will be ravished.
Za a fyaɗa’ya’yansu a ƙasa su yi kucu-kucu a idanunsu; za a washe gidajensu, a kuma kwana da matansu.
17 Behold, I will stir up against them the Medes, who have no regard for silver and no desire for gold.
Duba, zan zuga mutanen Medes su yi gāba da su, su da ba su kula da azurfa ba kuma ba sa damuwa da zinariya.
18 Their bows will dash young men to pieces; they will have no mercy on the fruit of the womb; they will not look with pity on the children.
Bakkunansu za su kashe samari; ba za su ji tausayin jarirai ba ba za su kuwa nuna jinƙai ga’yan yara ba.
19 And Babylon, the jewel of the kingdoms, the glory of the pride of the Chaldeans, will be overthrown by God like Sodom and Gomorrah.
Babilon, kayan daraja na mulkoki, abin fariyar Babiloniyawa, Allah zai kaɓantar da ita kamar yadda ya yi da Sodom da Gomorra.
20 She will never be inhabited or settled from generation to generation; no nomad will pitch his tent there, no shepherd will rest his flock there.
Ba za ƙara kasance da mazauna kuma ba ko a yi zama a cikinta dukan zamanai; Ba wani mutumin Arab da zai kafa tentinsa a can, ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can.
21 But desert creatures will lie down there, and howling creatures will fill her houses. Ostriches will dwell there, and wild goats will leap about.
Amma halittun hamada za su kwanta a can, diloli za su cika gidajenta; a can mujiyoyi za su zauna, a can kuma awakin jeji za su yi ta tsalle.
22 Hyenas will howl in her fortresses and jackals in her luxurious palaces. Babylon’s time is at hand, and her days will not be prolonged.
Kuraye za su yi ta kuka a kagarorinta, diloli kuma a cikin fadodinta masu alfarma. Lokacinta ya yi kusa, kwanakinta kuma ba za su yi tsawo ba.

< Isaiah 13 >