< Deuteronomy 11 >

1 You shall therefore love the LORD your God and always keep His charge, His statutes, His ordinances, and His commandments.
To, sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kullum ku kuma kiyaye abubuwan da yake bukata, ku kiyaye ƙa’idodinsa, dokokinsa da kuma umarnansu.
2 Know this day that it is not your children who have known and seen the discipline of the LORD your God: His greatness, His mighty hand, and His outstretched arm;
Ku tuna a yau, cewa’ya’yanku ba su ne suka gani suka kuma ɗanɗana horon Ubangiji Allahnku ba; ba su suka gani girmansa, hannunsa mai ƙarfi, hannunsa mai iko;
3 the signs and works He did in Egypt to Pharaoh king of Egypt and all his land;
alamun da ya aikata da abubuwan da ya yi a cikin Masar, ga Fir’auna sarkin Masar da kuma ga dukan ƙasarsa ba;
4 what He did to the Egyptian army and horses and chariots when He made the waters of the Red Sea engulf them as they pursued you, and how He destroyed them completely, even to this day;
ba su suka gani abin da ya yi wa mayaƙan Masar, da dawakansu da keken yaƙinsu, yadda ya sha kansu da ruwan Jan Teku yayinda suke bin ku, da yadda Ubangiji ya hallaka su ƙaƙaf ba.
5 what He did for you in the wilderness until you reached this place;
Ba’ya’yanku ba ne suka gani abin da ya yi dominku a hamada har sai da kuka kai wannan wuri ba,
6 and what He did in the midst of all the Israelites to Dathan and Abiram, the sons of Eliab the Reubenite, when the earth opened its mouth and swallowed them, their households, their tents, and every living thing that belonged to them.
ba su ba ne suka gani abin da ya yi ga Datan da Abiram,’ya’yan Eliyab mutumin Ruben, sa’ad da ƙasa ta buɗe bakinta a tsakiyar dukan Isra’ila ta haɗiye su tare da gidajensu, tentunansu da kowane abu mai rai da yake nasu ba.
7 For it is your own eyes that have seen every great work that the LORD has done.
Amma idanunku ne suka ga dukan waɗannan manyan abubuwan da Ubangiji ya yi.
8 You shall therefore keep every commandment I am giving you today, so that you may have the strength to go in and possess the land that you are crossing the Jordan to possess,
Saboda haka sai ku kiyaye dukan umarnan da nake ba ku a yau, don ku sami ƙarfin da za ku shiga, ku kuma karɓi ƙasar da kuke haye Urdun ku mallaka,
9 and so that you may live long in the land that the LORD swore to your fathers to give them and their descendants, a land flowing with milk and honey.
domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba su da zuriyarsu, ƙasa mai zub da madara da zuma.
10 For the land that you are entering to possess is not like the land of Egypt, from which you have come, where you sowed your seed and irrigated on foot, like a vegetable garden.
Ƙasar da kuke shiga, ku karɓa, ba kamar ƙasar Masar ba ce, inda kuka fito, inda kuka shuka iri, ku yi ta zuwa kuna banruwa kamar lambu.
11 But the land that you are crossing the Jordan to possess is a land of mountains and valleys that drinks in the rain from heaven.
Amma ƙasar da kuke haye Urdun ku mallaki, ƙasa ce ta duwatsu da kwaruruka wadda ruwan sama ne yake jiƙe ta.
12 It is a land for which the LORD your God cares; the eyes of the LORD your God are always on it, from the beginning to the end of the year.
Ƙasa ce da Ubangiji Allahnku yake lura da ita; idanun Ubangiji Allahnku yana a kai daga farkon shekara har zuwa ƙarshenta.
13 So if you carefully obey the commandments I am giving you today, to love the LORD your God and to serve Him with all your heart and with all your soul,
Saboda haka in kun yi biyayya ga umarnan da nake ba ku a yau cikin aminci, kuna ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna kuma bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku,
14 then I will provide rain for your land in season, the autumn and spring rains, that you may gather your grain, new wine, and oil.
sai in aika da ruwan sama a ƙasarku a lokacinsa, ruwan saman bazara da kuma na kaka, don ku tattara hatsinku, sabon inabinku da kuma manku.
15 And I will provide grass in the fields for your livestock, and you will eat and be satisfied.
Zan tanadar da ciyawa a filaye don shanunku, za ku ci, ku kuma ƙoshi.
16 But be careful that you are not enticed to turn aside to worship and bow down to other gods,
Ku yi hankali, kada a ruɗe ku har ku bauta wa alloli, ku kuma yi musu sujada,
17 or the anger of the LORD will be kindled against you. He will shut the heavens so that there will be no rain, nor will the land yield its produce, and you will soon perish from the good land that the LORD is giving you.
don kada fushin Ubangiji yă ƙuna a kanku, yă rufe sammai, ku rasa ruwa, ƙasa kuma ta kāsa ba da amfaninta, da haka za ku murmutu nan da nan a kyakkyawar ƙasar da Ubangiji yake ba ku.
18 Fix these words of mine in your hearts and minds; tie them as reminders on your hands and bind them on your foreheads.
Saboda haka, sai ku riƙe waɗannan kalmomina gam a zukatanku da ranku; ku ɗaura su kamar alama a hannuwanku, da goshinku.
19 Teach them to your children, speaking about them when you sit at home and when you walk along the road, when you lie down and when you get up.
Ku koyar da su ga’ya’yanku, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
20 Write them on the doorposts of your houses and on your gates,
Ku rubuta su a kan madogaran ƙofofin gidajenku, da a kan ƙofofinku,
21 so that as long as the heavens are above the earth, your days and those of your children may be multiplied in the land that the LORD swore to give your fathers.
saboda kwanakinku da kwanakin’ya’yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninku, muddin sama tana bisa duniya.
22 For if you carefully keep all these commandments I am giving you to follow—to love the LORD your God, to walk in all His ways, and to hold fast to Him—
In kuka lura, kuka kuma kiyaye dukan umarnai da nake ba ku, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma riƙe shi gam,
23 then the LORD will drive out all these nations before you, and you will dispossess nations greater and stronger than you.
Ubangiji zai kori dukan waɗannan al’ummai a gabanku, za ku kuma kore al’umman da suka fi ku yawa da ƙarfi.
24 Every place where the sole of your foot treads will be yours. Your territory will extend from the wilderness to Lebanon, and from the Euphrates River to the Western Sea.
Duk inda tafin ƙafanku ya taka, zai zama naku; iyakarku zai kama daga hamadan Lebanon da kuma daga Kogin Yuferites zuwa Bahar Rum.
25 No man will be able to stand against you; the LORD your God will put the fear and dread of you upon all the land, wherever you set foot, as He has promised you.
Babu mutumin da zai iya tsayayya da ku. Ubangiji Allahnku, zai sa razana da tsoronku a dukan ƙasar, a duk inda kuka tafi, kamar yadda ya alkawarta muku.
26 See, today I am setting before you a blessing and a curse—
Ga shi, a yau, ina sa a gabanku albarka da kuma la’ana,
27 a blessing if you obey the commandments of the LORD your God that I am giving you today,
albarka in kun yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, da nake ba ku;
28 but a curse if you disobey the commandments of the LORD your God and turn aside from the path I command you today by following other gods, which you have not known.
la’ana in ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, kuka kuma juya daga hanyar da na umarce ku, ta wurin bin waɗansu alloli, waɗanda ba ku sani ba.
29 When the LORD your God brings you into the land you are entering to possess, you are to proclaim the blessing on Mount Gerizim and the curse on Mount Ebal.
Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da za ku shiga ku ci gādonta, sai ku yi shelar albarkun nan a dutsen Gerizim, ku kuma yi na la’ana a dutsen Ebal.
30 Are not these mountains across the Jordan, west of the road toward the sunset, in the land of the Canaanites who live in the Arabah opposite Gilgal near the Oak of Moreh?
Waɗannan duwatsu biyu suna a hayin Urdun, yamma da hanya a ƙasar Kan’aniyawa mazaunan Araba, kusa da Gilgal wajajen manyan itatuwan More.
31 For you are about to cross the Jordan to enter and possess the land that the LORD your God is giving you. When you take possession of it and settle in it,
Kuna gab da ƙetare Urdun fa, ku shiga, ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Sa’ad da kuka karɓe ta, kuka kuma zauna a can,
32 be careful to follow all the statutes and ordinances that I am setting before you today.
ku tabbata kun yi biyayya da dukan ƙa’idodi, da kuma dokokin da nake sawa a gabanku a yau.

< Deuteronomy 11 >