< Acts 11 >

1 The apostles and brothers throughout Judea soon heard that the Gentiles also had received the word of God.
Yanzu Manzani da 'yan'uwa wadanda suke cikin Yahudiya suka ji cewa al'ummai ma sun karbi maganar Allah
2 So when Peter went up to Jerusalem, the circumcised believers took issue with him
Lokacin da Bitrus ya je Urushalima, wadanda suke na kaciya suka zarge shi;
3 and said, “You visited uncircumcised men and ate with them.”
suka ce, “Ka hada kai tare da mutane marasa kaciya kana ci tare da su!”
4 But Peter began and explained to them the whole sequence of events:
Amma Bitrus ya fara bayyana masu dalla-dalla; ya ce,
5 “I was in the city of Joppa praying, and in a trance I saw a vision of something like a large sheet being let down from heaven by its four corners, and it came right down to me.
Ina addu'a a cikin birnin Yafa, sai na ga wahayi game da taska yana saukowa, kamar babban mayafi da aka saukar daga sama ta kusurwan nan hudu. Ya sauko gabana.
6 I looked at it closely and saw four-footed animals of the earth, wild beasts, reptiles, and birds of the air.
Na zura masa ido kuma na yi tunani a kansa, na ga dabbobi masu kafa hudu na duniya, miyagun dabbobi, da masu rarrafe, da tsuntsayen sama.
7 Then I heard a voice saying to me, ‘Get up, Peter, kill and eat.’
Sai na ji murya tana ce da ni, “Tashi, Bitrus, yanka ka ci.”
8 ‘No, Lord,’ I said, ‘for nothing impure or unclean has ever entered my mouth.’
Na ce, “Ba haka ba, Ubangiji: gama babu abu mara tsarki ko mai kazanta da ya taba shiga bakina.”
9 But the voice spoke from heaven a second time, ‘Do not call anything impure that God has made clean.’
Amma murya ta amsa kuma daga sama cewa, “Abin da Allah ya kira mai tsarki, kada ka kira shi mara tsarki.”
10 This happened three times, and everything was drawn back up into heaven.
Wannan ya faru sau uku, sai dukan komai ya koma sama.
11 Just then three men sent to me from Caesarea stopped at the house where I was staying.
Nan da nan sai ga mutane uku tsaye a gaban gidan da muke; an aike su daga Kaisariya zuwa gare ni.
12 The Spirit told me to accompany them without hesitation. These six brothers also went with me, and we entered the man’s home.
Ruhun ya umurce ni in tafi tare da su, ba tare da nuna banbanci game da su ba. Yan'uwan nan shida sun tafi tare da ni, sai muka shiga gidan mutumin.
13 He told us how he had seen an angel standing in his house and saying, ‘Send to Joppa for Simon who is called Peter.
Ya fada mana yadda ya ga mala'ika tsaye a cikin gidansa yana cewa “Aiki mutane zuwa Yafa, su kirawo Saminu wanda ake kira Bitrus.
14 He will convey to you a message by which you and all your household will be saved.’
Zai gaya maku sakon da za ku sami ceto kai da dukan gidanka.”
15 As I began to speak, the Holy Spirit fell upon them, just as He had fallen upon us at the beginning.
Da na fara magana da su, Ruhu Mai Tsarki ya sauko akansu kamar yadda ya sauko mana tun da farko.
16 Then I remembered the word of the Lord, as He used to say, ‘John baptized with water, but you will be baptized with the Holy Spirit.’
Sai na tuna da maganar Ubangiji, yadda ya ce,”Hakika Yahaya ya yi baptisma da ruwa, amma ku za a yi maku baptisma da Ruhu Mai Tsarki.”
17 So if God gave them the same gift He gave us who believed in the Lord Jesus Christ, who was I to hinder the work of God?”
To, idan Allah ya yi masu baiwa kamar yadda ya yi mana yayin da muka bada gaskiya ga Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni da zan yi jayayya da Allah?
18 When they heard this, their objections were put to rest, and they glorified God, saying, “So then, God has granted even the Gentiles repentance unto life.”
Da suka ji wadannan abubuwa, suka rasa ta cewa, amma suka daukaka Allah suka ce “Ga al'ummai ma Allah ya basu tuba zuwa rai.”
19 Meanwhile those scattered by the persecution that began with Stephen traveled as far as Phoenicia, Cyprus, and Antioch, speaking the message only to Jews.
Sai wadanda suka warwatsu saboda tsananin da ya bi bayan mutuwan Istifanas, suka yadu har zuwa Finikiya, Kuburus da Antakiya, amma suka yi wa'azin Yesu ga Yahudawa kadai.
20 But some of them, men from Cyprus and Cyrene, went to Antioch and began speaking to the Greeks as well, proclaiming the good news about the Lord Jesus.
Amma wadan sunsu, mutane daga Kuburus da Kurane, suka zo Antakiya suka yi magana da hellenawa, suna yi masu wa'azin Ubangiji Yesu.
21 The hand of the Lord was with them, and a great number of people believed and turned to the Lord.
Kuma ikon Ubangiji yana tare da su, har mutane da yawa suka gaskata kuma suka juyo wurin Ubangiji.
22 When news of this reached the ears of the church in Jerusalem, they sent Barnabas to Antioch.
Labari game da su ya iso kunnen ikilisiya da ke Urushalima: sai suka aika da Barnaba zuwa can Antakiya.
23 When he arrived and saw the grace of God, he rejoiced and encouraged them all to abide in the Lord with all their hearts.
Da ya iso kuma ya ga kyautar Allah, sai ya yi farinciki; ya karfafa su dukka su kafu cikin Ubangiji da dukan zuciyar su.
24 Barnabas was a good man, full of the Holy Spirit and faith, and a great number of people were brought to the Lord.
Domin shi mutumin kirki ne, cike kuma da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, sai mutane da yawa suka karu ga Ubangiji.
25 Then Barnabas went to Tarsus to look for Saul,
Sai Barnaba ya tafi Tarsus domin ya nemi Shawulu.
26 and when he found him, he brought him back to Antioch. So for a full year they met together with the church and taught large numbers of people. The disciples were first called Christians at Antioch.
Da ya same shi, ya kawo shi Antakiya. Ya kasance, shekara guda suna taruwa tare da ikilisiya suka koyar da mutane da yawa. A Antakiya ne aka fara kiran almajiran Krista.
27 In those days some prophets came down from Jerusalem to Antioch.
A cikin kwanakin nan wadansu annabawa daga Urushalima suka zo Antakiya.
28 One of them named Agabus stood up and predicted through the Spirit that a great famine would sweep across the whole world. (This happened under Claudius.)
Daya daga cikinsu, mai suna Agabas ya mike tsaye yayi magana da ikon Ruhu cewa za a yi tsanani fari ko'ina a duniya. Wannan ya faru ne a zamanin Kalaudiya.
29 So the disciples, each according to his ability, decided to send relief to the brothers living in Judea.
Sai, almajiran, suka dau niyya kowa gwargwadon karfinsa, su aika wa 'yan'uwa da ke Yahudiya da taimako.
30 This they did, sending their gifts to the elders with Barnabas and Saul.
Suka yi haka; sun aika wa dattawa da kudi ta hanun Barnaba da Shawulu.

< Acts 11 >