< Exodus 31 >
1 Then the LORD said to Moses,
Sai Ubangiji ya ce wa Musa,
2 “See, I have called by name Bezalel son of Uri, the son of Hur, of the tribe of Judah.
“Duba, na zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, na kabilar Yahuda,
3 And I have filled him with the Spirit of God, with skill, ability, and knowledge in all kinds of craftsmanship,
na kuma cika shi da Ruhun Allah, fasaha, azanci, da kuma sani cikin kowace irin sana’a,
4 to design artistic works in gold, silver, and bronze,
don yin zāne-zāne na aikin zinariya, azurfa da tagulla,
5 to cut gemstones for settings, and to carve wood, so that he may be a master of every craft.
don yanka da shirya duwatsu, yin aikin katako, da kuma yin kowane irin aikin sana’ar hannu.
6 Moreover, I have selected Oholiab son of Ahisamach, of the tribe of Dan, as his assistant. I have also given skill to all the craftsmen, that they may fashion all that I have commanded you:
Ban da haka, na zaɓi Oholiyab ɗan Ahisamak, na kabilar Dan, don yă taimake shi. Na kuma ba da fasaha ga dukan masu aikin sana’ar hannu, don yin duk abin da na umarce ka.
7 the Tent of Meeting, the ark of the Testimony and the mercy seat upon it, and all the other furnishings of the tent—
Tentin Sujada, akwatin Alkawari tare da murfin kafara a bisansa, da dukan kayan aiki na tentin,
8 the table with its utensils, the pure gold lampstand with all its utensils, the altar of incense,
tebur da kayansa, wurin ajiye fitila na zinariya zalla, da dukan kayansa, bagaden ƙona turare,
9 the altar of burnt offering with all its utensils, and the basin with its stand—
bagaden hadaya ta ƙonawa da dukan kayansa, daro tare da mazauninsa,
10 as well as the woven garments, both the holy garments for Aaron the priest and the garments for his sons to serve as priests,
da kuma saƙaƙƙun riguna, tsarkakan riguna don Haruna firist da rigunan’ya’yansa maza, sa’ad da suke hidima a matsayin firistoci,
11 in addition to the anointing oil and fragrant incense for the Holy Place. They are to make them according to all that I have commanded you.”
da man shafewa, da turare mai ƙanshi don Wuri Mai Tsarki. Za a yi su kamar yadda na umarce ka.”
12 And the LORD said to Moses,
Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa,
13 “Tell the Israelites, ‘Surely you must keep My Sabbaths, for this will be a sign between Me and you for the generations to come, so that you may know that I am the LORD who sanctifies you.
“Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Dole ku kiyaye Asabbataina. Wannan zai zama alama tsakanina da ku daga tsara zuwa tsara, saboda ku sani ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.
14 Keep the Sabbath, for it is holy to you. Anyone who profanes it must surely be put to death. Whoever does any work on that day must be cut off from among his people.
“‘Ku kiyaye Asabbaci, domin yă zama mai tsarki a gare ku. Duk wanda ya ƙazantar da shi, za a kashe shi; duk wanda ya yi wani aiki a ranar, za a ware shi daga mutane.
15 For six days work may be done, but the seventh day is a Sabbath of complete rest, holy to the LORD. Whoever does any work on the Sabbath day must surely be put to death.
Kwana shida, za a yi aiki, amma a rana ta bakwai, Asabbaci ne na hutu, mai tsarki ga Ubangiji. Duk wanda ya yi wani aiki a Asabbaci, za a kashe shi.
16 The Israelites must keep the Sabbath, celebrating it as a permanent covenant for the generations to come.
Isra’ilawa za su kiyaye Asabbaci, suna bikinsa daga tsara zuwa tsara a matsayin madawwamin alkawari.
17 It is a sign between Me and the Israelites forever; for in six days the LORD made the heavens and the earth, but on the seventh day He rested and was refreshed.’”
Zai zama alama tsakanina da Isra’ilawa har abada, gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama da ƙasa, a rana ta bakwai kuma ya daina aiki, ya kuma huta.’”
18 When the LORD had finished speaking with Moses on Mount Sinai, He gave him the two tablets of the Testimony, tablets of stone inscribed by the finger of God.
Sa’ad da Ubangiji ya gama yin wa Musa magana a kan Dutsen Sinai, sai ya ba shi alluna biyu na Alkawari, allunan duwatsu rubutattu da yatsan Allah.