< 1 Chronicles 15 >

1 David constructed buildings for himself in the City of David, and he prepared a place for the ark of God and pitched a tent for it.
Bayan Dawuda ya yi gine-gine wa kansa a Birnin Dawuda, sai ya shirya wuri domin akwatin alkawarin Allah, ya kuma kafa tenti dominsa.
2 Then David said, “No one but the Levites may carry the ark of God, because the LORD has chosen them to carry the ark of the LORD and to minister before Him forever.”
Sa’an nan Dawuda ya ce, “Babu wani sai ko Lawiyawa kaɗai za su ɗauka akwatin alkawarin Allah, gama Ubangiji ya zaɓe su su ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji su kuma yi hidima a gabansa har abada.”
3 And David assembled all Israel in Jerusalem to bring up the ark of the LORD to the place he had prepared for it.
Dawuda ya tattara dukan Isra’ila a Urushalima don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurin da aka shirya dominsa.
4 Then he gathered together the descendants of Aaron and the Levites:
Ya tattara zuriyar Haruna a wuri ɗaya da kuma Lawiyawa.
5 From the Kohathites, Uriel the chief and 120 of his relatives;
Daga zuriyar Kohat, Uriyel shugaba da dangi 120;
6 from the Merarites, Asaiah the chief and 220 of his relatives;
daga zuriyar Merari Asahiya shugaba da dangi 220;
7 from the Gershomites, Joel the chief and 130 of his relatives;
daga zuriyar Gershom, Yowel shugaba da dangi 130;
8 from the Elizaphanites, Shemaiah the chief and 200 of his relatives;
daga zuriyar Elizafan, Shemahiya shugaba da dangi 200;
9 from the Hebronites, Eliel the chief and 80 of his relatives;
daga zuriyar Hebron, Eliyel shugaba da dangi 80;
10 and from the Uzzielites, Amminadab the chief and 112 of his relatives.
daga zuriyar Uzziyel, Amminadab shugaba da dangi 112.
11 David summoned the priests Zadok and Abiathar and the Levites Uriel, Asaiah, Joel, Shemaiah, Eliel, and Amminadab.
Sa’an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyatar, firistoci, tare da Uriyel, Asahiya, Yowel, Shemahiya, Eliyel da Amminadab, Lawiyawa.
12 And he said to them, “You are the heads of the Levitical families. You and your relatives must consecrate yourselves so that you may bring the ark of the LORD, the God of Israel, to the place I have prepared for it.
Ya ce musu, “Ku ne kawunan iyalan Lawiyawa; ku da’yan’uwanku Lawiyawa, sai ku tsarkake kanku ku hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila, zuwa wurin da na shirya dominsa.
13 It was because you Levites were not with us the first time that the LORD our God burst forth in anger against us. For we did not consult Him about the proper order.”
Domin ku, Lawiyawa ba ku haura da shi da farko ba ne ya sa Ubangiji Allahnmu ya husata a kanmu. Ba mu tambaye shi game da yadda za mu yi shi a hanyar da aka ƙayyade ba.”
14 So the priests and Levites consecrated themselves to bring up the ark of the LORD, the God of Israel.
Saboda haka firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu don su hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila.
15 And the Levites carried the ark of God on their shoulders with the poles, as Moses had commanded in accordance with the word of the LORD.
Sai Lawiyawa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah da sanduna a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji.
16 David also told the leaders of the Levites to appoint their relatives as singers to lift up their voices with joy, accompanied by musical instruments—harps, lyres, and cymbals.
Dawuda ya faɗa wa shugabannin Lawiyawa su sa’yan’uwansu su zama mawaƙa don su rera waƙoƙi masu farin ciki, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, molaye, garayu da ganguna.
17 So the Levites appointed Heman son of Joel; from his brothers, Asaph son of Berechiah; from their brothers the Merarites, Ethan son of Kushaiah;
Saboda haka Lawiyawa suka zaɓi Heman ɗan Yowel, da Asaf ɗan Berekiya daga cikin’yan’uwansu. Daga iyalin Merari kuma aka zaɓi Etan ɗan Kushahiya.
18 and with them their brothers next in rank: Zechariah, Jaaziel, Shemiramoth, Jehiel, Unni, Eliab, Benaiah, Maaseiah, Mattithiah, Eliphelehu, Mikneiah, and the gatekeepers Obed-edom and Jeiel.
Tare da su kuma’yan’uwansa da suke biye bisa ga matsayi. Wato, Zakariya, Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ben, Ma’asehiya, Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom da Yehiyel, matsaran ƙofofi.
19 The musicians Heman, Asaph, and Ethan were to sound the bronze cymbals.
Mawaƙan nan Heman, Asaf da Etan, ne za su buga kugen tagulla.
20 Zechariah, Aziel, Shemiramoth, Jehiel, Unni, Eliab, Maaseiah, and Benaiah were to play the harps according to Alamoth.
Zakariya, Aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ma’asehiya da Benahiya, ne za su kaɗa molaye masu murya sama-sama, bisa ga alamot.
21 And Mattithiah, Eliphelehu, Mikneiah, Obed-edom, Jeiel, and Azaziah were to lead the music with lyres according to Sheminith.
Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom, Yehiyel da Azaziya, ne za su ja garayu masu murya ƙasa-ƙasa bisa ga sheminit.
22 Chenaniah the head Levite was the director of the music because he was highly skilled.
Kenaniya, shugaban Lawiyawa, shi ne mai bi da waƙoƙi. Wannan hakkinsa ne, gama shi gwani ne a wannan fanni.
23 Berechiah and Elkanah were to be guardians of the ark.
Berekiya da Elkana, ne za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin.
24 Shebaniah, Joshaphat, Nethanel, Amasai, Zechariah, Benaiah, and Eliezer—the priests—were to blow the trumpets before the ark of God. Obed-edom and Jehiah were also to be guardians of the ark.
Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zakariya, Benahiya da Eliyezer firistoci, su ne za su busa ƙahoni a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-Edom da Yehiya su ma za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin.
25 So David, the elders of Israel, and the commanders of thousands went with rejoicing to bring the ark of the covenant of the LORD from the house of Obed-edom.
Sai Dawuda da dattawan Isra’ila da shugabannin ƙungiyoyi dubu suka haura don su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-Edom, da farin ciki.
26 And because God helped the Levites who were carrying the ark of the covenant of the LORD, they sacrificed seven bulls and seven rams.
Domin Allah ya taimaki Lawiyawan da suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, aka miƙa hadayar bijimai bakwai da raguna bakwai.
27 Now David was dressed in a robe of fine linen, as were all the Levites who were carrying the ark, as well as the singers and Chenaniah, the director of music for the singers. David also wore a linen ephod.
To, fa, Dawuda yana saye da kyakkyawar rigar lilin, kamar yadda dukan Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin suka sa, da kuma yadda mawaƙa, da Kenaniya, wanda yake bi da waƙar mawaƙan ya sa. Dawuda kuma ya sa efod lilin.
28 So all Israel brought up the ark of the covenant of the LORD with shouting, with the sounding of rams’ horns and trumpets, and with cymbals and the music of harps and lyres.
Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu.
29 As the ark of the covenant of the LORD was entering the City of David, Saul’s daughter Michal looked down from a window and saw King David dancing and celebrating, and she despised him in her heart.
Yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yake shiga Birnin Dawuda, Mikal’yar Shawulu ta leƙa daga taga. Sa’ad da ta ga Sarki Dawuda yana rawa yana shagali, sai ta rena masa wayo a zuciyarta.

< 1 Chronicles 15 >