< 1 Corinthians 6 >

1 If any of you has a grievance against another, how dare he go to law before the unrighteous instead of before the saints!
Idan wani a cikin ku yana jayayya da wani, to sai ya tafi kotu gaban alkali marar bada gaskiya, a maimakon gaban masu bi?
2 Do you not know that the saints will judge the world? And if you are to judge the world, are you not competent to judge trivial cases?
Ko ba ku sani ba, masubi ne za su yiwa duniya shari'a? Kuma idan ku za ku yi wa duniya shari'a, sai ku kasa sasanta al'amura marasa mahimmanci?
3 Do you not know that we will judge angels? How much more the things of this life!
Baku sani ba mu za mu yiwa mala'iku shari'a? Balle shari'ar al'amuran wannan rai?
4 So if you need to settle everyday matters, do you appoint as judges those of no standing in the church?
Idan kuna shar'anta al'amuran yau da kullum, don me ku ke kai irin wadannan matsaloli gaban wadanda ba 'yan ikilisiya ba?
5 I say this to your shame. Is there really no one among you wise enough to arbitrate between his brothers?
Na fadi wannan domin ku kunyata. Babu wani mai hikima a cikin ku ko daya da zai iya sasanta gardama a tsakanin 'yan'uwa?
6 Instead, one brother goes to law against another, and this in front of unbelievers!
Amma kamar yadda yake, mai bi ya na kai karar mai bi a kotu, kuma a gaban mai shari'a wanda ba mai bi ba!
7 The very fact that you have lawsuits among you means that you are thoroughly defeated already. Why not rather be wronged? Why not rather be cheated?
Kasancewar rashin jituwa a tsakanin Kirista na nuna cewa kun rigaya kun gaza. Don me ba za ka shanye laifi ba? Don me ba za ka yarda a kware ka ba?
8 Instead, you yourselves cheat and do wrong, even against your own brothers!
Amma kun yi wa wadansu laifi kun kuma cutar su, su kuwa 'yan'uwanku ne!
9 Do you not know that the wicked will not inherit the kingdom of God? Do not be deceived: Neither the sexually immoral, nor idolaters, nor adulterers, nor men who submit to or perform homosexual acts,
Ba ku sani ba marasa adalci ba za su gaji Mulkin Allah ba? Kada ku gaskata karya. Da fasikai, da masu bautar gumaka, da mazinata, da karuwai maza, da masu ludu,
10 nor thieves, nor the greedy, nor drunkards, nor verbal abusers, nor swindlers, will inherit the kingdom of God.
da barayi, da masu zari, da mashaya, da masu zage-zage, da 'yan damfara - ba waninsu da zai gaji Mulkin Allah.
11 And that is what some of you were. But you were washed, you were sanctified, you were justified, in the name of the Lord Jesus Christ and by the Spirit of our God.
Kuma da haka wadansu a cikinku suke, amma an tsarkake ku, an mika ku ga Allah, an maida tsayuwar ku dai-dai a gaban Allah a cikin sunan Ubangji Yesu Almasihu, kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.
12 “Everything is permissible for me,” but not everything is beneficial. “Everything is permissible for me,” but I will not be mastered by anything.
Dukkan abu halal ne a gare ni”, amma ba kowanne abu ne mai amfani ba. “Dukan abu halal ne a gare ni,” amma ba zan yarda wani abu ya mallake ni ba.
13 “Food for the stomach and the stomach for food,” but God will destroy them both. The body is not intended for sexual immorality, but for the Lord, and the Lord for the body.
“Abinci don ciki ne, kuma ciki don abinci ne”, amma Allah za ya kawar da su duka. Ba a yi jiki saboda fasikanci ba. Maimakon haka, jiki don Ubangiji ne, kuma Ubangiji zai yi wa jiki tanaji.
14 By His power God raised the Lord from the dead, and He will raise us also.
Allah ya tada Ubangiji, kuma za ya tashe mu ta wurin ikonsa.
15 Do you not know that your bodies are members of Christ? Shall I then take the members of Christ and unite them with a prostitute? Never!
Ba ku sani ba jikunanku gabobi ne na Almasihu? Na dauki gabobin Almasihu in hada su da karuwa? Allah ya sawwake!
16 Or don’t you know that he who unites himself with a prostitute is one with her in body? For it is said, “The two will become one flesh.”
Ko baku sani ba dukan wanda yake hade da karuwa, ya zama jiki daya da ita kenan?
17 But he who unites himself with the Lord is one with Him in spirit.
Kamar yadda Littafi ya fadi, “Su biyun za su zama nama daya.” Amma wanda yake hade da Ubangiji ya zama ruhu daya da shi kenan.
18 Flee from sexual immorality. Every other sin a man can commit is outside his body, but he who sins sexually sins against his own body.
Ku gujewa fasikanci! Kowane zunubi mutum yake aikatawa a waje da jikinsa yake, amma mutum mai fasikanci yana zunubi gaba da jikinsa.
19 Do you not know that your body is a temple of the Holy Spirit who is in you, whom you have received from God? You are not your own;
Ba ku sani ba jikinku haikali ne na Ruhu Mai-tsarki, wanda yake zaune a cikinku, wanda ku ka samu daga wurin Allah? Ba ku sani ba cewa ku ba na kanku ba ne?
20 you were bought at a price. Therefore glorify God with your body.
An saye ku da tsada. Don haka, ku daukaka Allah da jikin ku.

< 1 Corinthians 6 >