< 2 Kings 9 >

1 Now Elisha the prophet summoned one of the sons of the prophets and said to him, “Tuck your cloak under your belt, take this flask of oil, and go to Ramoth-gilead.
Sai Elisha ya kira wani daga cikin ƙungiyar annabawa, ya ce masa, “Ka sha ɗamara, ka ɗauki wannan kwalabar mai ka je Ramot Gileyad.
2 When you arrive, look for Jehu son of Jehoshaphat, the son of Nimshi. Go in, get him away from his companions, and take him to an inner room.
Da ka isa can, ka nemi Yehu ɗan Yehoshafat, ɗan Nimshi. Ka je wurinsa, ka ja shi gefe daga abokansa, ka shiga da shi ɗaki na ciki.
3 Then take the flask of oil, pour it on his head, and declare, ‘This is what the LORD says: I anoint you king over Israel.’ Then open the door and run. Do not delay!”
Sa’an nan ka ɗauki kwalabar man ka zuba a kansa, ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, na naɗa ka sarkin Isra’ila.’ Sa’an nan ka buɗe ƙofa ka ruga a guje; kada ka ɓata lokaci!”
4 So the young prophet went to Ramoth-gilead,
Sai saurayin nan, annabi, ya tafi Ramot Gileyad.
5 and when he arrived, the army commanders were sitting there. “I have a message for you, commander,” he said. “For which of us?” asked Jehu. “For you, commander,” he replied.
Da ya isa can, sai ya tarar da hafsoshin soji zaune a wuri guda. Sai ya ce, “Ina da saƙo dominka komanda.” Sai Yehu ya ce, “Wanne a cikinmu?” Sai ce, “Dominka, komanda.”
6 So Jehu got up and went into the house, where the young prophet poured the oil on his head and declared, “This is what the LORD, the God of Israel, says: ‘I anoint you king over the LORD’s people Israel.
Sai Yehu ya tashi ya shiga cikin gida. Sa’an nan annabin ya zuba wa Yehu mai a kā, ya ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na naɗa ka sarki a bisa jama’ar Ubangiji, wato, Isra’ila.
7 And you are to strike down the house of your master Ahab, so that I may avenge the blood of My servants the prophets and the blood of all the servants of the LORD shed by the hand of Jezebel.
Za aka hallaka gidan Ahab maigidanka, zan kuma ɗauki fansar jinin bayina annabawa da kuma jinin dukan bayin Ubangiji da Yezebel ta zub da.
8 The whole house of Ahab will perish, and I will cut off from Ahab every male, both slave and free, in Israel.
Dukan gidan Ahab zai hallaka. Zan kashe dukan’ya’yan Ahab maza a Isra’ila, bayi ko’yantattu.
9 I will make the house of Ahab like the houses of Jeroboam son of Nebat and Baasha son of Ahijah.
Zan mai da gidan Ahab kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat da kuma kamar gidan Ba’asha ɗan Ahiya.
10 And on the plot of ground at Jezreel the dogs will devour Jezebel, and there will be no one to bury her.’” Then the young prophet opened the door and ran.
Game da Yezebel kuwa, karnuka za su cinye ta a fili a Yezireyel, ba kuwa wanda zai binne ta.’” Sa’an nan ya buɗe ƙofa ya ruga a guje.
11 When Jehu went out to the servants of his master, they asked, “Is everything all right? Why did this madman come to you?” “You know his kind and their babble,” he replied.
Da Yehu ya koma wurin sauran hafsoshin sai ɗaya daga cikinsu ya tambaye shi, “Lafiya? Me ya kawo wannan mahaukaci a wurinka?” Sai Yehu ya ce, “Ka san mahaukacin nan da irin maganganunsa.”
12 “That is a lie!” they said. “Tell us now!” So Jehu answered, “He talked to me about this and that, and he said, ‘This is what the LORD says: I anoint you king over Israel.’”
Suka ce masa, “Ba gaskiya ba ne, ka dai faɗa mana.” Yehu ya ce, “Ga abin da ya ce mini, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, na naɗa ka sarki a bisa Isra’ila.’”
13 Quickly, each man took his garment and put it under Jehu on the bare steps. Then they blew the ram’s horn and proclaimed, “Jehu is king!”
Sai suka yi sauri suka ɗauki rigunansu suka shimfiɗa a ƙasa, suka busa kakaki, suka yi ihu, suka ce, “Yehu ne sarki.”
14 Thus Jehu son of Jehoshaphat, the son of Nimshi, conspired against Joram. (Now Joram and all Israel had been defending Ramoth-gilead against Hazael king of Aram,
Saboda haka, Yehu ɗan Yehoshafat, ɗan Nimshi, ya ƙulla wa Yoram maƙarƙashiya (To, Yoram da dukan Isra’ila suna kāre Ramot Gileyad daga Hazayel sarkin Aram,
15 but King Joram had returned to Jezreel to recover from the wounds he had suffered at the hands of the Arameans in the battle against Hazael their king.) So Jehu said, “If you commanders wish to make me king, then do not let anyone escape from the city to go and tell it in Jezreel.”
amma Sarki Yoram ya koma Yezireyel don yă farfaɗo daga raunukan da Arameyawa suka ji masa a wata gabzawar da ya yi da Hazayel sarkin Aram.) Yehu ya ce, “In haka kuke ji, kada ku bar wani yă sulluɓe daga birnin yă kai labarin Yezireyel.”
16 Then Jehu got into his chariot and went to Jezreel, because Joram was laid up there and Ahaziah king of Judah had gone down to see him.
Sai ya tashi ya ɗauki keken yaƙinsa ya tafi Yezireyel gama Yoram yana hutawa a can. Ga kuma Ahaziya sarkin Yahuda ya je don yă gan shi.
17 Now the watchman standing on the tower in Jezreel saw Jehu’s troops approaching, and he called out, “I see a company of troops!” “Choose a rider,” Joram commanded. “Send him out to meet them and ask, ‘Have you come in peace?’”
Mai tsaro kuwa yana tsaye a kan hasumiya a Yezireyel, sai ya hangi rundunar Yehu sa’ad da yake zuwa. Ya ce, “Na ga wata runduna.” Sai Yoram ya umarta, “Nemi mahayin doki a aike shi yă tarye su, yă kuma tambaye su, ‘Lafiya?’”
18 So a horseman rode off to meet Jehu and said, “This is what the king asks: ‘Have you come in peace?’” “What do you know about peace?” Jehu replied. “Fall in behind me.” And the watchman reported, “The messenger reached them, but he is not coming back.”
Sai mahayin dokin ya hau, ya ruga, ya taryi Yehu, ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’” Sai Yehu ya ce masa, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.” Sai mai tsaron ya ce wa sarki, “Ɗan saƙon ya kai wurinsu, amma ba ya dawowa.”
19 So the king sent out a second horseman, who went to them and said, “This is what the king asks: ‘Have you come in peace?’” “What do you know about peace?” Jehu replied. “Fall in behind me.”
Saboda haka sarki ya sāke aika mahayin doki na biyu. Sa’ad da ya isa wurinsu sai ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’” Yehu ya ce, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.”
20 Again the watchman reported, “He reached them, but he is not coming back. And the charioteer is driving like Jehu son of Nimshi —he is driving like a madman!”
Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma shi ma ba ya dawowa. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa kamar mahaukaci.”
21 “Harness!” Joram shouted, and they harnessed his chariot. Then Joram king of Israel and Ahaziah king of Judah set out, each in his own chariot, and met Jehu on the property of Naboth the Jezreelite.
Yoram ya umarta, “Haɗa mini keken yaƙi!” Da aka haɗa, sai Yoram sarkin Isra’ila, da Ahaziya sarkin Yahuda, suka hau suka tafi, kowa a keken yaƙinsa, don su taryi Yehu. Suka sadu da shi a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel.
22 When Joram saw Jehu, he asked, “Have you come in peace, Jehu?” “How can there be peace,” he replied, “as long as the idolatry and witchcraft of your mother Jezebel abound?”
Sa’ad da Yoram ya ga Yehu sai ya tambaye shi, “Lafiya kuwa ka zo, Yehu?” Yehu ya ce, “Ina kuwa lafiya, da yake dukan bautar gumaka da bokancin mahaifiyarka Yezebel sun bazu ko’ina?”
23 Joram turned around and fled, calling out to Ahaziah, “Treachery, Ahaziah!”
Yoram ya juya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya, “Cin amana, Ahaziya!”
24 Then Jehu drew his bow and shot Joram between the shoulders. The arrow pierced his heart, and he slumped down in his chariot.
Sai Yehu ya ja bakansa ya harbi Yoram a tsakanin kafaɗunsa. Kibiyar ta same shi a zuciyarsa sai ya fāɗi a cikin keken yaƙinsa.
25 And Jehu said to Bidkar his officer, “Pick him up and throw him into the field of Naboth the Jezreelite. For remember that when you and I were riding together behind his father Ahab, the LORD lifted up this burden against him:
Yehu ya ce wa Bidkar, hafsan keken yaƙinsa, “Ka ɗauke shi ka jefar a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel. Ka tuna yadda ni da kai muke a kekunan yaƙi a bayan Ahab mahaifinsa sa’ad da Ubangiji ya yi wannan annabci game da shi,
26 ‘As surely as I saw the blood of Naboth and the blood of his sons yesterday, declares the LORD, so will I repay you on this plot of ground, declares the LORD.’ Now then, according to the word of the LORD, pick him up and throw him on the plot of ground.”
‘Jiya na ga jinin Nabot da jinin’ya’yansa, in ji Ubangiji, kuma ba shakka zan ɗauki fansa a wannan fili, in ji Ubangiji.’ Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar da shi a bisa wannan fegi, bisa ga faɗin Ubangiji. Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar a filin, in ji Ubangiji.”
27 When King Ahaziah of Judah saw this, he fled up the road toward Beth-haggan. And Jehu pursued him, shouting, “Shoot him too!” So they shot Ahaziah in his chariot on the Ascent of Gur, near Ibleam, and he fled to Megiddo and died there.
Sa’ad da Ahaziya sarkin Yahuda ya ga abin da ya faru, sai ya haura hanyar Bet Haggan a guje. Yehu ya bi shi yana ihu, “A kashe shi, shi ma!” Suka ji masa rauni a keken yaƙinsa a hanya zuwa Gur, kusa da Ibileyam amma ya tsere zuwa Megiddo ya mutu a can.
28 Then his servants carried him by chariot to Jerusalem and buried him with his fathers in his tomb in the City of David.
Barorinsa suka ɗauke shi cikin keken yaƙi zuwa Urushalima suka binne shi a kabarinsa tare da kakanninsa a birnin Dawuda.
29 (In the eleventh year of Joram son of Ahab, Ahaziah had become king over Judah.)
(A shekara ta goma sha ɗaya ta Yoram ɗan Ahab, Ahaziya ya zama sarkin Yahuda.)
30 Now when Jehu arrived in Jezreel, Jezebel heard of it. So she painted her eyes, adorned her head, and looked down from a window.
Sa’an nan Yehu ya je Yezireyel. Sa’ad da Yezebel ta sami labari, sai ta sha kwalliya ta gyara gashin kanta, ta zauna tana kallo daga taga.
31 And as Jehu entered the gate, she asked, “Have you come in peace, O Zimri, murderer of your master?”
Yayinda Yehu ya shiga ƙofa, sai ta ce, “Lafiya, kai Zimri, mai kashe maigidansa?”
32 He looked up at the window and called out, “Who is on my side? Who?” And two or three eunuchs looked down at him.
Sai ya ɗaga ido ya dubi tagan ya ce, “Wa yake gefena? Wane ne?” Sai bābānni biyu ko uku suka leƙo suka dube shi.
33 “Throw her down!” yelled Jehu. So they threw her down, and her blood splattered on the wall and on the horses as they trampled her underfoot.
Yehu ya ce musu, “Ku jefa ta ƙasa!” Sai suka jefar da ita, jininta ya fantsama a jikin bango da kuma a jikin dawakai yayinda suke tattaka ta.
34 Then Jehu went in and ate and drank. “Take care of this cursed woman,” he said, “and bury her, for she was the daughter of a king.”
Yehu ya shiga ya ci, ya kuma sha. Ya ce, “Ku san yadda za ku yi da la’ananniyan nan, ku binne ta, gama’yar sarki ce.”
35 But when they went out to bury her, they found nothing but her skull, her feet, and the palms of her hands.
Amma sa’ad da suka je don su binne ta, ba su sami kome ba sai ƙoƙon kanta, ƙafafunta da kuma hannuwanta.
36 So they went back and told Jehu, who replied, “This is the word of the LORD, which He spoke through His servant Elijah the Tishbite: ‘On the plot of ground at Jezreel the dogs will devour the flesh of Jezebel.
Suka komo suka faɗa wa Yehu, wanda ya ce, “Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya faɗa ta bakin bawansa Iliya mutumin Tishbe. A fili, a Yezireyel, karnuka za su cinye naman Yezebel.
37 And Jezebel’s body will lie like dung in the field on the plot of ground at Jezreel, so that no one can say: This is Jezebel.’”
Gawar Yezebel zai zama kamar juji a ƙasa, a fili, a Yezireyel, har ba wanda zai iya cewa, ‘Wannan Yezebel ce.’”

< 2 Kings 9 >