< Acts 2 >
1 When the day of Pentecost came, they were all together in one place.
Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya.
2 Suddenly a sound like a mighty rushing wind came from heaven and filled the whole house where they were sitting.
Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune.
3 They saw tongues like flames of fire that separated and came to rest on each of them.
Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu.
4 And they were all filled with the Holy Spirit and began to speak in other tongues as the Spirit enabled them.
Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.
5 Now there were dwelling in Jerusalem God-fearing Jews from every nation under heaven.
To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya.
6 And when this sound rang out, a crowd came together in bewilderment, because each one heard them speaking his own language.
Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa.
7 Astounded and amazed, they asked, “Are not all these men who are speaking Galileans?
Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne?
8 How is it then that each of us hears them in his own native language?
To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa?
9 Parthians, Medes, and Elamites; residents of Mesopotamia, Judea and Cappadocia, Pontus and Asia,
Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya,
10 Phrygia and Pamphylia, Egypt and the parts of Libya near Cyrene; visitors from Rome,
Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma
11 both Jews and converts to Judaism; Cretans and Arabs—we hear them declaring the wonders of God in our own tongues!”
(Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!”
12 Astounded and perplexed, they asked one another, “What does this mean?”
A ruɗe kuma cike da mamaki, suka tambayi junansu cewa, “Mene ne wannan yake nufi?”
13 But others mocked them and said, “They are drunk on new wine!”
Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.”
14 Then Peter stood up with the Eleven, lifted up his voice, and addressed the crowd: “Men of Judea and all who dwell in Jerusalem, let this be known to you, and listen carefully to my words.
Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa.
15 These men are not drunk, as you suppose. It is only the third hour of the day!
Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai!
16 No, this is what was spoken by the prophet Joel:
A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa,
17 ‘In the last days, God says, I will pour out My Spirit on all people. Your sons and daughters will prophesy, your young men will see visions, your old men will dream dreams.
“Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe, zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane.’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, samarinku za su ga wahayoyi, dattawanku kuma za su yi mafarkai.
18 Even on My menservants and maidservants I will pour out My Spirit in those days, and they will prophesy.
Kai, har ma a kan bayina, maza da mata, zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki, za su kuwa yi annabci.
19 I will show wonders in the heavens above and signs on the earth below, blood and fire and billows of smoke.
Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama da alamu a nan ƙasa, jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi.
20 The sun will be turned to darkness, and the moon to blood, before the coming of the great and glorious Day of the Lord.
Za a mai da rana duhu, wata kuma ya zama jini, kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji.
21 And everyone who calls on the name of the Lord will be saved.’
Kuma duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’
22 Men of Israel, listen to this message: Jesus of Nazareth was a man certified by God to you by miracles, wonders, and signs, which God did among you through Him, as you yourselves know.
“Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani.
23 He was delivered up by God’s set plan and foreknowledge, and you, by the hands of the lawless, put Him to death by nailing Him to the cross.
An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye.
24 But God raised Him from the dead, releasing Him from the agony of death, because it was impossible for Him to be held in its clutches.
Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya’yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.
25 David says about Him: ‘I saw the Lord always before me; because He is at my right hand, I will not be shaken.
Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa, “‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana. Gama yana a hannuna na dama, ba zan jijjigu ba.
26 Therefore my heart is glad and my tongue rejoices; my body also will dwell in hope,
Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna, jikina kuma zai kasance da bege,
27 because You will not abandon my soul to Hades, nor will You let Your Holy One see decay. (Hadēs )
gama ba za ka bar ni cikin kabari ba, ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba. (Hadēs )
28 You have made known to me the paths of life; You will fill me with joy in Your presence.’
Ka sanar da ni hanyoyin rai, za ka cika ni da farin ciki a gabanka.’
29 Brothers, I can tell you with confidence that the patriarch David died and was buried, and his tomb is with us to this day.
“’Yan’uwa, zan iya tabbatar muku gabagadi cewa kakanmu Dawuda ya mutu aka kuma binne shi, kabarinsa kuwa yana a nan har yă zuwa yau.
30 But he was a prophet and knew that God had promised him on oath that He would place one of his descendants on his throne.
Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa.
31 Foreseeing this, David spoke about the resurrection of the Christ, that He was not abandoned to Hades, nor did His body see decay. (Hadēs )
Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba. (Hadēs )
32 God has raised this Jesus to life, to which we are all witnesses.
Allah ya tashe wannan Yesu zuwa rai, mu kuwa duk shaidu ne ga wannan.
33 Exalted, then, to the right hand of God, He has received from the Father the promised Holy Spirit and has poured out what you now see and hear.
An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji.
34 For David did not ascend into heaven, but he himself says: ‘The Lord said to my Lord, “Sit at My right hand
Gama Dawuda bai hau zuwa sama ba, duk da haka ya ce, “‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana,
35 until I make Your enemies a footstool for Your feet.”’
sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.”’
36 Therefore let all Israel know with certainty that God has made this Jesus, whom you crucified, both Lord and Christ!”
“Saboda haka bari dukan Isra’ila su tabbatar da wannan. Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.”
37 When the people heard this, they were cut to the heart and asked Peter and the other apostles, “Brothers, what shall we do?”
Sa’ad da mutane suka ji wannan, sai suka soku a zuci sai suka ce wa Bitrus da sauran manzanni, “’Yan’uwa, me za mu yi?”
38 Peter replied, “Repent and be baptized, every one of you, in the name of Jesus Christ for the forgiveness of your sins, and you will receive the gift of the Holy Spirit.
Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki.
39 This promise belongs to you and your children and to all who are far off—to all whom the Lord our God will call to Himself.”
Alkawarin dominku ne da’ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.”
40 With many other words he testified, and he urged them, “Be saved from this corrupt generation.”
Da waɗansu kalmomi masu yawa ya gargaɗe su; ya kuma roƙe su cewa, “Ku ceci kanku daga wannan lalataccen zamani.”
41 Those who embraced his message were baptized, and about three thousand were added to the believers that day.
Waɗanda suka yarda da saƙonsa kuwa aka yi musu baftisma, a ranar kuwa yawansu ya ƙaru da mutum kusan dubu uku.
42 They devoted themselves to the apostles’ teaching and to the fellowship, to the breaking of bread and to prayer.
Suka ba da kansu ga koyarwar manzanni da kuma ga zumunci, ga gutsuttsura burodin da kuma ga addu’a.
43 A sense of awe came over everyone, and the apostles performed many wonders and signs.
Kowa ya cika da tsoro, manzannin kuwa suka aikata abubuwan banmamaki da alamu masu yawa.
44 All the believers were together and had everything in common.
Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare.
45 Selling their possessions and goods, they shared with anyone who was in need.
Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa.
46 With one accord they continued to meet daily in the temple courts and to break bread from house to house, sharing their meals with gladness and sincerity of heart,
Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya,
47 praising God and enjoying the favor of all the people. And the Lord added to their number daily those who were being saved.
suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.