< Hosea 5 >

1 “Hear this, O priests! Take heed, O house of Israel! Give ear, O royal house! For this judgment is against you because you have been a snare at Mizpah, a net spread out on Tabor.
“Ku ji wannan, ku firistoci! Ku kasa kunne, ku Isra’ilawa! Ku saurara, ya ku gidan sarauta! Wannan hukunci yana a kanku, kun zama tarko a Mizfa, ragar da aka shimfiɗa a kan Tabor.
2 The rebels are deep in slaughter; but I will chastise them all.
’Yan tawaye sun yi zurfi cikin kisan gilla. Zan hore su duka.
3 I know all about Ephraim, and Israel is not hidden from Me. For now, O Ephraim, you have turned to prostitution; Israel is defiled.
Na san Efraim ƙaf; Isra’ila ba a ɓoye take a gare ni ba. Efraim, yanzu ka juya ka shiga karuwanci; Isra’ila ta lalace.
4 Their deeds do not permit them to return to their God, for a spirit of prostitution is within them, and they do not know the LORD.
“Ayyukansu ba su ba su dama su koma ga Allahnsu ba. Halin karuwanci yana cikin zuciyarsu; ba su yarda da Ubangiji ba.
5 Israel’s arrogance testifies against them; Israel and Ephraim stumble in their iniquity; even Judah stumbles with them.
Girmankan Isra’ila yana ba da shaida a kansu; Isra’ilawa, har ma Efraim, sun yi tuntuɓe a cikin zunubinsu; Yahuda ma ya yi tuntuɓe tare da su.
6 They go with their flocks and herds to seek the LORD, but they do not find Him; He has withdrawn Himself from them.
Sa’ad da suka tafi tare da garkunan shanu, tumaki da awakinsu don su nemi Ubangiji, ba za su same shi ba; ya janye kansa daga gare su.
7 They have been unfaithful to the LORD; for they have borne illegitimate children. Now the New Moon will devour them along with their land.
Su marasa aminci ne ga Ubangiji; suna haihuwar shegu. Yanzu bukukkuwar Sabon Watansu za su cinye su da gonakinsu.
8 Blow the ram’s horn in Gibeah, the trumpet in Ramah; raise the battle cry in Beth-aven: Lead on, O Benjamin!
“Amon kakaki a Gibeya, ƙaho a Rama. Ku yi kirarin yaƙi a Bet-Awen; ku ja gaba, ya Benyamin.
9 Ephraim will be laid waste on the day of rebuke. Among the tribes of Israel I proclaim what is certain.
Efraim za tă zama kango a ranar hukunci. A cikin kabilan Isra’ila na yi shelar abin da yake tabbatacce.
10 The princes of Judah are like those who move boundary stones; I will pour out My fury upon them like water.
Shugabannin Yahuda suna kamar waɗanda suke matsar da duwatsun shaidar da aka sa a kan iyaka ne. Zan zubo musu da fushina a kansu kamar rigyawar ruwa.
11 Ephraim is oppressed, crushed in judgment, for he is determined to follow worthless idols.
An danne Efraim, an murƙushe ta a shari’a ta ƙudura ga bin gumaka.
12 So I am like a moth to Ephraim, and like decay to the house of Judah.
Na zama kamar asu ga Efraim, kamar ruɓa ga mutanen Yahuda.
13 When Ephraim saw his sickness and Judah his wound, then Ephraim turned to Assyria and sent to the great king. But he cannot cure you or heal your wound.
“Sa’ad da Efraim ya ga ciwonsa, Yahuda kuwa miyakunta, sai Efraim ya juya ga Assuriya, ya aika wurin babban sarki don neman taimako. Amma bai iya warkar da kai ba, bai iya warkar da miyakunka ba.
14 For I am like a lion to Ephraim and like a young lion to the house of Judah. I, even I, will tear them to pieces and then go away. I will carry them off where no one can rescue them.
Gama zan zama kamar zaki ga Efraim, kamar babban zaki ga Yahuda. Zan yage su kucu-kucu in tafi; zan kwashe su, ba wanda zai kuɓutar da su.
15 Then I will return to My place until they admit their guilt and seek My face; in their affliction they will earnestly seek Me.”
Sa’an nan zan koma wurina sai sun yarda da laifinsu. Za su kuma nemi fuskata; cikin azabansu za su nace da nemana.”

< Hosea 5 >