< Matthew 27 >

1 When the morning came, all the chief priests and elders of the people held a consultation against Jesus, that they might put him to death.
Da gari ya waye, duk manyan firistoci da dattawan jama'a suka shirya yadda zasu kulla makirci domin su kashe shi.
2 And they bound him and led him away, and delivered him to Pontius Pilate the governor.
Suka daure shi, suka mika shi ga gwamna Bilatus.
3 Then Judas, who had delivered him up, when he saw that he was condemned, stung by remorse, brought back the thirty pieces of silver to the chief priests and elders,
Sa'adda Yahuza, wanda ya bashe shi, ya ga an zartarwa Yesu hukuncin kisa, ya nemi tuba ya kuma mayar da azurfar talatin ga manyan firistocin da dattawan,
4 saying: I have sinned in having delivered up innocent blood. They replied: What is that to us? You will see to that.
yace, “Na yi zunubi ta wurin cin amanar mara laifi.” Amma sukace, “Ina ruwan mu? Ka ji da shi da kanka?”
5 And he threw down the money in the temple, and departed, and went and hanged himself.
Sai ya jefar da kwandalolin azurfar a kasa cikin haikalin ya kuma bar su, ya tafi ya rataye kansa.
6 And the chief priests took the money, and said: It is not lawful to put it into the sacred treasury, because it is the price of blood.
Sai babban firist ya dauki kwandalolin azurfar ya ce, “Ba daidai bane bisa ga shari'a musa wannan cikin ma'aji, saboda kudin jini ne.”
7 And they took counsel, and bought with it the potter’s field, as a burial-place for foreigners.
Sai suka tattauna al'amarin a tsakanin su, kudin kuma suka sayi filin maginin tukwane domin makabatar baki.
8 For this reason, that field is called the field of blood, to this day.
Dalilin wannan ne ake kiran wurin, “Filin jini” har yau.
9 Then the word was fulfilled which was spoken by Jeremiah the prophet, saying: And they took the thirty pieces of silver, the price of him that had a price set upon him, on whom some of the children of Israel did set a price,
Sai abin da aka fada ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa, “Suka dauki tsabar azurfa talatin na farashin da mutanen Isra'ila suka sa a kansa,
10 and gave them for the potter’s field, as the Lord appointed me.
suka bayar domin sayen filin mai tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”
11 And Jesus stood before the governor; and the governor asked him, saying: Are you the king of the Jews? Jesus replied to him: You say it.
Sai Yesu ya tsaya a gaban gwamna, gwamna ya kuma tambaye shi, “Kai sarkin Yahudawa ne?” Yesu ya amsa, “Haka ka fada.”
12 And when he was accused by the chief priests and elders, he made no answer.
Amma da manyan firistocin da dattawan suka zarge shi, bai ce komai ba.
13 Then Pilate said to him: Do you not hear how many things they testify against you?
Sai Bilatus yace masa, “Baka ji dukan zarge-zargen da ake yi maka ba?”
14 And he gave him answer to not one word, so that the governor was greatly astonished.
Amma bai ce masa ko kalma guda ba, sai gwamna yayi matukar mamaki.
15 Now at the feast, the governor was in the habit of releasing to the multitude one prisoner, whom they chose.
To lokacin bikin idi, al'adar gwamna ne ya saki mutum guda wanda jama'a suka zaba.
16 They then had a notorious prisoner, called Barabbas.
A wannan lokacin suna da wani sanannen dan kurkuku mai suna Barabbas.
17 Therefore, while they were together, Pilate said to them: Which do you wish me to release to you, Barabbas, or Jesus, who is called Christ?
To da suka tattaru, sai Bilatus yace masu, “Wa kuke so a sakar maku? Barabbas, ko Yesu wanda ake kira Almasihu?”
18 For he knew that through envy they had delivered him up.
Saboda ya san sun kawo shi ne domin kishi.
19 While he was sitting on the judgment-seat, his wife sent to him, saying: Have nothing to do with that just man, for I have suffered much to-day in a dream, because of him.
Da yake zaune a kujerar shari'a, matarsa ta aika masa cewa, “Ka fita sha'anin mutumin nan marar laifi. Saboda na sha wahala sosai a yau cikin mafarki saboda shi.”
20 But the chief priests and the elders persuaded the multitude to ask Barabbas, and destroy Jesus.
A lokacin nan manyan firistoci da dattawa suka rinjayi ra'ayin jama'a suce a sakar masu da Barabbas, a kashe Yesu.
21 The governor answered and said to them: Which of the two do you wish me to release to you? They replied: Barabbas.
Sai gwamna ya tambayesu, “Wa kuke so a sakar maku?” Sukace, “Barabbas.”
22 Pilate said to them: What then shall I do with Jesus, who is called Christ? They all said to him: Let him be crucified.
Bilatus yace masu, “Me zan yi da Yesu wanda ake kira Almasihu?” Sai duka suka amsa, “A gicciye shi.”
23 But the governor said: Why, what evil has he done? But they cried vehemently, saying: Let him be crucified.
Sai yace, “Don me, wane laifi ya aikata?” Amma suka amsa da babbar murya, “A gicciye shi”
24 When Pilate saw that he gained nothing, but rather that a tumult was rising, he took water, and washed his hands before the multitude, and said: I am innocent of the blood of this just man; you will see to it.
Amma da Bilatus ya ga ba zai iya komai ba don hargitsi zai iya barkewa, ya dauki ruwa ya wanke hannuwansa a gaban jama'a, yace, “Ba ni da laifi ga jinin mutumin nan marar laifi. Ku yi abin da kuka ga dama.”
25 And all the people answered and said: His blood be upon us and upon our children.
Duka mutanen sukace, “Bari jininsa ya kasance a kan mu da 'ya'yan mu.”
26 Then he released to them Barabbas; but after he had scourged Jesus, he delivered him up to be crucified.
Sai ya sakar masu da Barabbas amma yayi wa Yesu bulala ya mika shi garesu domin su gicciye shi.
27 Then the soldiers of the governor took Jesus into the palace, and brought together to him the whole band.
Sai sojojin gwamna suka dauki Yesu zuwa farfajiya suka kuma tara dukan rundunar sojoji.
28 And they stripped him, and put on him a scarlet cloak;
Suka yi masa tumbur sa'annan suka sa masa jar alkyabba.
29 and when they had plaited a crown of thorn branches, they put it upon his head, and a reed in his right hand; and kneeling before him, they derided him, saying: Hail, King of the Jews!
Sai suka yi masa rawanin kaya suka sa a kansa, suka kuma bashi sanda a hannunsa na dama. Suka rusuna a gabansa suna masa ba'a, suna cewa, “Ranka ya dade, Sarkin Yahudawa!”
30 And they spit upon him, and took the reed, and struck him on the head.
Suka kuma tofa masa yawu, suka kwace sandar suka buga masa a ka.
31 And when they had derided him, they took off the cloak from him, and put his own clothes on him, and led him away to crucify him.
Bayan sun gama masa ba'a, suka cire masa alkyabbar suka sa masa kayansa, suka jagorance shi zuwa wurin da za a gicciye shi.
32 And as they were going out, they found a man of Cyrene, named Simon: this man they compelled to carry his cross.
Da suka fito waje, sai suka iske wani Bakurame mai suna Saminu, wanda suka tilasta ya tafi tare dasu domin ya dauki gicciyen.
33 And when they had come to a place called Golgotha, which, when translated, is the place of a skull,
Suka iso wani wuri da ake kira Golgotta, wanda ke nufin,”Wurin kwalluwa.”
34 they gave him vinegar to drink, mingled with gall; and when he had tasted it, he refused to drink.
Suka bashi ruwan inabi da aka gauraya da wani abu mai daci. Amma da ya 'dan-'dana shi sai ya ki sha.
35 And when they had crucified him, they divided his clothing among themselves, by casting the lot.
Bayan da suka gicciye shi, suka kada kuri'a a kan rigarsa.
36 And they sat down and watched him there.
Suka kuma zauna suna kallonsa.
37 And they placed above his head the charge that was made against him, written: THIS IS JESUS THE KING OF THE JEWS.
A sama da kansa suka sa abinda ake tuhumarsa da ita a rubuce, “Wannan shine sarkin Yahudawa.”
38 Then were two robbers crucified with him; one on his right hand, and the other on his left.
An gicciye shi da 'yanfashi guda biyu, daya ta damansa dayan kuma ta hagunsa.
39 And they that passed by reviled him, shaking their heads,
Wadanda suke wucewa suna zaginsa, suna girgiza kai,
40 and saying: You that destroy the temple, and build it in three days, save yourself; if you are the Son of God, come down from the cross.
suna kuma cewa, “Kai da kace zaka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, ka ceci kanka mana! In dai kai Dan Allah ne, ka sauko daga gicciyen!”
41 In like manner also the chief priests, with the scribes and elders, derided him, and said:
Ta haka ma manyan firistocin suka rika yi masa ba'a, tare da marubuta da shugabannin, suna cewa,
42 He saved others; himself he can not save. If he is the King of Israel, let him now come down from the cross, and we will believe on him.
“Ya ceci wasu amma ya kasa ceton kansa. Shi ne sarkin Isra'ila. Ya sauko mana daga kan gicciyen, sai mu ba da gaskiya gareshi.
43 He trusted in God; let him deliver him now, if he delights in him; for he said: I am the Son of God.
Tun da ya yarda da Allah. Bari Allahn ya cece shi mana, saboda yace, “Ni dan Allah ne.”
44 The robbers also that were crucified with him, uttered the same reproaches against him.
Hakan nan ma 'yanfashin guda biyu da aka gicciye su tare suka zage shi.
45 From the sixth hour there was darkness over all the land till the ninth hour.
To tun da tsakar rana sai duhu ya rufe kasar gaba daya har karfe uku na yamma.
46 But about the ninth hour, Jesus cried out with a loud voice, saying: Eli, Eli, lamah sabachthani? that is, My God, my God, why hast thou forsaken me?
Wajen karfe uku, Yesu ya tada murya mai karfi yace, “Eli, Eli lama sabaktani?” wanda ke nufin, “Allahna, Allahna, don me ka yashe ni?”
47 Some of those who were standing there, when they heard it, said: This man calls for Elijah.
Da wadanda suke tsaye kusa suka ji haka, sai sukace, “Yana kiran Iliya.”
48 And immediately one of them ran, and took a sponge, and having filled it with vinegar, put it on a reed, and gave it to him to drink.
Nan take wani ya ruga da gudu ya dauki soso ya tsoma cikin ruwan inabi mai tsami ya soka kan sandar kara ya mika masa ya sha.
49 The rest said: Wait, let us see if Elijah is coming to save him.
Sai sauran sukace, “Rabu da shi mu gani ko Iliya zai zo ya cece shi.”
50 And Jesus again cried with a loud voice, and gave up his spirit.
Sai Yesu ya ta da murya mai karfi yayi kuka sai ya saki ruhunsa.
51 And behold, the vail of the temple was rent in two from top to bottom. And the earth did shake, and the rocks were rent:
Sai labullen haikali ya yage gida biyu daga sama zuwa kasa. Kasa kuma ta girgiza, duwatsu suka farfashe.
52 and the sepulchers were opened, and many bodies of the saints that slept, arose.
Kaburbura suka bude, tsarkaka kuwa wadanda suke barci da yawa suka tashi.
53 And they came out of their sepulchers after his resurrection, and entered the holy city, and appeared to many.
Suka fito daga kaburbura bayan tashinsa, suka shiga birni mai tsarki suka bayyana ga mutane da yawa.
54 Now the centurion, and those who were with him watching Jesus, when they saw the earthquake, and what was done, were greatly afraid, and said: Of a truth, this was the Son of God.
Da hafsan sojan da wadanda suke kallon Yesu suka ga girgizar kasar da abinda ya faru, suka ji tsoro kwarai sukace, “Hakika wannan Dan Allah ne”
55 Many women that had followed Jesus from Galilee, and had ministered to him, were there, looking on from a distance.
Mata dayawa da suka bi Yesu daga Galili domin su lura da shi suka tsaya suna kallo daga nesa.
56 Among these was Mary Magdalene, and Mary the mother of James and Joses, and the mother of the sons of Zebedee.
A cikin su akwai Maryamu Magadaliya, Maryamu uwar Yesu da Yusufu, da uwar 'ya'yan Zabadi.
57 When the evening had come, there came a rich man of Arimathea, named Joseph; and he also was a disciple of Jesus.
Da yamma sai wani attajiri mutumin Armatiya ya zo, mai suna Yusufu wanda shi ma almajirin Yesu ne.
58 This man went to Pilate, and asked for the body of Jesus. Then Pilate commanded the body to be given.
Ya je wurin Bilatus ya roka a bashi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a bashi.
59 And Joseph took the body and wrapped it in clean linen,
Yusufu ya dauki jikin, ya rufe shi da likafani mai tsabta,
60 and laid it in his own new tomb, which he had hewn out in the rock. And he rolled a great stone to the door of the tomb, and departed.
sai ya sa shi a cikin sabon kabarinsa da ya sassaka cikin dutse. Sai ya mirgina babban dutse a bakin kofar kabarin ya tafi.
61 And Mary Magdalene was there, and the other Mary, sitting opposite the tomb.
Maryamu Magadaliya da dayan Maryamun suna nan zaune akasin kabarin.
62 On the morrow, which was the day after the preparation, the chief priests and the Pharisees came together to Pilate,
Washegari, wato bayan ranar Shiri, Sai manyan firistoci da Farisawa suka taru tare da Bilatus.
63 and said: Sir, we remember that that deceiver said, while he was yet alive, After three days I will arise.
Sukace, “Mai gida, mun tuna lokacin da mayaudarin nan yake da rai, yace, “Bayan kwana uku zan tashi.”
64 Therefore, command that the sepulcher be made safe till the third day, lest his disciples come and steal him away, and say to the people, He has risen from the dead; and the last error will be worse than the first.
Saboda haka, ka bada umarni a tsare kabarin na kwana uku. In ba haka ba almajiransa zasu zo su sace shi, kuma su ce wa mutane, “Ya tashi daga mattatu.” Kuma yaudarar karshe zata fi ta farko muni.”
65 Pilate said to them: You have a guard; go, make it as safe as you know how.
Bilatus yace masu, “Ku dauki masu tsaro. Kuyi tsaro iyakar karfin ku.”
66 And they went and made the sepulcher safe, by placing a seal upon the stone, and setting the guard.
Sai suka tafi suka tsare kabarin, suka hatimce dutsen, suka sa masu tsaro.

< Matthew 27 >