< 1 Chronicles 3 >

1 These were the sons of David who were born to him in Hebron: The firstborn was Amnon by Ahinoam of Jezreel; the second was Daniel by Abigail of Carmel;
Waɗannan su ne’ya’yan Dawuda maza da aka haifa masa a Hebron. Ɗan farinsa shi ne Amnon ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel; na biyun, Daniyel ɗan Abigiyel mutuniyar Karmel;
2 the third was Absalom the son of Maacah daughter of King Talmai of Geshur; the fourth was Adonijah the son of Haggith;
na ukun, Absalom ɗan Ma’aka’yar Talmai sarkin Geshur; na huɗun, Adoniya ɗan Haggit;
3 the fifth was Shephatiah by Abital; and the sixth was Ithream by his wife Eglah.
na biyar, Shefatiya ɗan Abital; da kuma na shida, Itireyam ta wurin matarsa Egla.
4 These six sons were born to David in Hebron, where he reigned seven years and six months. And David reigned in Jerusalem thirty-three years,
Waɗannan su ne aka haifa wa Dawuda a Hebron, inda ya yi mulki shekaru bakwai da wata shida. Dawuda ya yi mulki a Urushalima shekaru talatin da uku,
5 and these sons were born to him in Jerusalem: Shimea, Shobab, Nathan, and Solomon. These four were born to him by Bathsheba daughter of Ammiel.
kuma waɗannan su ne yaran da aka haifa masa a can. Shimeya, Shobab, Natan da Solomon. Waɗannan huɗu ne Bat-shuwa’yar Ammiyel ta haifa.
6 David’s other sons were Ibhar, Elishua, Eliphelet,
Akwai kuma Ibhar, Elishama, Elifelet,
7 Nogah, Nepheg, Japhia,
Noga, Nefeg, Yafiya,
8 Elishama, Eliada, and Eliphelet—nine in all.
Elishama, Eliyada da Elifelet, su tara ne duka.
9 These were all the sons of David, besides the sons by his concubines. And Tamar was their sister.
Dukan waɗannan’ya’yan Dawuda ne maza, ban da’ya’yansa maza ta wurin ƙwarƙwaransa. Tamar ita ce’yar’uwarsu.
10 Solomon’s son was Rehoboam: Abijah was his son, Asa his son, Jehoshaphat his son,
Zuriyar Solomon su ne Rehobowam, da Abiya, da Asa, da Yehoshafat,
11 Joram his son, Ahaziah his son, Joash his son,
da Yoram, da Ahaziya, da Yowash,
12 Amaziah his son, Azariah his son, Jotham his son,
da Amaziya, da Azariya, da Yotam,
13 Ahaz his son, Hezekiah his son, Manasseh his son,
da Ahaz, da Hezekiya da Manasse,
14 Amon his son, and Josiah his son.
da Amon, da Yosiya.
15 The sons of Josiah: Johanan was the firstborn, Jehoiakim the second, Zedekiah the third, and Shallum the fourth.
’Ya’yan Yosiya maza su ne, Yohanan ɗan fari, Yehohiyakim ɗa na biyu, Zedekiya ɗa na uku Shallum ɗa na huɗu.
16 The successors of Jehoiakim: Jeconiah his son, and Zedekiah.
Magādan Yehohiyakim su ne, Yekoniya ɗansa, da Zedekiya.
17 The descendants of Jeconiah the captive: Shealtiel his son,
Zuriyar Yekoniya kamamme su ne, Sheyaltiyel,
18 Malchiram, Pedaiah, Shenazzar, Jekamiah, Hoshama, and Nedabiah.
Malkiram, Fedahiya, Shenazzar, Yekamiya, Hoshama da Nedabiya.
19 The sons of Pedaiah: Zerubbabel and Shimei. The children of Zerubbabel: Meshullam and Hananiah, their sister Shelomith,
’Ya’yan Fedahiya su ne, Zerubbabel da Shimeyi.’Ya’yan Zerubbabel maza su ne, Meshullam da Hananiya. Shelomit ce’yar’uwarsu.
20 and five others: Hashubah, Ohel, Berechiah, Hasadiah, and Jushab-hesed.
Akwai kuma waɗansu biyar, Hashuba, Ohel, Berekiya, Hasadiya da Yushab-Hesed.
21 The descendants of Hananiah: Pelatiah, Jeshaiah, and the sons of Rephaiah, of Arnan, of Obadiah, and of Shecaniah.
Zuriyar Hananiya su ne, Felatiya da Yeshahiya, Refahiya, Arnan, Obadiya da Shekaniya.
22 The six descendants of Shecaniah were Shemaiah and his sons: Hattush, Igal, Bariah, Neariah, and Shaphat.
Zuriyar Shekaniya su ne, Shemahiya da’ya’yansa maza. Hattush, Igal, Bariya, Neyariya da Shafat, su shida ne duka.
23 The sons of Neariah: Elioenai, Hizkiah, and Azrikam—three in all.
’Ya’yan Neyariya maza su ne, Eliyohenai, Hezekiya da Azrikam, su uku ne duka.
24 The sons of Elioenai: Hodaviah, Eliashib, Pelaiah, Akkub, Johanan, Delaiah, and Anani—seven in all.
’Ya’yan Eliyohenai su ne, Hodawiya, Eliyashib, Felahiya, Akkub, Yohanan, Delahiya da Anani, su bakwai ne duka.

< 1 Chronicles 3 >